Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Inuwa Ya Bukaci A Kara Zuba Jari A Ilimin Sana’o’i Domin Samar Wa Matasa Aikin Yi Afrika
  • Gwamnonin Arewa Sun Yi Jimamin Rasuwar Bamanga Tukur, Sun Yaba Da Gudunmawarsa Ga Najeriya Afrika
  • Tsohon Shugaban PDP, Bamanga Tukur, Ya Rasu Yana da Shekaru 91 Afrika
  • Filato: Gwamnati Ta Ƙarfafa Matakan Kariya Yayin Sake Buɗe Makarantu Afrika
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika

Kungiyar Mata Manoma A Najeriya Ta Raba Kyautar Abinci A Gombe
Published: March 8, 2026 at 4:00 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Ƙungiyar Mata Manoma a Najeriya, wato WOFAN, ƙarƙashin jagorancin Hajiya Salamatu Garba, ta raba buhunan shinkafa dubu biyar ga mata a jihar Gombe domin tallafa musu wajen inganta rayuwar iyalansu, a wani shiri da aka gudanar domin tunawa da Ranar Mata ta Duniya.

Da yake jawabi yayin ƙaddamar da rabon tallafin, Shugaban WOFAN a Jihar Gombe, Usman Rayyanu Dabai, ya bayyana cewa shirin ya shafi mata a wasu daga cikin ƙananan hukumomin jihar da suka haɗa da Gombe, Akko, Yamaltu Deba, Kwami da Dukku.

Ya ce an shirya wannan tallafi ne a wani ɓangare na bikin Ranar Mata ta Duniya, domin ƙarfafa mata da kuma taimaka musu su tallafa wa iyalansu, musamman mazajensu, wajen tafiyar da al’amuran gida.

Rayyanu Dabai ya kuma yi kira ga mata a faɗin Jihar Gombe da su ci gaba da bai wa mazajensu haɗin kai a harkokin gida, domin ƙarfafa zaman lafiya da kyakkyawar rayuwar aure.

A nasu jawaban yayin karɓar tallafin, wasu daga cikin sarakunan gargajiya da suka haɗa da Banban Hakimin Gombe, Alhaji Bappah Ibrahim, Hakimin Bokna, Alhaji Abubakar Usman Deba, da Lamidon Akko, Alhaji Umaru Muhammadu Atiku, sun yaba wa Hajiya Salamatu Garba bisa wannan karamci da ta nuna wa al’ummar Jihar Gombe.

Sarakunan gargajiyar sun kuma buƙaci mata a jihar da su zauna lafiya da mazajensu tare da riƙa ba su goyon baya, domin ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kan iyalai.

An gudanar da bikin ƙaddamar da rabon tallafin ne a Makarantar Firamare ta Orji Estate da ke Gombe, inda wakilan mata daga kowace ƙaramar hukuma da abin ya shafa suka halarta domin karɓar nasu kaso na tallafin.

Afrika, Labarai, Najeriya, Nishadi, Rumbun Hotuna

Post navigation

Previous Post: Ambaliyar Ruwa Yayi Ajalin Mutane A Nairobi
Next Post: Majalisar Kwararrun Iran Ta Sanar Da Sabon Shugaban Addini

Karin Labarai Masu Alaka

Taron Sulhu Tsakanin Addinai Mabanbanta Na Arewacin Najeriya Labarai
Farfesa Inuwa Ja’afaru Yakarbi Ragamar Shugabancin Jami’ar Kashere Labarai
‘Yan Tawayen Kasar Kwango Ne Suka Kai Hari Filin Jirgin Saman Kisangani Labarai
Eziekel Gomos Ya Zamo Babban Daraktan Sakatariyar Zauren Gwamnonin Arewa Najeriya
Magoya Bayan Dan Hamayya A Afirka Ta Kudu Sun Hallara A Kotu Afrika
Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Inuwa Ya Bukaci A Kara Zuba Jari A Ilimin Sana’o’i Domin Samar Wa Matasa Aikin Yi
  • Gwamnonin Arewa Sun Yi Jimamin Rasuwar Bamanga Tukur, Sun Yaba Da Gudunmawarsa Ga Najeriya
  • Tsohon Shugaban PDP, Bamanga Tukur, Ya Rasu Yana da Shekaru 91
  • Filato: Gwamnati Ta Ƙarfafa Matakan Kariya Yayin Sake Buɗe Makarantu
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • NYSC – Sai An Gabatar Da Takardar NERD Kafin Shiga Bautar Ƙasa Afrika
  • Ana Cigaba Da Ceto Masunta Daga Ruwa A Ghana Labarai
  • Malaman Addinin Musulunci Da Kirista Sunyi Bikin Cika Shekara 15 Na Iftar A Najeriya Afrika
  • Rikicin Hakar Gwal Ya Janyo Hallaka Mutane 70 A Sudan Ta Kudu Afrika
  • Rundunar Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Shirya Taron Masu Ruwa Da Tsaki A Jihar Filato Afrika
  • Hukumomi A Kasar Syri Lanka Suna Kokarin Fidda Jirgin Yakin Iran Daga Kasar Afrika
  • Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha: Tura Sojojin Birtaniya Ukraine Zai Kara Ta’azzara Yaki Labarai
  • Shugaba Trump Ya Jinjinawa Tinubu Kan Yaƙi Da Ta’addanci A Najeriya Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.