Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Majalisar Kwararrun Iran Ta Sanar Da Sabon Shugaban Addini
Published: March 9, 2026 at 3:45 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Majalisar kwararru a kasar Iran ta ayyana Mojtaba Khameini a matsayin sabon shugaban addini, domin maye gurbin mahaifinsa, marigayi Ayatollah Ali Khameini, yayin da Iran take kara nuna jajircewa da hare-haren da ake kai mata, kuma a yayin da yawan sojojin Amurka da suka mutu ya karu zuwa 7.

Mojtaba Khameini wanda ke tsaka-tsaki cikin jerin manyan malamai na Iran, yana da alaka mai karfi da rundunar sojojin juyin juya hali na Iran, har aka yi ta ganinsa a matsayin wanda zai iya gadon mahaifinsa.

Duk da cewa akidar Shi’a ta Iran ba ta karfafa gadon mulki daga uba zuwa da, Mojtaba ya kasance yana da magoya baya masu yawa da karfi a rundunar ta juyin juya hali da kuma ofishin shugabancin addini na mahaifinsa.

Isra’ila ta yi barazanar kai farmaki a kan duk wanda za a zaba, yayin da shi ma shugaba Donald Trump na Amurka ya bukaci da ya taka rawa wajen zaben sabon shugaban.

A ranar lahadi, Amurka ta ba da sanarwar mutuwar sojanta na 7 daga raunukan da ya samu a hare-haren ramuwar gayya na farklo da kasar Iran ta kai a makon da ya shige.

Wannan na zuwa kwana guda a bayan da Trump ya jagoranci bukin tarbar gawarwakin sojoji 6 da aka kashe tun fari.

A yayin da Trump yake fadin cewa tilas Iran ta mika wuya, kakakin majalisar dokokin Iran, Mohammed Bagher Qalibaf, yace ba su neman a tsagaita wuta a wannan yakin, kuma zasu lallasa wadanda suka kai musu farmaki.

Afrika, Amurka, Labarai, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Kungiyar Mata Manoma A Najeriya Ta Raba Kyautar Abinci A Gombe
Next Post: Kurdawa Sun Gargadi ‘Yan Uwansu Game Da Alaka Da Amurka Wajen Yakar Iran

Karin Labarai Masu Alaka

An Yi Fashin Kaguwa Da Dodon-Kodi Na Miliyoyin Dalar Amurka Amurka
Ferfesa Pantami Yasamu Tikitin Takarar Gwamnan Gombe A Jami’yar PDP Afrika
Karamar Sallah: Hukumar Kashe Gobara A Gombe Ta Kuduri Aniyar Kare Al’umma Afrika
Hukumar IMF Tana Naziri Domin Kara Bada Lamuni Ga Kasar Zambiya Afrika
Dr. Kabiru Hassan Ya Kammala Wa’adinsa A GOGIS, Ya Yi Bitar Sauye-Sauyen Harkokin Filaye Afrika
Angano Gawar Wani Dan Myanmar A Arewacin New York Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Hukumar DSS Ta Sake Kama Abubakar Malami Labarai
  • Kamfanin Mai Mallakar Saudiya Aramco Zai Sanja Hanyar Fitar Da Danyen Mai Labarai
  • Gobara Ta Tashi A Hukumar FIRS Dake Abuja Najeriya
  • Motar Yashi Ta Kashe Mutane Shida A Wani Coci Dake Legas Najeriya
  • Shugaba Trump Ya Amince Da Tsawaita Cinikayya Tsakanin Amurka Da Kasashen Afirka Afrika
  • An Harbo Jirgin Yakin Amurka A Iran Amurka
  • Burkina Faso Ta Sako Jami’an Rundunar Sojin Saman Najeriya 11 Da Aka Tsare Tsaro
  • Kasar Amurka Takara Saka Takunkumi Akan Kasar Venezuela Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.