Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

Shugaba Tinubu Ya Taya Murtala Garo Murnar Zama Mataimakin Gwamnan Kano
Published: May 5, 2026 at 5:01 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya Alhaji Murtala Sule Garo murnar rantsar da shi a matsayin sabon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, wanda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kaddamar a ranar Talata.

Gwamna Abba ya nada Murtala Garo ne domin cike gurbin da Comrade Aminu Abdulsalam ya bari, bayan murabus din da ya yi biyo bayan sauya shekar gwamnan zuwa jam’iyyar APC.

Murtala Garo, mai shekara 48, gogajen dan siyasa ne wanda ya rike mukamai daban-daban, ciki har da Shugaban Karamar Hukumar Kabo,Kwamishinan Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Al’amuran Masarautu a karkashin gwamnatin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, kuma dan takarar Mataimakin Gwamna na jam’iyyar APC a zaben shekarar 2023.

Shugaba Tinubu ya jinjina wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa wannan nadi, yana mai bayyana cewa matakin zai karfafa hadin kan da ake bukata a cikin sahu da jerin mambobin jam’iyyar APC a Jihar Kano.

Haka zalika, Shugaban ya yi kira ga daukacin masu ruwa da tsaki da su mara wa Gwamnan da mataimakinsa baya domin ciyar da jihar gaba.

Ya kuma bukaci sabon Mataimakin Gwamnan da ya yi aiki kafada-da-kafada da gwamna domin samar da shugabanci na gari da zai bunkasa jihar.

A karshe, Shugaba Tinubu ya yi wa Murtala Garo fatan alheri a wannan sabon nauyi da aka dora masa.

Labarai, Najeriya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: CNG Ta Farfado Da Jarin Masu Adaidaita Sahu A Kaduna
Next Post: Shugaba Tinubu Ya Gana Da Masu Zuba Jari A Birnin Paris

Karin Labarai Masu Alaka

Guguwa Mai Karfi Ta Raunata Dubban Mutane A Madagascar Labarai
Kasar China Ta Sauka Daga Ragamar Bada Bashi Labarai
Gwamna Inuwa Yahaya Ya Rantsar Da Sabon Shugaban Ma’aikatan Jiha da Kwamishinoni 23 Afrika
Atiku Ya Bukaci Hadin Kan ‘Yan Adawa Domin Kawo Sauyi A Najeriya Afrika
Babban Hafsan Sojan Libya Ya Mutu A Wani Hatsarin Jirgin Saman Turkiyya Afrika
An Saka Dokar Hana Fita A Jos Ta Arewa Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Tsohuwar Jarumar Kannywood Wasila Ismail Ta Rasu Afrika
  • ‘Yan Sanda A Gombe Sun Jaddada Shirin Yaƙi Da Munanan Dabi’u Afrika
  • Kwankwaso Yayi Kakkausar Lafazi Bayan Ficewar Abba Kabir Yusuf Daga NNPP Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Yau Shekaru 60 Da Kisan Gilla Ga Sir. Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Kungiyar Kwallon Mata Sun Tsallaka Iyakar Turkiyya Zuwa Iran Afrika
  • Amurka Zata Aika Jiragen Yaki Biyu Gabas Ta Tsakiya Amurka
  • Ukraine Ta Aika Tawagar Kwararru Gabas Ta Tsakiya Afrika
  • Rikici Ya Lafa A Kasar Iran Bayan Daukar Matakai Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.