Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

Shugaban Kasar Afirka Ta Tsakiya Ya Roki Rasha Ta Taimakawa Kasar
Published: March 6, 2026 at 8:49 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaban Afirka ta tsakiya Faustin Toudera yayi kira ga Rasha ta taimakawa kasar sa ta fuskar makamashi saboda kalubale da kasar take fuskanta ta wannan fanni.

Shugaba Toudera wadda yayi wannan kira a ranar Alhamis, ya kuma godewa Rasha, a fara ganawa tsakanin shugabannin kasashen biyu a Moscow, yace Rasha ta taka muhimmiyar rawa ta fuskar tsaro a kasar wadda ya bada damar a gudanar da zaben kasar da aka yi bada jumawan nan ba, da ya bashi nasara na wani wa’adi na shekaru bakwai. Yace Rasha tana da kwarewa ta fuskar makamashi.

Kasashen yammacin duniya suna nuna damuwa saboda ganin karin rawar da Rasha take takawa a wasu sassan Afirka, wadda hakan koma baya ne ga muradun Faransa da Amurka. Rundunar Afirka da Rasha wacce ta gaji Kungiyar sojojin haya na Rasha da ake kira Wagner, tana aiki a kasashen Afirka da dama da suka hada da Mali, da Equatorial Guinea, da Afirka ta tsakiya.

Shugaban Rasha Vladimiri Putin yace kasashen biyu suna da damar kara karfafa dangantaka tare da da aiki da juna ta fuskar makashi, noma, da kuma samarda ababen more rayuwa.

Afrika, Labarai, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Shugaba Trump Yace Tehran Tana Neman Kulla Alaka Da Washington
Next Post: Yakin Gabas Ta Tsakiya Ya Haifar Da Tsadar Taki Da Mai Ga Manoma

Karin Labarai Masu Alaka

Nijar: Zamu Tsananta Bincike A Bakin Iyakokin Mu Afrika
Makarantun Allo Zasu Yi Gogayya Da Na Boko Labarai
Ambaliyar Ruwan Sama Yayi Ajalin Mutum 13 A Malawi Labarai
Kasashen Amurka,Israela Da Iran Sun Amince Da Dakatar Da Yaki Afrika
Kano: Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Amince da Garo A Matsayin Mataimakinsa Na 2027 Afrika
Shugaban Amurka Donald Trump Yace Bai Taba Shiga Jirgin Jeffrey Epstein Ba Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Prime Ministan Senegal Ya Bayyana Shirin Sauya Sheka Afrika
  • Gwamnatin Jihar Gombe Ta Haramta Sana’ar Bola Jari Tsaro
  • Rundunar Hadinkan Saudiya Tayi Ikirarin Mayar Da Martani Ga ‘Yan Aware Labarai
  • Shugaban Ukraine Ya Tattauna Da Trump Akan Zaman Lafiya Amurka
  • APC Ta Yi Babban Taron Amincewa Da Shugabannin Jam’iyyar Ba Hamayya Najeriya
  • ‘Yan Bindiga A Mali Sun Kashe Direbobin Manyan Motoci Afrika
  • Magoya Bayan Dan Hamayya A Afirka Ta Kudu Sun Hallara A Kotu Afrika
  • Hamas Ta Kwance Damara Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.