Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Inuwa Ya Bukaci A Kara Zuba Jari A Ilimin Sana’o’i Domin Samar Wa Matasa Aikin Yi Afrika
  • Gwamnonin Arewa Sun Yi Jimamin Rasuwar Bamanga Tukur, Sun Yaba Da Gudunmawarsa Ga Najeriya Afrika
  • Tsohon Shugaban PDP, Bamanga Tukur, Ya Rasu Yana da Shekaru 91 Afrika
  • Filato: Gwamnati Ta Ƙarfafa Matakan Kariya Yayin Sake Buɗe Makarantu Afrika
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika

Ruwan Sama Yayi Ajalin Daruruwan Mutane A Afirka Ta Kudu
Published: January 17, 2026 at 10:41 AM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: January 18, 2026

Hukumomi a Afirka ta Kudu sun ce ruwan sama me karfi da ambaliyar ruwa ya yi sanadiyar rayukan mutane fiye da dari a kasashen Afirka ta Kudu, Mozambique, da Zimbabwe a makonnin nan, kuma sun yi gargadin sake samun mummunan yanayi a fadin yankin na kudancin Afirka.

Jiragen sojoji masu saukar ungulu sun kubutar da mutane da suka fake a saman gidaje, yayin da ake ceto daruruwan ‘yan yawon bude ido daga wani babban wurin aje namun daji da yake daya daga cikin mafi girma a duniya.

Kasar Mozambique ce ta fi shan bugu, inda aka samu ambaliyar ruwa da ya ratsa yankunan ta na tsakiya da Lardukan da ke kudancin kasar kuma ma’aikatar lura da lalacewar yanayi da rage hadurra ta kasar ta ce mutane 103 ne suka rasa rayukan su sakamakon yanayi na ruwan sama me karfi tun shekarar da ta gabata, duk da mutuwar ta kunshi wasu dalilai da ban da ya hada da fadowar aradu, fadowar gine-gine, da nutsewa a ruwa sakamakon ambaliya.

Abin ya Shafi fiye da mutane 200,000 a Mozambique, dubbanan gidaje sun lalace ba zasu zaunu ba, a kasar da talauci ya riga ya yi katutu, ga karancin ababen more rayuwa, da ta sha fuskantar iskar guguwa mai karfi da aikata barna a cewar hukumar shirin samar da abinci ta duniya.

Afrika

Post navigation

Previous Post: Trump Zai Sasanta Tsakanin Masar Da Habasha
Next Post: Rikici Ya Lafa A Kasar Iran Bayan Daukar Matakai

Karin Labarai Masu Alaka

Mabiya Dariqar Tijjaniyya Sunfara Gudanar Da Addu’oi Saboda Tsare Sheikh Sani Khalifa Zariya Afrika
‘Yan Bindiga Sun Kashe Dan Gaddafi A Gidansa Dake Kasar Libya Afrika
Maulidi: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranar Hutu Afrika
An Kama Masu Fasa Kaurin Gawayi A Malawi Afrika
Fargaba Ta Karu Duk Da Tsagaita Wuta Tsakanin Iran Da Amurka Afrika
Gwamnatin Kasar Ghana Ta Rage Farashin Cocoa Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Inuwa Ya Bukaci A Kara Zuba Jari A Ilimin Sana’o’i Domin Samar Wa Matasa Aikin Yi
  • Gwamnonin Arewa Sun Yi Jimamin Rasuwar Bamanga Tukur, Sun Yaba Da Gudunmawarsa Ga Najeriya
  • Tsohon Shugaban PDP, Bamanga Tukur, Ya Rasu Yana da Shekaru 91
  • Filato: Gwamnati Ta Ƙarfafa Matakan Kariya Yayin Sake Buɗe Makarantu
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Donald Trump Yace Basu Cimma Matsaya Da Benjamin Natanyahu Ba Afrika
  • Kasar Kenya Zata Samar Da Makamashi Labarai
  • Farashin Man Fetur Yakara Tashi Labarai
  • Anyi Rashin ‘Yan Jarida 6 A Jihar Gombe Sakamakon Hatsarin Mota Labarai
  • Shugabannin Darikar Anglican Sun Bada Sanarwar Kafa Sabuwar Majalisa Afrika
  • Amurka Zata Kamallah Yaki Da Iran A Makonni Biyu Masu Zuwa Amurka
  • Mayakan RSF Sun Zafafa Kai Hare Hare Da Jirgi Maras Matuki A Sudan Labarai
  • Gobara Ta Tashi A Hukumar FIRS Dake Abuja Najeriya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.