Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

Bayan Rikicin Manoma Da Makiyaya, Kwamitin White Paper Ya Ziyarci Bojude Da Kwami
Published: July 15, 2026 at 6:47 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnatin jihar Gombe dake arewa maso Gabashin Najeriya ta sake jaddada aniyarta na tabbatar da zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya ta hanyar ƙarfafa matakan kare hanyoyin kiwo da kuma dazukan kiwo domin rage rikice-rikicen da ke faruwa tsakanin bangarorin biyu.

Wannan na ƙunshe ne cikin ziyarar duba aiki da Ƙaramin Kwamitin Aiwatar da Rahoton White Paper kan Hanyoyin Kiwo ya kai garin Jauro Jibir da ke Kwami, gundumar Bojude, da kuma Filin Kiwo na Ƙasa da Ƙasa na Kwalale da ke yankin Daban Fulani a jihar Gombe

Da yake jawabi ga al’ummar yankunan, ɗaya daga cikin mambobin kwamitin, Ardo Chindo Abubakar, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta umarci jama’a, musamman manoma, da su guji noma a cikin hanyoyin kiwo da filayen kiwo da aka keɓe domin wannan manufa.

Ya ce filayen kiwo mallakin Gwamnatin jihar Gombe ne, kuma an ware su ne domin kiwon dabbobi, yana mai cewa kiyaye su zai taimaka wajen rage rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya tare da tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa.

A nasa jawabin, Hakimin Bojude, Alhaji Ibrahim Dan Buram, da Hakimin Daban Fulani, Alhaji Muhammad Seyo, sun buƙaci al’ummominsu da su mara wa manufofin gwamnatin jihar baya tare da bai wa Kwamitin Aiwatar da Rahoton White Paper cikakken haɗin kai domin cimma nasarar aikin da aka ɗora masa.

Hakiman sun kuma shawarci jama’a da su kasance masu bin doka da oda, su guji duk wani abu da ka iya kawo tashin hankali ko ɓata sunan al’ummominsu da addininsu.

A nasa jawabin, Shugaban Ƙaramar Hukumar Kwami, wanda shugaban Sashen Noma na ƙaramar hukumar, Muhammad Ibrahim Bojude, ya wakilta, ya yi kira ga jama’a, musamman manoma da makiyaya, da su mutunta dokokin da suka shafi hanyoyin kiwo tare da ba kwamitin cikakken goyon baya da haɗin kai.

Ya ce haɗin kan gwamnati, sarakunan gargajiya, manoma da makiyaya zai taimaka matuƙa wajen samar da zaman lafiya da bunƙasa harkokin noma da kiwo a Jihar Gombe.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sana'o'i, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Kano: Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Amince da Garo A Matsayin Mataimakinsa Na 2027
Next Post: Ƙungiyar Mata Sunyi Kira Ga Jam’iyar P R P Da Ta Dauki Baheejja A Matsayin Mataimakiyar Gwamnan A Bauchi 2027

Karin Labarai Masu Alaka

Rundunar Tsaron Haɗin Gwiwa Ta Arewa Maso Gabas Ta Kashe Fiye Da ‘Yan Ta’adda 438 Labarai
Sunayen Jakadu: Kungiyar CISLAC Ta Nemi A Janye Sunan Mr. Ayodele Oke Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Kwamitin Aikin Hajjin Najeriya Ya Shigar Da Korafi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
ECOWAS Zata Taimakawa Kasar Benin Da Dakarun Soji Afrika
Babban Sakataren MDD Yayi Allah Wadai Da Matakin Soja A Gabas Ta Tsakiya Afrika
Rundunar Sojin Najeriya Ta Dakile Harin ‘Yan Ta’adda A Jihar Borno Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Nijar: Zamu Tsananta Bincike A Bakin Iyakokin Mu Afrika
  • Tinubu: Abba Magajin Aminu Kano Ne A Fagen Siyasa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Wani Bincike Ya Nuna Cewar Da Wuya Iran Ta Bude Mashigin Hormuz Afrika
  • Bayan Shafe Shekaru Hudu A Mulki Sarkin Hausawan Ibadan Ya Rasu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya Ta Kai Wasan Kusa Da Na Karshe A Wasan Dambe Na Matasan Afirka Wasanni
  • APC: Tinubu Da Shettima Za Su Sake Neman Wa’adi Na Biyu A 2027 Afrika
  • Guterres: Babban Kuskure Ne Yadda Isra’ila Ta Kai Farmaki A Gaza Labarai
  • Tinubu: Zamu Kara Kyautata Samar Da Kayan Aiki Ga Jami’an Tsaro Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.