Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

Iran Zata Shigar Da Lebanon Cikin Cimma Yarjejeniya
Published: March 26, 2026 at 9:50 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Iran ta sanarwa masu shiga tsakani cewa, dole ne a haɗa da ƙasar Lebanon a cikin duk wata yarjejeniyar tsagaita wuta da za a cimma da Amurka da Isra’ila, kamar yadda wasu majiyoyi shida daga yankin da suka san matsayin Iran suka bayyana. Hakan na nuni da cewa, kawo ƙarshen yaƙin yana da alaƙa da dakatar da hare-haren Isra’ila kan ƙungiyar Hezbollah.

Tashar Press TV ta Iran ta rawaito a jiya Laraba cewa wani jami’in Iran ya ce Tehran na son duk wata yarjejeniya da Amurka ta tabbatar da kawo ƙarshen yaƙin, ba kawai a kanta ba har ma da sauran ƙungiyoyin “gwagwarmaya” a yankin.

Wani babban jami’in Iran ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters duk a jiya Laraba cewa, har yanzu Tehran na nazarin shawarar Amurka na kawo ƙarshen rikicin yankin, da ya kwashe kusan wata guda yana gudana, abin da ke nuna cewa Iran ba ta yi watsi da shawarar gaba ɗaya ba har yanzu.

Majiyoyi shida daga yankin, waɗanda suka nemi a sakaya sunayensu saboda muhimmancin batun, sun ce Tehran ta sanar da masu shiga tsakani tun daga tsakiyar watan Maris cewa, tana neman yarjejeniya da za ta kuma dakatar da hare-haren Isra’ila kan ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon.

Afrika, Amurka, Labarai

Post navigation

Previous Post: Iran Tana Duba Yiwuwar Cimma Yarjejeniya Da Amurka
Next Post: Rasha Ta Yiwa Amurka Tayin Daina Bada Bayanan Sirri

Karin Labarai Masu Alaka

CAF Ta Hukunta Samuel Eto’o AFCON 2025 Labarai
Sanata Goje Yayi Watsi Da Fidda ‘Yan Takarar APC A Gombe Afrika
Jami’an Tsaro A Jihar Borno Sun Kama ‘Yan Bindiga Labarai
Atiku Ya Bukaci Hadin Kan ‘Yan Adawa Domin Kawo Sauyi A Najeriya Afrika
An Sako Dan Siyasar Kasar Venezuela Daga Gidan Yari Labarai
Wani Dan Bindiga Ya Harbi Dakarun Tsaron Cikin Gida Su Biyu A Washington DC Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kungiyar Enyimba: Bamu Da Niyyar Rage Albashin ‘Yan-Wasa Wasanni
  • Ana Cigaba Da Bincike Game Da Mutuwar Matar Da Likita Ya Manta Almakashi A Cikinta A Kano Najeriya
  • Jihar Kano Tayi Rashin ‘Yan Majalisu Biyu Najeriya
  • Majalisa Ta Tabbatar Da Murtala Sule Garo A Matsayin Mataimakin Gwamnan Kano Afrika
  • ‘Yan-Ta’adda Sun Yi Ma Wasu Mutane Yankan Rago A Jihar Neja Labarai
  • Wakilan Majalisar Dokokin Phillipines Suna Yunkurin Tsige Shugaban Kasar Afrika
  • Iran Tana Duba Yiwuwar Cimma Yarjejeniya Da Amurka Afrika
  • Hukumar IMF Tana Naziri Domin Kara Bada Lamuni Ga Kasar Zambiya Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.