Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

An Murkushe Wani Yunkurin Juyin Mulki A Jamhuriyar Benin
Published: December 7, 2025 at 3:20 PM | By: Yusuf Aliyu Harande

Gwamnatin Jamhuriyar Benin ta ce dakarun sojojinta sun murkushe wani yunkurin juyin mulki, a bayan da wasu sojoji suka fito cikin tashar telebijin ta ƙasar suna iƙirarin kwace mulki.

Wannan yunkurin juyin mulki na baya bayan nan a yankin Afirka ta Yamma, inda sojoji suka kwace mulki a makwabtan Benin, watau Nijar da Burkina Faso, da kuma a ƙasashen Mali da Guinea-Conakry.

Ko a watan da ya shige ma, sojojin sun kwace mulki a kasar Guinea-Bissau.

Da sanyin safiyar yau lahadi, sojoji akalla 8 suka fito a gidan telebijin na kasar, wasu ɗauke da bindigogi, su na sanar da cewa wani kwamitin soja a karkashin jagorancin Kanar Tigri Pascal, ta karɓe ragamar mulkin ƙasar, tare da dakatar da yin aiki da tsarin mulki da kuma rufe bakin iyakokinta ta sama da kasa da ta ruwa.

‘Yan sa’o’i kaɗan a bayan wannan, ministan harkokin cikin gidan Benin, Alassane Seidou, ya fito a telebijin na ƙasa yana fadin cewa rundunar sojoji ta murkushe juyin mulkin.

Seidou yayi kira ga jama’a da su fito su ci gaba da gudanar da ayyukansu na yau da kullum.

Wani kakakin gwamnatin Jamhuriyar Benin, yace ya zuwa yammacin nan agogon kasar, an kama mutane akalla 14 dangane da yunkurin juyin mulkin.

Afrika, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Post navigation

Previous Post: Gwamnatin Kasar Benin Ta Nemi ‘Yan Kasa Su Kwantar Da Hankali
Next Post: ECOWAS Zata Taimakawa Kasar Benin Da Dakarun Soji

Karin Labarai Masu Alaka

Jam’iyyu Shida Sun Shiga Zaben Kananan Hukumomin Gombe – GOSIEC Afrika
Shugaban Kare Hakkin Dan Adam Na Majalisar Dinkin Duniya Yace RSF Sun Aikata Zalunci Afrika
Amurka Da Tarayyar Turai Sun Fidda Sanarwa Afrika
Pakistan Zata Karbi Tattaunawar Rikicin Gabas Ta Tsakiya Afrika
Farashin Danyen Mai Da Iskar Gas Ya Tashi Afrika
Pakistan Zata Karbi Bakwancin Saudiya, Turkiyya Da Masar Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Farashin Mai Ya Cigaba Da Tashi Afrika
  • An Gano Wasu Boma Bomai Da Aka Binne A Jihar Neja Najeriya
  • RSF Ta Kasar Sudan, Tana Yin Garkuwa Da Mazauna A Yankin Darfur Afrika
  • Wasu Zakaru Da Suka Samu Karramawar Hukumar CAF Ta Afrika Wasanni
  • Shugabannin Kiristoci Sun Taya Musulmi Murnar Sallah Domin Ƙarfafa Zaman Lafiya Afrika
  • Kasar Amurka Takara Saka Takunkumi Akan Kasar Venezuela Amurka
  • Iran Zata Sassauta Shirin Nukiliya Tsakaninta Da Amurka Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya: Ba Don Leken Asiri Muka Tura Jirgin Yakin Mu Ba Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.