Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Kurdawa Sun Gargadi ‘Yan Uwansu Game Da Alaka Da Amurka Wajen Yakar Iran
Published: March 9, 2026 at 3:58 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

A halin da ake ciki, Kurdawan kasar Sham ko Syria, sun gargadi ‘yan’uwansu na kasar Iran da kada su yarda su kulla kawance da Amurka wajen yakar Gwamnatin Iran.

Kurdawan na kasar Syria sun yi misali da irin halin da suka samu kansu a ciki, suna masu fadin cewa za a yi amfani da su ne kawai a kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters yace rundunonin sa kai na Kurdawan Iran dake zaune a yankin arewacin Iraqi, sun gana a lokuta da dama da wakilan Amurka a cikin ‘yan kwanakin nan a kan kai farmaki kan dakarun kasar Iran a yankin yammacin kasar, yayin da Amurka da Isra’ila ke kai hare-hare ta sama.

Amma Kurdawan Syria, wadanda suka yi kawance da Amurka sun ja kunnen ‘yan’uwansu na Iran cewa za a jefa su a rana, a bar su, kamar yadda Amurka ta yi ma Kurdawan na Syria.

Wani Bakurde mai shekaru 45 mazaunin garein Qamishli na Kurdawa a arewa maso gabashin Syria, ya jaddada gargadi ga Kurdawan Iran cewa kada su yi kuskuren da Kurdawan Syria suka yi.

Afrika, Amurka, Labarai, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Majalisar Kwararrun Iran Ta Sanar Da Sabon Shugaban Addini
Next Post: Rundunar Sojin Iran Tace Harin Amurka Ya Kashe Musu Sama Da Mutane Dari

Karin Labarai Masu Alaka

An Gano Wani Kurkukun Sirri Da Ake Azaftar Da Mutane A Kasar Libya Afrika
Masar Ta Kayyade Farashin Buradi A Kasar Afrika
CP Chuso Ya Jaddada Muhimmancin Haɗin Gwiwar Hukumomin Tsaro A Gombe Afrika
Tashoshin Mai Basa Iya Loda Mai A Rasha Labarai
Kamfanonin Jiragen Sama Suna Fama Da Karin Farashin Mai Labarai
Iran Tace Farisa Zata Kai Hari Kan Mayakan Amurka Amurka

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugaba Trump Yace Akwai Yiwuwar Cimma Yarjejeniya Da Iran Afrika
  • Majalisar Wakilai Tayi Allah Wadai Da Hare-Haren ‘Yan Bindiga A Gombe Labarai
  • Ukraine Ta Aika Tawagar Kwararru Gabas Ta Tsakiya Afrika
  • Harin Bom Din Maiduguri Ya Kashe Mutane Biyar Ya Raunata Fiye Da Talatin Najeriya
  • Amurka Tafara Yiwa Kasar Iraq Barazana Amurka
  • Kasashen Amurka Da China Sun Matsawa Ghana Domin Rage Kudaden Haraji Afrika
  • Amurka Ta Gabatarwa Sassan Dake Yakar Juna A Sudan da Shirin Tsagaita Wuta Afrika
  • Tinubu: Munsayi Jiragen Yaki Daga Wajen Amurka Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.