Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Dawo Da Kudaden Ma’aikata
Published: May 8, 2026 at 5:01 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: May 8, 2026

Gwamnatin jihar Kano a Najeriya ta kafa wani kwamitin mutum 12 domin dawo da naira biliyan 1.8 da aka ce an cire ba bisa ƙa’ida ba daga albashin ma’aikatan gwamnati ta hannun kamfanonin bada lamuni masu zaman kansu.

Haka kuma gwamnatin ta dakatar da duk wata sabuwar yarjejeniyar rance tsakanin ma’aikatan gwamnati da kamfanonin lamunin, tana mai cewa daga yanzu ba za ta ƙara shiga tsakani a irin waɗannan yarjejeniyoyi ba.

Sakataren Gwamnatin Jiha, Umar Faruq Ibrahim, ya bayyana cewa wani bincike mai zaman kansa ya gano yadda wasu kamfanonin bada lamuni ke cire kuɗi daga albashin ma’aikata fiye da yadda doka ta tanada.

A cewarsa, dokar ta amince ne kada a cire fiye da kaso ɗaya bisa uku na albashin ma’aikaci, amma binciken ya nuna an karya wannan ƙa’ida.

Ya ce Majalisar Zartarwar Jihar ta amince da rahoton binciken tare da bai wa kwamitin da Kwamishinan Kuɗi, Ismaila Aliyu Danmaraya, ke jagoranta umarnin gano duk ma’aikatan da lamarin ya shafa, ko suna raye ko sun rasu, domin mayar musu da kuɗaɗensu.

SSG ɗin ya kuma bayyana cewa binciken ya wanke tsohon Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar, Abdullahi Musa, daga zargin hannu a badakalar.

Ya ƙara da cewa tun farko an yi kuskuren bayyana cewa kuɗin da suka ɓace sun kai naira biliyan 1.5, sai dai binciken ya tabbatar da cewa adadin ya kai naira biliyan 1.8.

Gwamnatin ta kuma nuna damuwa kan yadda ma’aikata ke ci gaba da karɓar lamuni daga kamfanoni masu zaman kansu, inda ta bayyana cewa jimillar bashin da ake bin ma’aikatan gwamnati a yanzu ya kai kusan naira biliyan 13.

Afrika, Labarai, Najeriya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Ana Kokarin Kawo Karshen Matsalar Kashe Matafiya A Filato
Next Post: Rundunar Operation Endurance Peace Ta Gano Wajen Kera Makamai A Jihar Filato

Karin Labarai Masu Alaka

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane A Katsina Afrika
Harin ‘Yan Daba Ya Hallaka Mutane 70 A Kasar Haiti Labarai
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Ya Gana Da Shugaba Tinubu Siyasa
Tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso Ya Fice Daga NNPP Afrika
Kasar Belarus Zata Taffawa Jamhuriyar Nijar Afrika
Ana Cigaba Da Yaki Tsakanin Amurka Da Isra’ila Da Kasar Iran Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugaba Trump Ya Bukaci A Cigaba Da Zanga Zanga A Iran Labarai
  • Amurka Tana Cigaba Da Kare Jami’in Da Ya Kashe Ba Amurke Amurka
  • Kotu A Kasar Tunisiya Ta Daure Wani Babban Dan Kasuwa Da Wasu ‘Yan Majalisa Afrika
  • Babu Alamar Tsagaita Wuta A Yaki Da Akeyi Tsakanin Isra’ila Da Amurka Afrika
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Kasar Malawi Ta Kaddamar Da Rigakafin Shan Inna Kiwon Lafiya
  • Amurka Zata Aika Jiragen Yaki Biyu Gabas Ta Tsakiya Amurka
  • Masar Ta Kayyade Farashin Buradi A Kasar Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.