Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

Iran Tace Jakadan Kasar Ta A Lebanon Zai Cigaba Da Zama A Beirut
Published: March 30, 2026 at 6:31 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: March 30, 2026

Kasar Iran ta ce a yau Litinin jakadan ta a kasar Lebanon zai ci gaba da zama a ofishin sa a Beirut, inda tayi watsi da umarnin da ma’aikatar kasashen waje ta Lebanon ta bayar na ya fice daga kasar bata bukatar sa.

Yakin da ake tafkawa tsakanin kungiyar Hezbolla na Lebanon da Isra’ila ya kawo zaman tsami tsakanin gwamnatin Lebanon da Hezbolla da Iran ke marawa baya, inda gwamnatin ke sukar Hezbolla kan shigar da Iran yaki.

A makon da ya gabata ne ma’aikatar harkokin waje ta Lebanon ta bawa Jakadan Iran Mohammed Reza Shibani zuwa 29 ga wannan watan da ya fice daga kasar, saboda ya sabawa tsarin diplomasiyya, ta tofa bakin sa kan harkokin siyasar cikin gida na Lebanon.

Kakakin majalisar Lebanon Nabih Berry, kuma, wanda yake dan Shi’a ne, kuma me goyon bayan Hezbolla, ya kalubalanci shawarar da ma’aikatar harkokin wajen ta yanke, inda yace Shibani yayi zaman sa.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin waje ta Iran ma Esma’il Baghaei, yace Shibani zai ci gaba da zama a Beirut.

Afrika, Labarai, Sauran Duniya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Kasar Spain Ta Rufe Sararin Saman Kasar
Next Post: Sojojin Amurka Sunfara Isowa Gabas Ta Tsakiya

Karin Labarai Masu Alaka

Tsofin Ma’aikatan Gwamnati Sunyi Zanga Zanga A Jihar Neja Labarai
Kenya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kasar Rasha Afrika
Shugaba Yoweri Musevini Ya Zamo Shugaban Uganda Na 7 Yana Da Shekaru 81 Kuma Ya Shafe Shekaru 50 A Mulki Labarai
Shugaba Tinubu Yasa Hannu Kan Dokar Kasafin 2026 Afrika
Rasha Da Ukraine Sun Cigaba Da Yakar Juna Afrika
Zaben Fidda Gwani Ya Gudana Lafiya A Jihar Gombe Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Dan Gaddafi A Gidansa Dake Kasar Libya Afrika
  • Wasan Dambe Ya Dau Sabon Salo A Jihar Inugu Wasanni
  • Majalisar Dattawar Najeriya Ta Amince Da Tura Sakamakon Zabe Ta Intanet Labarai
  • An Bukaci Sabbin Shugabanni Su Yi Jagoranci Nagari da Inganta Ayyukan Jama’a Labarai
  • Kasar Jamus Ta Haramtawa Yara Kasa Da Shekaru 14 Hawa Dandalin Sada Zumunta Labarai
  • ‘Yan Sandan Gombe Sun Fara Kama Motocin Da Ba Su Da Lambar Rajista ko Masu Boye Lambobinsu Afrika
  • Hawan Babbar Sallah A Masarautar Kaltungo Dake Jihar Gombe Afrika
  • Kasar Iran Zata Kai Hare Haren Ramuwar Gayya Isra’ila Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.