Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama Afrika
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara Afrika
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe Afrika
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro Afrika
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa Afrika

Nnamdi Kanu Zai Daukaka Kara Har Zuwa Kotun Koli
Published: November 21, 2025 at 4:50 AM | By: Yusuf Aliyu Harande

Mukarraban shugaban ‘yan awaren Biyafara Nnamdi Kanu sun yi alwashin daukaka kara biyo bayan yanke ma sa hukuncin daurin rai da rai a babbar kotun tarayya ta yi.

Daya daga lauyoyi na kan gaba wajen kare Kanu, Aloy Ejimakor ya bayyana wannan muradi da zayyana cewa har kotun koli za su iya zuwa don bin kadin hukuncin.

Ba ma wani abun mamaki ba ne aniyar mukarraban na Kanu na daukaka kara don tun gabanin yanke hukuncin na alkalin babbar kotun James Omotosho, su ka bukaci kotun daukaka kara ta sa baki don a sake bude shari’ar da sauraron Kanu duk da ya tsaya kai da fata cewa shi ba zai bude kariya ba don ya na ganin bai aikata laifi ba kan dokar da a ke yi ma sa shari’a a kai.

“Mazi Nnamdi Kanu ya yada magana a kafar labaru, to sai me har a ka yanke ma sa hukunci kan tuhumar ta’addanci” Inji Aloy Ejimakor da ke cewa ba inda kalaman da Kanu ya yi su ka hada hanya da ko marin wani.

“Dagan an za mu tafi kotun daukaka kara, don ita ce kotu ta gaba da za ta duba shari’ar nan a tsarin dokokin kasar nan. Za mu fuskanci alkalai a can don su duba abun da ya faru a kotu yau. Kuma mu na da yakini alakalai za su amince da cewa an keta haddin adalci a hukuncin da a ka yanke. Idan kotun daukaka kara ba ta amince da mu ba za mu wuce kotun koli” Inji Ejimakor a jawabin da ya yi wa manema labaru bayan yanke hukuncin.

In a na bin shari’ar dai, alkalin babbar kotun tarayya James Omotosho ya samu Kanu da laifi a dukkan caji 7 da sashen gabatar da kara ya gabatar.

In ka debe caji na 2 da na 6 da Omotosho ya daure Kanu shekara 20 da kuma 5, sauran su ne na rai da rai

James Omotosho ya ce da ya biyewa laifin Kanu mai girman kai da rashin nadama hukuncin kisa zai yanke ma sa amma ya duba sura ta 23 aya ta 23 a littafin Matta da ke magana kan tausayawa ko mutunta rai ” na yankewa wanda a ka samu da laifi hukuncin daurin rai da rai kan laifi na 1, 4. 5 da na 6 maimakon hukuncin kisa”

Sai da ta kai ga alkalin ya umurci jami’an DSS su fitar da Kanu daga kotun don yanda ya nemi tada hanyaniya da ma farmaki kan jami’an tsaro.

In za a tuna an zargi Kanu da amfani da kafar labarunsa ta Rediyo Biyafara wajen tunzura magoya bayansa a kudu maso gabar inda rundunarsa ta mayakan ESN su ka kashe adadi da yawa na jami’an tsaro da fararen hula ciki har da  mai ba wa tsohon shugaba Jonathan shawara kan shari’a Barista Ahmad Gulak.

Hukumar zabe ta sha yin korafi kan yanda ‘yan awaren Biyafara na IPOB ke yunkurin kawo cikas wajen gudanar da zabe a jihohin kudu maso gabar duk da jami’an tsaro kan jajirce don tabbatar da doka da oda.

Jami’ar labaru ta hukumar zaben Zainab Aminu ta kan fayyace yanda ma’aikatansu kan samu barazana daga ‘yan IPOB.

Alkali Omotosho ya umurci a tsare Kanu a wajen da ya dace da yanayinsa na mai tashintashina da kuma a karbe na’urorin rediyonsa a sarayar da su ga gwamnatin tarayya.

An samu labarin jibge jami’an tsaro a gewayen gidan gwamnatin Abia da nan ne jihar su Nnamdi Kanu don alamun kauda barar duk wata hatsaniya.

Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Post navigation

Previous Post: Ba Shakka Najeriya Zata Iya Shiga Gasar Harbi Ta Duniya
Next Post: Shugaban Guinea-Bissau Umaro Na Fuskantar Matsin Lamba

Karin Labarai Masu Alaka

Jihohin Arewaci Sun Kafa Asusun Yaki Da Ta’addanci Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
CP Chuso Ya Yaba da Matakan Gwamnatin Gombe Wajen Rage Rikicin Makiyaya Da Manoma Afrika
‘Yan Bindiga Sun Kama Akalla Mutane 13 A Wani Coci A Jihar Kogi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Musa: “Da Yaddar Allah Zamu Ga Bayan Ta’addanci A Najeriya” Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
‘Yan Sandan Habasha Sun Kama Dubban Albarusai Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
AIG Kwaimo Ya Kai Ziyarar Aiki Gombe, Ya Buƙaci Ƙara Ƙaimi A Yaƙi Da Ta’addanci Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gwamnatin Amurka Na Kokarin Watsi Da Tsohuwar Dokar Jones Labarai
  • Ƙungiyoyin Premier 17 Za Su Rasa ‘Yan Wasa 40 saboda Gasar AFCON 2025, Wasanni
  • ‘Yan Tawayen M23 Masu Samun Goyon Bayan Rwanda Basu Jamye A Ulvira Ba Labarai
  • JEI Da Abokan Hulɗar Sun Gudanar Da Aikin Shuka Itatuwa Domin Bikin Ranar Muhalli Ta Duniya Afrika
  • Amurka Zata Bada Gudunwa Ga Masu Zanga-Zanga A Iran Sauran Duniya
  • CP Chuso Ya Yaba da Matakan Gwamnatin Gombe Wajen Rage Rikicin Makiyaya Da Manoma Afrika
  • Jirgin Sojojin Ruwa Yayi Gobara A Cross River Najeriya
  • Ana Cigaba Da Ceto Masunta Daga Ruwa A Ghana Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.