Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

CP Chuso Ya Yaba da Matakan Gwamnatin Gombe Wajen Rage Rikicin Makiyaya Da Manoma
Published: July 13, 2026 at 6:33 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar Gombe, CP Umar Ahmed Chuso, ya ce ci gaba da tattaunawa da kuma daukar matakin gaggawa kan matsalolin da ke tasowa shi ne mafita wajen hana rikice-rikicen makiyaya da manoma a jihar.

CP Chuso ya bayyana haka ne yayin taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan rikicin makiyaya da manoma da aka gudanar a Hedikwatar Rundunar ‘Yan Sandan jihar Gombe.

Ya ce idan shugabannin al’umma a matakai daban-daban suka rika magance matsalolin tun kafin su rikide zuwa rikici, za a samu raguwar rikice-rikicen makiyaya da manoma.

Kwamishinan ‘yan sandan ya bayyana cewa dalilan rikicin makiyaya da manoma sun bambanta daga wannan yanki zuwa wani, don haka akwai bukatar duk masu ruwa da tsaki su hada kai wajen samar da mafita mai dorewa.


Ya yabawa Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, bisa kafa kwamitocin sasanta rikice-rikice a matakai daban-daban, yana mai cewa hakan ya taimaka wajen rage nauyin da ke kan rundunar ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

Taron ya tattauna kan muhimman batutuwa da suka hada da mamaye hanyoyin shanun kiwo, samar da wuraren kiwo na zamani (ranches), zirga-zirgar dabbobi daga jiha zuwa jiha domin kiwo, da kuma hanyoyin gaggauta kai rahoton duk wata matsala domin daukar matakin da ya dace cikin lokaci.


Taron ya samu halartar sarakunan gargajiya, shugabannin addinai, shugabannin makiyaya na Fulani da suka Gudanar da jawabai amadadin mabiyansu Daga dukkan Sassan jihar Gombe da kuma manyan jami’an rundunar ‘yan sanda daga kananan hukumomi goma sha daya na jihar Gombe, domin karfafa hadin gwiwa wajen tabbatar da zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Shugabannin Kiristocin Arewa Sun Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga Iyalan Ummulkhairi
Next Post: An Bude Gasar Bauchi Annual International Polo 2026

Karin Labarai Masu Alaka

Kasar Congo Ta Dau Alwashin Bin Tsari Wajen Rarraba Ma’adanai Afrika
Babban Hafsan Tsaron Najeriya Ya Gargadi Jama’ar Arewa Maso Gabas Afrika
Najeriya, Sojoji Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Sama Da 80, Sun Ceto 34 Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Jakadan Kasar Sin a Najeriya Ya Ziyarci Tinubu Najeriya
Nigeria Zata Bude Asusun Dala Bilyan Biyu Don Habaka Sashin Makamashi Labarai
Kotu Ta Bada Belin Nasiru El Rufai Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Dillalan Mai Suna Fuskantar Karancin Mai Sakamakon Yakin Amurka Da Iran Afrika
  • Kotu A Birnin Tarayya Abuja Ta Bada Belin Tsohon Minista Abubakar Malami Najeriya
  • APC: Tinubu Da Shettima Za Su Sake Neman Wa’adi Na Biyu A 2027 Afrika
  • Majalisar Dottawa Ta Kafa Komitin Dokar Zabe Najeriya
  • Mayakan ISWAP Sun Kai Farmaki Kan Sojojin Najeriya Najeriya
  • Gwamnan Gombe Ya Ƙara Tallafin N148.76bn Domin Aiwatar da Sabon Tsarin Albashi A Jami’ar Gombe Afrika
  • Anyi Taho Mugama Tsakanin ‘Yan Sandan Turkiyya Da ‘Yan Kungiyar ISIS Afrika
  • Rivers: ‘Yan Majalisa 16 Sun Canza Sheka Zuwa APC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.