Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

Kotu Ta Bada Belin Nasiru El Rufai
Published: May 18, 2026 at 10:21 AM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: May 18, 2026

Kotu ta bayar da belin Nasir El-Rufai kan Naira miliyan 100

Wata babbar kotu da ke Abuja a Najeriya bayar da beli ga tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, kan zargin karan tsaye ga tsaron kasa da ake yi masa.

Mai shari’a Joyce Abdulmalik, yayin yanke hukunci kan buƙatar beli a ranar Litinin, ta gindaya wasu tsauraran sharuɗɗa da El-Rufai zai cika kafin a sake shi.

Kotun ta umarce shi da ya kawo mutum guda da zai tsaya masa beli da adadin kuɗin iri ɗaya.

Kotun ta ce dole ne wanda zai tsaya masa ya kasance mazaunin yankin Maitama ko Asokoro a Abuja, sannan ya ajiye asalin takardar mallakar fili ko gida a ma’ajiyar kotu.

Haka kuma, wanda zai tsaya belin dole ne ya kasance ma’aikacin gwamnatin tarayya mai matsayi bai gaza mataki na 17 ba, tare da gabatar da shaidar biyan albashi na akalla watanni uku, wanda manajan bankinsa a yankin kotun ya tabbatar.

Kotun ta kuma umurci wanda zai tsaya masa ya rantse da takardar bayyana kadarori, ya sanya hannu kan yarjejeniyar beli tare da gabatar da sabon hoton fasfo a ma’ajiyar kotu.

A cikin sharuɗɗan belin, an umurci El-Rufai da ya miƙa duk wasu ingantattun fasfo na ƙasashen waje ga kotu.

Kotun ta kuma buƙaci a gabatar da wasiƙar tabbatarwa daga sashen aikin wanda ya tsaya belin, tare da takardar biyan haraji ta watanni shida da suka gabata.

Mai shari’a Abdulmalik ta kuma umurci wanda ake tuhuma da ya riƙa zuwa hedikwatar Hukumar Tsaro ta DSS a kowace Juma’ar ƙarshe ta wata da ƙarfe 10 na safe domin sanya hannu a rajistar halarta har sai an kammala shari’ar.

Alƙaliyar ta yi gargaɗin cewa rashin bin waɗannan sharuɗɗa zai sa a soke belin kai tsaye.

Kotun ta ƙara umurtar El-Rufai da ya gabatar da wasiƙar shaida daga Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Kaduna.

Haka kuma, kotun ta ba da umarnin a gaggauta sauraron shari’ar da gwamnatin Najeriya ta shigar a kansa.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Najeriya Da Jamus Sun Kulla Yarjejeniyar Zuba Jari
Next Post: Jami’an ‘Yan Sanda A Gombe Sun Kama Barayi

Karin Labarai Masu Alaka

Rundunar Tsaron Haɗin Gwiwa Ta Arewa Maso Gabas Ta Kashe Fiye Da ‘Yan Ta’adda 438 Labarai
Yeriman Ingila Ya Gana Da Yeriman Saudiya Mai Jiran Gado Amurka
Karancin Iskar Gas Kalubale Ne Ga Wutar Lantarki Labarai
Yajin Aikin Ma’aikatan Lafiya Na Shafar Harkokin Jinya A Asibitoci Kiwon Lafiya
Farashin Dalar Amurka Ya Tashi Ranan Juma’a Amurka
Jami’in Diflomasiyyar Da Ake Zargi Da Kisan Prime minister Ya Daukaka Kara Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Tinubu Ya Maye Gurbin Badaru Da Tsohon Soja Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Matatar Man Dangote Ta Kara Yawan Mai Dake Zuwa Kasashen Afirka Afrika
  • Mali Da Burkina Faso Za Su Haramta Wa Amurkawa Izinin Shiga Ƙasashen Su Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Jami’an tsaro sama da dubu biyar ne zasuyi aikin tabbatar da tsaro Alokacin bikin karamar sallah a Jihar Nejan Najeriya. Najeriya
  • China Ta Dawo Da Harajin Magungunan Hana Haihuwa Labarai
  • Shirin Dare 26.11.2025 Rediyo
  • Fintiri: Zamu Maida Jihar Adamawa Sabuwar Duniya Labarai
  • SERVICOM, ATBUTH Ta Cafke Wani Da Ake Zargin Dan Damfara Ne Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.