Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

Shugabannin Kiristocin Arewa Sun Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga Iyalan Ummulkhairi
Published: July 13, 2026 at 7:00 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Barista Solomon Dalung, ya jagoranci tawagar limaman Kirista da shugabannin matasan Kirista daga jihohi 19 na Arewacin Najeriya zuwa ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayiya Malama Ummulkhairi, wata Musulma da ake zargin an kashe ta ta hanyar dukan tsiya daga wasu fusatattun mutane a Maraban Jos, jihar Kaduna.

Tawagar ta ƙunshi fitattun limaman Kirista, wakilan ƙungiyoyin matasan Kirista na Arewa da masu rajin zaman lafiya. Sun kai ziyarar ne domin jajanta wa iyalan marigayiyar, yi musu addu’a tare da nuna goyon baya a wannan lokaci na jimami.

Mambobin tawagar sun bayyana cewa, ziyarar ta kuma kasance wata hanya ta ƙarfafa zaman lafiya, fahimtar juna tsakanin mabiya addinai da kuma girmama darajar rayuwar ɗan Adam ba tare da la’akari da addini ko ƙabila ba.

Da yake jawabi yayin ziyarar, Barista Solomon Dalung ya bayyana kisan a matsayin abin takaici da ke nuna illar rikicin taron jama’a da kuma ɗaukar doka a hannu.
Ya ce babu al’ummar da za ta samu zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa idan ana kashe mutane ba tare da bin tanadin doka ba.

Dalung ya jaddada cewa kowane ɗan Najeriya yana da haƙƙin samun adalci da sauraron shari’arsa kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, yana mai cewa babu wani mutum ko ƙungiya da ke da ikon zama alƙali, mai yanke hukunci da kuma mai aiwatar da hukunci a lokaci guda.

Ya ce, “Dole ne ɗan Adam ya kasance abin fifiko. Ya kamata mu daraja rayuwar kowane mutum ba tare da la’akari da addini, ƙabila ko matsayinsa a cikin al’umma ba. Tare za mu iya gina ƙasa inda ake neman adalci ta hanyar hukumomin da doka ta tanada, ba ta hanyar tashin hankali ba.”

Tsohon ministan ya buƙaci Gwamnatin Jihar Kaduna, hukumomin tsaro da sauran hukumomin da abin ya shafa su gudanar da cikakken bincike kan lamarin tare da gurfanar da waɗanda ke da hannu a gaban kotu.

Ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya, musamman matasa a jihohi 19 na Arewa, da su kwantar da hankulansu, su guji tashin hankali tare da ci gaba da inganta zaman lafiya, haɗin kai da mutunta juna tsakanin mabiya addinai daban-daban.

Shi ma da yake jawabi, Babban Faston Christ Evangelical and Life Intervention Ministry da ke Kaduna, Dakta Yohanna Buru, ya ce ziyarar ta nuna aniyar shugabannin Kiristocin Arewa na tsayawa tare da duk wanda aka zalunta ba tare da la’akari da addininsa ba.

Ya ce limaman Kirista da dama sun yi tattaki daga sassa daban-daban na Arewacin Najeriya domin jajanta wa iyalan marigayiyar, yana mai bayyana lamarin a matsayin abin takaici da ba za a amince da shi ba.

A cewarsa, dukkan addinai suna koyar da darajar rayuwar ɗan Adam, tausayi, yafiya da adalci.

Ya ce, “A matsayinmu na shugabannin addini, muna da alhakin yin Allah-wadai da duk wani nau’in tashin hankali da zalunci. Ɗaukar doka a hannu abu ne da ba za a amince da shi ba, kuma wajibi ne duk masu son zaman lafiya su yi Allah-wadai da shi.”

Pasto Buru ya buƙaci shugabannin addini, sarakunan gargajiya, ƙungiyoyin fararen hula da shugabannin al’umma su ƙara wayar da kan jama’a game da illar kisan gilla tare da ƙarfafa tattaunawa, haƙuri da warware rikice-rikice cikin lumana.

Haka kuma, Shugaban Ƙungiyar Northern Nigerian Christian Youth Professionals, Mista Isaak Abrak, ya yi kira ga matasan Arewa da su guji ɗaukar doka a hannu da kuma duk wani abu da ka iya kawo cikas ga zaman lafiya da haɗin kan al’umma.

Ya ce duk wata sabani ko zargi ya kamata a bi hanyoyin doka wajen warware shi, domin tashin hankali na ƙara rarrabuwar kai da raunana haɗin kan ƙasa.

Da yake mayar da martani a madadin iyalan marigayiyar, Mallam Aliyu, mijin marigayiya Malama Ummulkhairi, ya nuna matuƙar godiyarsa ga tawagar bisa ta’aziyya, addu’o’i da goyon bayan da suka nuna.

Ya ce ziyarar ta kawo wa iyalan kwanciyar hankali tare da nuna cewa mabiya addinai daban-daban na iya haɗuwa a lokacin jimami domin nuna tausayi da kuma tsayawa tare wajen yaƙi da zalunci.

An kammala ziyarar da gudanar da addu’o’i na neman Allah Ya gafarta wa marigayiya, Ya ba iyalanta haƙurin jure rashinta, tare da sake yin kira da a tabbatar da adalci, hukunta masu hannu a lamarin da kuma ci gaba da ƙarfafa haɗin kai tsakanin mabiya addinai domin hana aukuwar irin wannan lamari nan gaba.

Tawagar ta jaddada cewa kare rayuwar ɗan Adam da tabbatar da adalci nauyi ne da ya rataya a wuyan kowane ɗan Najeriya ba tare da la’akari da addini ko ƙabila ba.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: An Yaba Wa Gwamnatin Bauchi Bisa Karban Bakuncin Gasar Polo
Next Post: CP Chuso Ya Yaba da Matakan Gwamnatin Gombe Wajen Rage Rikicin Makiyaya Da Manoma

Karin Labarai Masu Alaka

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Yace Rahoton Kasashe Biyar Akan Rasha Yana Dauke Da Damuwa Amurka
Sojojin Najeriya Sun Kwato Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Najeriya
Shugabannin Darikar Anglican Sun Bada Sanarwar Kafa Sabuwar Majalisa Afrika
Amurka Ta Sanya Hanu Kan Yarjejeniyar Kiwon Lafiya Da Ƙasashen Madagascar, Saliyo, Botswana, Ethiopia Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Shugaban Kasar Brazil: Yakamata Amurka Ta Gurfanar Da Shugaban Venezuela A Kotu Afrika
Shugaba Trump Yace Zai Dakatar Da Kai Hari Cibiyar Makamashin Iran Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Amurka Ta Kakaba Takunkumi Ga Kwamandojin Yakin Kasar Sudan Sauran Duniya
  • Ministan Yaɗa Labarai: Ceto Daliban Neja An Samu Natsuwa A Kasa Labarai
  • Shugaba Trump Yace Amurka Zata Janye Yaki Da Iran Afrika
  • Magoya Bayan Obi Sun Yi Tutsu Gabanin Zaben 2027 Siyasa
  • Hadakar Gwamnatin Najeriya Da Amurka Ne Suka Kai Hari Sokoto Najeriya
  • An Kashe Mutane 169 A Wani Harin Sudan Ta Kudu Afrika
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe Afrika
  • Tinubu, Akpabio da Ministoci 9 Zasu Tafi Ƙasar Birtaniya Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.