Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Inuwa Ya Bukaci A Kara Zuba Jari A Ilimin Sana’o’i Domin Samar Wa Matasa Aikin Yi Afrika
  • Gwamnonin Arewa Sun Yi Jimamin Rasuwar Bamanga Tukur, Sun Yaba Da Gudunmawarsa Ga Najeriya Afrika
  • Tsohon Shugaban PDP, Bamanga Tukur, Ya Rasu Yana da Shekaru 91 Afrika
  • Filato: Gwamnati Ta Ƙarfafa Matakan Kariya Yayin Sake Buɗe Makarantu Afrika
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika

Kotun Kasar Rasha Ta Daure Dan Kasar Belarus Shekarar 22 A Kurkuku
Published: December 18, 2025 at 8:08 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Wata kotun soja a kasar Rasha ta yanke hukumcin daurin shekaru 22 a gidan kurkuku a kan wani dan kasar Belarus wanda hukumar tsaron cikin gida ta Rasha ta ce ya kai harin bam a kan wasu jiragen kasar biyu a yankin Siberiya, bisa umurnin hukumar leken asirin kasar Ukraine.

Ofishin gabatar da kararraki ta Rasha ta fada yau alhamis cewa an samu Sergei Yeremeyev da laifin ta’addanci ta hanyar dasa bama-bamai a wasu jiragen kasa na daukar kaya biyu a shekarar 2023.

Hukumar tsaron cikin gidan Rasha ta fada a lokacin da aka kama shi cewa ya amsa laifinsa.

Hukumar leken asirin Ukraine ta ce ita ce ta shirya kai hare-haren biyu a yankin Buryatia dake bakin iyaka da kasar Mongoliya, wanda kuma dubban kilomitoci daga bakin iyakar Ukraine, amma hukumar leken asirin ta Ukraine ta fada a lokacin cewa tana kokari ne ta gurgunta zirga zirgar jiragen kasa a Siberiya wanda ta yi ikirarin cewa Rasha na amfani da su wajen jigilar kayayyakin yaki.

Labarai

Post navigation

Previous Post: Kimanin Ganga Miliyan 40 Na Danyen Albarkatun Mai Yayi Kwantai A Kasashen Afirka Ta Yamma
Next Post: A Kowacce Rana Kasar China Tana Sayan Danyen Mai Ganga Dubu 600 Daga Kasar Venezuela

Karin Labarai Masu Alaka

Sabuwar Shekarar Musulunci: Shugaban Gwamnonin Arewa Ya Yi Kira Da A Yawaita Addu’o’i Da Haɗin Kai Afrika
Nigeria Zata Bude Asusun Dala Bilyan Biyu Don Habaka Sashin Makamashi Labarai
Dakarun Sojin Najeriya Sun Kashe Yan Kungiyar Lakurawa Afrika
Kasar Colombia Tare Da Amurka Zasu Fitar Da Man Venezuela Labarai
Dr. Kabiru Hassan Ya Kammala Wa’adinsa A GOGIS, Ya Yi Bitar Sauye-Sauyen Harkokin Filaye Afrika
Shugaban Amurka Yace Zasu Kakabawa Mashigar Hormuz Takunkumi Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Inuwa Ya Bukaci A Kara Zuba Jari A Ilimin Sana’o’i Domin Samar Wa Matasa Aikin Yi
  • Gwamnonin Arewa Sun Yi Jimamin Rasuwar Bamanga Tukur, Sun Yaba Da Gudunmawarsa Ga Najeriya
  • Tsohon Shugaban PDP, Bamanga Tukur, Ya Rasu Yana da Shekaru 91
  • Filato: Gwamnati Ta Ƙarfafa Matakan Kariya Yayin Sake Buɗe Makarantu
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gwamnan Jihar Kano Ya Fice Daga Jam’iyar NNPP Siyasa
  • Ankara Kai Wani Harin Bom Birnin Maiduguri Afrika
  • Babban Hafsan Tsaron Najeriya Ya Gargadi Jama’ar Arewa Maso Gabas Afrika
  • Jirgin Ruwan ‘Yan Gudun Hijira Ya Nitse Kogi A Tunisiya Labarai
  • Rwanda Zata Janye Dakaru Daga Mozambique Afrika
  • Rundunar Wanzar Da Zaman Lafiya Zata Tabbatar Da Tsagaita Wuta A Kwango Afrika
  • Shugaban Amurka Yace Sojojin Amurka Dana Iran Sunyi Taho Mugama Amurka
  • Ingila, Hauhawar Farashi Yayi ƙasa Sosai Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.