Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Masu Hakar Ma’adanai 37 Sun Mutu A Jihar Filato
Published: February 19, 2026 at 3:42 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: February 19, 2026

Rundunar ‘yan sandan jihar Filato tace ta tura jami’anta dake bangaren tantance bam, zuwa wurin hakar ma’adinai na kwal, a Kampanin Zurak dake karamar hukumar Wase, inda a kalla mutane talatin da bakwai suka rasa rayukansu, wassu ishirin da shida aka kai su asibiti, sanadiyyar shakar gubar gas a lokacin da suke aiki.

A wata sanarwa da ta aike wa manema labarai, rundunar ‘yan sandan a Jihar Filato tace binciken da ta fara gudanarwa ya nuna cewa guba dake cikin Ma’adanai lead oxide da sulfur da carbon monoxide ne suka hallaka masu hakar ma’adinan.

Sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sandan a jihar Filato, Alfred Alabo ya sanya wa hannu ta nuna da cewa babu alamar tashin bam a wurin, duk da haka dai jami’an sun sauki samfurin dutse da rairayi da ma’adinan dake wurin don ci gaba da bincike.

Shugaban matasan Wase, Shafi’u Sambo yace ya zuwa yanzu mutane talatin da takwas ne suka rasa ransu a wurin hakar ma’adinan na Kamfanin Zurak.

A halin da ake ciki kuma, gwamnatin jihar Filato ta jajanta wa iyalan wadanda suka rasun da kuma addu’ar sauki wa wadanda ke jinya a asibiti.

A sanarwa da komishinan yada labarai da sadarwa na jihar Filato, Madam Joyce Ramnap ta sanya wa hannu, gwamnatin tace zata karfafa dokar harkokin hakar ma’adinai don tsaron lafiyar al’umma.

Sanarwar tace gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang ya sha alwashin hadin gwiwa da hukumomin tarayya da sauran hukumomin dake kula da ayyukan hakar ma’adinai, kamfanoni da al’umman yankin da ake hakar ma’adinan don aiwatar da matakan kariya.

Ga Rahoton Zainab Babaji Daga Jos

https://gtahausa.com/wp-content/uploads/2026/02/GUBAR-GAS-YA-HALLAKA-MASU-HAKAR-MAADINAI-A-FILATO.mp3
Bidiyo, Labarai

Post navigation

Previous Post: Mutane Biyu Sun Mutu A Yayin Zaben Shugabannin Gundumomin APC A Jihar Ondo
Next Post: Shugaba Tinubu Ya Gana Da Takwaransa Na Kasar Jamus Akan Sha’anin Tsaro

Karin Labarai Masu Alaka

Shugaba Saied Yana Cigaba Da Samun Goyon Bayan Al’ummar Kasar Tunisiya Afrika
Kasashen Thailand Da Cambodia Sun Amince Da Tsagaita Wuta Labarai
Tinubu Zai Gabatar Da Jawabi ga Shugabannin Duniya A Taron UNGA Afrika
Kawayen Amurka Bazasu Shiga Matakin Shugaba Trump Ba Amurka
Prime Ministan Senegal Ya Bayyana Shirin Sauya Sheka Afrika
GOSEMA Ta Horar Da Mambobin LEMCs A Jihar Gombe Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Nasarawa United Ta Kai Wasan Kusa da Ƙarshe Na Gasar Gusau/Ahlan 2026 Wasanni
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa Afrika
  • Ana Cigaba Da Kai Kayan Agaji Kasar Morocco Sakamakon Tsananin Hunturu Afrika
  • Zaben Fidda Gwani Ya Gudana Lafiya A Jihar Gombe Afrika
  • ‘Yan Sanda Sunce Mutum Daya Ne Yakai Hare-Haren Jami’ar Brown Da Kuma Na MIT Boston Amurka
  • Zabebben Shugaban Hungary Yace Zaidawo Da Tsarin Dimokraɗiyya Afrika
  • Shugaba Trump Ya Kara Matsin Lamba Kan Iran Amurka
  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.