Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Anfara Kirga Kuri’a A zaben Kasar Guinea
Published: December 29, 2025 at 10:02 AM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: December 29, 2025

An fara kidaya kuri’u a kasar Guinea-Conakry, bayan zaben shugaban kasa da aka gudanar ranar lahadi, zaben da ake kyautata zaton shugaban gwamnatin mulkin soja, Mamady Doumbouya, wanda ya kwace mulki a shekarar 2021, shine zai lashe cikin sauki.

Tsohon kwamandan rundunar zaratan sojojin na Guinea, ya fuskanci ‘yan takara 8 a wannan zaben na jiya, wanda in ya lashe, zai ba shi wa’adin shekaru 7 a kan karagar mulki, tare da kawo karshen shirin maido da mulkin farar hula.

Hambararren shugaban Guinea-Conakry, Alpha Conde, da dadadden madugun hamayya Cellou Dalein Diallo, har yanzu su na zaman gudun hijira a waje.

Babu wani tashin hankali da aka samu a lokacin zaben, inda a babban birnin kasar watau Conakry, wadanda suka fito ba su da yawa.  Amma akasarin jama’a sun ce an riga da an san yadda zaben zai kaya, don haka ba sai sun bata lokaci wajen zuwa jefa kuri’a ba.

Doumbouya, wanda ya sanya babbar riga fara tare da matarsa, ya jefa kuri’arsa a wata mazabar dake wani asibiti a Conakry.

Ana sa ran samun sakamakon farko na zaben nan da kwana biyu ko uku.

Labarai

Post navigation

Previous Post: Shugaba Bola Tinubu Ya Tafi Turai
Next Post: Isra’ila Zata Karbi Mutanenta A Yankin Gaza

Karin Labarai Masu Alaka

CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
Gwamnatin Najeriya Na Shirin Yin Zamiya Don Biyan Bashi Labarai
Fadar Shugaban Kasa Ta Karyata Jita-Jitar Yunkurin Sanya Wa Tinubu Guba A Abinci Afrika
An Kafa Majalisar Kotun Sulhu Ta Kano Labarai
Yaki Ta Sararin Samaniya Ya Cigaba Tsakanin Amurka, Isra’ila Da Iran Afrika
An Gano Wani Kurkukun Sirri Da Ake Azaftar Da Mutane A Kasar Libya Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • NEDC Ta Fara Shirin Kera Sanitary Pads A Gombe Domin Samar Da Sana’o’i Afrika
  • Zaman Lafiya Yafara Dawowa A Sudan Afrika
  • Gwamnatin Tarayya Tayi Baje Kolin Nasarorin Tinubu Afrika
  • NFF Ta Nada Eguavoen Kocin Rikon Kwarya Na Super Falcons Wasanni
  • Shugaban Kasar Najeriya Ya Nada Sabon Ministan Kudi Labarai
  • ‘Yan Kasashen Afirka Da Dama Suna Fafatawa Da Rasha A Yaki Da Ukraine Afrika
  • Ambaliyar Ruwa Ya Tilastawa Dubban Jama’a Rasa Muhallensu A Morocco Afrika
  • Fargaba Ta Karu Duk Da Tsagaita Wuta Tsakanin Iran Da Amurka Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.