Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

‘Yan-Ta’adda Sun Yi Ma Wasu Mutane Yankan Rago A Jihar Neja
Published: January 5, 2026 at 3:24 PM | By: Yusuf Aliyu Harande

Akalla Mutane 37 ne aka kashe ta hanyar yi masu yankan rago a Jihar Nejan Najeriya.

Rahotanni daga kauyen kasuwar Daji dake yankin karamar Hukumar Borgu na nuna cewa wasu mahara da ake zaton mayakan lakurawa ne ko kuma Boko Haram bayan kashe wadan nan mutane sun kuma yi garkuwa da wasu mutanen da dama.

Wasu daga cikin mazauna yankin sunce maharan sun share yinin ranar Asabar suna ta’asubancinsu a yankin tare da kona kasuwar Garin.

Shugaban karamar hukumar ta Borgu Hon. Muhammad Nasir Abdullahi ya tabbatar da aukuwar lamarin inda yace suna cikin yanayi na tashin hankali.

Gwamnatin jihar Nejan tace tana cikin yanayi na tashin hankali amma kuma Gwamnati na daukar mataki na shawo kan wannan matsala a ta bakin Hon. Obed Nana Kwamishina yada Labarai na Jihar Nejan, ya kara da cewa sun hada hannu da Gwamnatin Tarayya domin tun karar matsalar kai tsaye.

Yankin na kasuwar Daji dai yana kusa da Garin Papiri inda aka saci yaran makarantar St Mary a cikin watan Nuwamban da ta gabata.

Labarai

Post navigation

Previous Post: Manchester United Ta Sallami Ruben Amorim
Next Post: Hukumar Zabe A Najeriya Ta Cigaba Da Rijistar Katin Zabe

Karin Labarai Masu Alaka

Za’a Fuskanci Bala’in Yunwa A Najeriya Labarai
Tsohon Jagoran Masu Kishin Kasa A Hungry Ya Amince Da Shan Kaye Labarai
Shugaban Ƙasar Koriya Ta Arewa Ya Halarci Gwajin Makami Mai Linzamin Kasar Labarai
Shugaba Trump Ya Bukaci Kasar Iran Ta Mika Wuya Amurka
China Ta Dawo Da Harajin Magungunan Hana Haihuwa Labarai
Akwai Doka Mai Tsanani Wajen Mallakar Bindiga A Kasashen Yammacin Turai Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • “Banga Abun Da Zai Canza Ba A Nadin Janar Christopher Ministan Tsaro” Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Hukumar Kula Da Makamashin Nukiliya Ta Duniya Zata Binciki Kasar Iran Afrika
  • Gwamnan Jihar Gombe Ya Ƙarfafa Wa Sabbin Masu Ashaka Cement Gwiwar Samar Da Ayyukan Yi Afrika
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji A Jihar Kebbi Afrika
  • Kamfanin Hakar Ma’adanai Na Kasar Kanada Ya Cigaban Da Aikinsa Labarai
  • Shugaba Tinubu Yace Bazai Bawa ‘Yan Najeriya Kunya Ba Afrika
  • Rasha Takai Hari Ukraine Da Jirgi Marar Matuki Afrika
  • UPF Ta Bukaci Haɗin Gwiwa Da NERDC Domin Gina Al’umma Mai Zaman Lafiya Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.