Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya Afrika
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel Afrika
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki Afrika
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe Afrika
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba Afrika

Rasha Takai Hari Ukraine Da Jirgi Marar Matuki
Published: April 5, 2026 at 9:27 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Mutane biyar sun halaka a Ukraine wasu 19 kuma suka ji rauni sakamakon wani harin da Rasha ta kai da jirgin da bashi da matuki akan wata kasuwa a wani gari dake daf da fagen yakin kasar da Rasha da ake kira Nikopol a ranar Asabar, kamar yadda wata sanarwa daga ofishin babban lauyan gwamnatin kasar tayi bayani.

Garin Nikopol, mai tazarar ‘yan kilomitoci daga yankin kasar da Rasha ta mamaye dake kan gabar kogin da ake kira Dnipro, ya dade yana fuskantar hare hare daga Rasha.

“Wannan harin wani kari ne kan laifuffukan yaki da Rasha ta ke aikatawa,” inji sanarwar da ofishin babban lauyan gwamnatin kasar ya fitar.

Ahalinda ake ciki kuma, wani hadimin shugaba Volodimyr Zelensky na Ukraine, yace akwai yiwuwar jakadun Amurka na musamman Steve Whitkoff, da Jared Kushner, za su ziyarci Kyiv cikin watan nan, a wani yunkuri na sake farfado da shawarwarin sulhu da Rasha, wanda ya tsaya, sakamakon barkewar yakin hadin guiwar Amurka da Isra’ila suka kaddamar kan Iran.

Afrika, Labarai, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Isra’ila Zata Kai Hari Cibiyar Makamashin Iran
Next Post: Jami’an Tsaro Suna Farautar Wasu ‘Yan Ta’adda A Najeriya

Karin Labarai Masu Alaka

Kasar Zimbabwe Ta Samar Da Dokar Tsawaita Mulkin Mnangagwa Zuwa 2030 Labarai
Kasuwannin Hannun Jari Sun Farfado Afrika
Kwararru Sun Tabbatar Da Lafiyar Kangimi Dam Bayan Binciken Tsaro Afrika
Hukumomin Tsaron Kenya Sunce ‘Yan Kasar Suna Fafata Yaki Da Dakarun Rasha A Ukraine Afrika
Amurka Zata Fice Daga Iran Cikin Gaggawa Afrika
Rundunar Wanzar Da Zaman Lafiya Zata Tabbatar Da Tsagaita Wuta A Kwango Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gwamnatin Gombe Ta Kaddamar Da Sabon Ofishin GOGIS Don Inganta Tsarin Filaye Afrika
  • Afirka Ta Kudu Tace Bazata Yanke Alaka Da Iran Ba Afrika
  • Sheikh Ibrahim Sheikh Dahiru Ya Zamo Khalifan Sheikh Dahiru Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mataimakin Shugaban Kasar Amurka Ya Gana Da Wasu Wakilai Amurka
  • Shugaban Kasar Ukraine Yace Rasha Tana Bawa Iran Bayanan Sirri Afrika
  • Kasashen Amurka,Israela Da Iran Sun Amince Da Dakatar Da Yaki Afrika
  • Hari Akan Wata Mashaya Ya Rutsa Da Mutane 9 A Afirka Ta Kudu Afrika
  • Tinubu Ya Kafa Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.