Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama Afrika
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara Afrika
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe Afrika
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro Afrika
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa Afrika

Peter Obi Ya Gayyaci Gwamnan Bauchi Bala Abdulkadir Kan Yazo Su Hada Kai Su Gyara Nijeriya.
Published: April 23, 2026 at 6:18 PM | By: Bala Hassan

Peter Obi, da Gwamnan Bauchi zasu hada kai don nemo hanyoyin da za’a warware matsalolin Nijeriya kafin zaben 2027
Daga Ahmad Muhammad,Bauchi

Tsohon Gwamnan Jihar Anambra Kuma tsohon dan Takarar Shugaban ƙasa a Jam’iyyar Labour Party Chief Peter Obi ya gayyaci Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Abdulqadir Mohammed Kan yazo su hada kai suyi aikin. Gyara Nijeriya.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai Obi yace Wajibine a garemu mu ceto Nijeriya saboda yanayin halin da ake ciki Bai dace da rayuwarmu da rayuwar ‘ya’yanmu da jikokinmu ba.

“Na zo ne domin neman goyon bayan Gwamna Bala Mohammed da daukacin yankin Arewa maso Gabas yayin da muke kokarin tabbatar da hadin kan kasa. A halin yanzu, kasar nan tana kan hanya mara kyau, kuma yana da muhimmanci mu dauki matakai na gaggawa domin gyara alqiblar da muke kai.”

 

Obi ya ce ziyarar tana da nufin havaka haɗin kai da ƙarfafa haɗin gwiwa a faɗin ƙasar.

“Manufata ita ce neman goyon baya da haɗin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki, musamman daga jihar Bauchi da arewa maso Gabas,a cikin ƙoƙarinmu na haɗa kan wannan ƙasar,”

Ya yi watsi da jita-jitar da ake yi game da sauya sheƙa a siyasance, yana mai dagewa cewa batun da sukeyi ba wai game da haɗakar jam’iyya ba ne. “Ba ma gayyatar junanmu zuwa jam’iyyun siyasa ba; Muna gayyatar kanmu NE don mu gina ingantacciyar Najeriya,”

Yace abin damuwa ne ace Yau manomi ba Zai Iya zuwa Gona lafiya ba, xalibai basa Iya zuwa makaranta suyi karatu, baza ka Iya tafiya daga wannan gari zuwa wancan Garin ba Sai a Kamaka ace Sai ka Biya Kuxin fansa.
Ga Tarin matsalolin tsaro matsalolin tattalin arziki da sukayi tarnaqi wa rayuwar al’umma Wanda ya zamo dole muhaxa kai da sauran ‘yan Nijeriya don aceto qasarnan yadda za’a Samu ci gaba da kuma Zaman lafiya sannan a samu makoma Mai kyau da Zai yaqi yunwa, Talauci, rashin tsaro, rashin ingancin tattalin arziki da sauransu dole ne mu tsaya mu warware waxannan matsaloli da sukayi mana tarnaqi.

Da yake maida Jawabi ,Gwamnan Bauchi Sanata Bala Abdulqadir Mohammed ya godewa Peter Obi saboda wannan ziyarar yace Wajibine SU haxa kansu a siyasance don a Samu mafita Mai xorewa wa qasarnan.
Gwamna Bala yace su da suke vangaren adawa Wajibine SU nemi inuwar da zasu haxa kai su tafi tare domin ceto qasarnan.

 

Gwamna Bala ya ce yanzu shi “dan siyasa ne mai zaman kansa” ba tare da wata alaqa ta kai tsaye da kowace jam’iyya ba.

Gwamnan ya ce taron ya mayar da hankali kan haxin kan qasa da haxin gwiwa, yana mai cewa tattaunawar ba ta dogara ne da muradun jam’iyya ba. “PDP ko ADC ba sa tsayawa ni kaxai.
Ni xan siyasa ne mai zaman kansa yanzu, kuma jam’iyyarsa ma tana cikin ruxani. Muna duba vangaren shari’a. “Tabbas, dukkanmu muna cikin jam’iyyar adawa, kuma shi ya sa na ce wannan tattaunawa ce ta siyasa. Ba za mu bayyana duk abin da muka tattauna da yadda zamuyi ba.

Ya qara da cewa ci gaba da tattaunawa tsakanin masu ruwa da tsaki na siyasa ya mayar da hankali ne kan yiwuwar sake haxewa da haxin gwiwa kafin zave mai zuwa. “Ba za mu iya aiki ba tare da wani dandamali ba.” A ƙarshe, yanayin siyasa na yanzu na iya taimakawa wajen haɗa kanmu da kuma ƙarfafa damarmu ta cin zaɓe,” in ji shi.

Gwamnan ya bayyana ziyarar Obi a matsayin alama, na qarfafa guiwa,kuma yazo da tocila mai haskaka mana hanya.

” Saboda Yana magana ne game da haɗa kan ƙasar, , da kuma ƙirƙirar rayuwa Mai kyau ga Najeriya. Wannan shine abin da muke tsayawa a kai a matsayinmu na jiha da kuma a matsayinmu na mutane.
Muna jin daɗin wannan ziyarar sosai,” in ji Gwamnan.

 

in ji shi. Taron ya samu halartar masu ruwa da tsaki da dama a Kudu maso Gabas, ciki har da tsohon gwamnan jihar Imo, Achike Udenwa, da Sanata Enyinnaya Abaribe da Victor Umeh.

Wannan ziyarar yazo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da shawarwari kan siyasa da Neman mafita kan makomar siyasan Gwamnan da magoya bayansa, tun bayan lokacin da Shugaban Jamiyyar PDP yace sun dakatar da tattaunawa da Jamiyyar APC, Kuma Abaya a cikin ‘yan watannin nan ya karvi baquncin masu ruwa da tsaki a dukkan fannoni na jam’iyya, ciki har da wakilin Shugaban Jamiyyar ADC DA Shugaban Jamiyyar APC , Jam’iyyun PRP DA NDC Suna ci gaba da yayin da ake qoqarin inda zaa Sami daidaito kafin zaven 2027.

Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Post navigation

Previous Post: Shugaba Tinubu Zai Kara Karbo Bashin Dala Miliyan 516
Next Post: Gwamnatin Tarayya Tayi Baje Kolin Nasarorin Tinubu

Karin Labarai Masu Alaka

Zulum Ya Tallafa Wa Mambobin NYSC Da Naira Miliyan 8.2 A Borno Afrika
Farashin Danyen Mai Ya Fadi A Kasuwar Duniya Afrika
Anfara Gangamin Kafa Dokoki Masu Tsanani Ga ‘Yan Luwadi A Senegal Afrika
Shugaba Tinubu Ya Gana Da Takwaransa Na Kasar Jamus Akan Sha’anin Tsaro Labarai
An Bukaci Matasa Su Taka Gagarumar Rawa Wajen Gina Zaman Lafiya A Arewa Maso Gabas Afrika
Tinubu: Mun Ware Biliyan 42 Don Inganta Lafiyar ‘Yan-Kasa Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • An Kama Wani Da Abubuwan Fashewa A Zamfara Najeriya
  • Shugaban Amurka Ya Sauke Antoni Janar Amurka
  • Gwamna Zulum: Ya Bukaci Sojoji Su Cigaba Da Yakar Boko Haram Da ISWAP Labarai
  • “Banga Abun Da Zai Canza Ba A Nadin Janar Christopher Ministan Tsaro” Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Jami’an Tsaro A Jihar Borno Sun Kama ‘Yan Bindiga Labarai
  • Shugaba Tinubu Ya Rantsar Da Christ Musa Ministan Tsaro Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Shugaban Amurka Donald Trump Ya Jadda da Kudirinsa Da Kwace Iyakar Greenland Amurka
  • Barayin Waya Sun Yanke Yatsun Hannu Guda Biyu Da Gefen Kunne A Bauchi Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.