Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Farashin Danyen Mai Ya Fadi A Kasuwar Duniya
Published: February 17, 2026 at 10:04 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Farashin danyen mai ya fadi da kusan kashi daya a ranar talata, bayan da ministan harkokin wajen Iran yace Amurka da Farisan sun amince akan sharuddan da za su mutunta a tattaunawar da suke yi kan shirin Nukuliyar kasar, mataki da ya rage fargabar da ‘yan kasuwa suke yi game da karuwar zaman dar dar.

Mai da ake kira Brent yayi kasa da kusan dala daya, ya tsaya kan dala 67. da centi 71 akan ko wace ganga, bayan da ya tashi da kamar kashi 1.33 a ranar litinin.

Yayinda mai da ake kira West Texas ana sayen ko wace gangar mai akan dala 62 da centi 79 ya fadi da kamar centi 10, wannan farashi ya shafi dukkanin hada hadar da akayi ranar Litinin, wadda ba’a cimma daidaito akanta ba, saboda ranar hutu ne a Amurka.

Galibin manyan kasuwannnin sayen hannayen jari a Asiya suna hutu ranar talata na sabuwar shekarar su da suka hada da China, da Hong Kong, da Taiwan, da Korea ta kudu da Singapore.

Ministan harkokin wajen na Iran Abbas Araqchi ya fadawa wata kafar yada labaran kasar cewa, ci gaba da aka samu a wajen tattaunawar ba yana nufin za’a sami saukin kulla yarjejeniya ba, sai dai hakan yana nuni da cewa an kama hanyar samun ci gaba ne a shawarwarin.

Farashin mai zai ci gaba da kasancewa cikin rashin tabbas saboda batutuwa na Diflomasiyyar ne suke tasiri, maimakon bukata, inji Sugandha Sachdeva, mai kamfanin SS a New Delhi.

Afrika, Amurka, Labarai

Post navigation

Previous Post: An Ga Watan Ramadan A Najeriya Da Nijar
Next Post: Kamfanin Dangote Zai Sayo Na’urori Daga Kasar China

Karin Labarai Masu Alaka

Kawayen Amurka Bazasu Shiga Matakin Shugaba Trump Ba Amurka
Farashin Mai Ya Doshi Dala 100 Kowacce Ganga Afrika
Gwamnatin Tarayya Ta Cire Sharadin Rubuta UTME Ga Masu Neman Shiga Kwalejojin Ilimi Afrika
An Samu Bullar Cutar COVID 19 A Najeriya Afrika
NAHCON Ta Kaddamar da Tawagar Malamai Afrika
Kasar Chadi Ta Rufe Iyakar Ta Da Kasar Sudan Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Amurka Zata Bawa Sojojin Najeriya Horo Labarai
  • Anyi Bikin Cikar Tsohon Shugaban Kasa Abdulsalami Shekaru 84 Afrika
  • Harin Jirgi Maras Matuki Ya Hallaka Mutane A Sudan Labarai
  • Wasu Yara 50 Sun Kubuta Daga Hannun ‘Yan-Ta’adda Labarai
  • Mutane Biyu Sun Rasa Rayukansu A Hatsarin Da Ya Rutsa Da Antothy Joshua Najeriya
  • Sojoji Sun Dakile Harin ’Yan Ta’adda a Kukareta Afrika
  • Lawal, Filin Wasa Na Rashidi Yekini Ko Turai Iyaka Wasanni
  • Sojojin Amurka Sun Kashe Wasu Fararen Hula Ba Dalili Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.