Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

APC Ta Ayana Tsohon Gwamnan Bauchi M.A Abubakar A Matsayin Dan Takarar Gwamna
Published: May 23, 2026 at 10:52 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Jam’iyyar APC a jihar Bauchi ta bayyana tsohon gwamnan jihar, Mohammed Abdullahi Abubakar, a matsayin ɗan takararta na gwamna a zaɓen shekarar 2027, bayan nasarar da ya samu a zaɓen fidda gwani da jam’iyyar ta gudanar.

An sanar da sakamakon zaɓen ne da sanyin safiyar Asabar daga bakin shugaban kwamitin gudanar da zaɓen fidda gwani na APC a Bauchi, tsohon mataimakin sufeton ‘yan sanda, John Bassey Abang, wanda ya ce an gudanar da zaɓen a ranar Juma’a 22 ga watan Mayun 2026 a faɗin jihar.

A cewarsa, M.A Abubakar SAN ya samu kuri’u dubu 57,517 inda ya doke sauran ‘yan takara shida da suka fafata a zaɓen. Tsohon Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar, ya zo na biyu da kuri’u dubu 26,001, yayin da Nura Manu Soro ya samu kuri’u dubu 13,638.

Sauran waɗanda suka shiga takarar sun haɗa da Bala Maijama’a Wunti wanda ya samu kuri’u 13,648, Kabiru Baba Ma’aji mai kuri’u 8,157, Baba Abubakar Suleiman da ya samu kuri’u 7,688, sai Yakubu Yakubu Abdullahi da ya samu kuri’u 7,181.

Da yake bayyana sakamakon, shugaban kwamitin ya ce M.A Abubakar ya cika dukkan sharuɗɗan da ake buƙata, kuma ya samu mafi yawan ƙuri’un da aka kaɗa, saboda haka aka ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen fidda gwani na APC a Bauchi.

Mohammed Abdullahi Abubakar ya taba zama gwamnan Jihar Bauchi tsakanin shekarun 2015 zuwa 2019 a ƙarƙashin jam’iyyar APC, kafin ya sha kaye a hannun gwamna mai ci yanzu, Bala Mohammed, na jam’iyyar PDP a zaɓen shekarar 2019.

Nasarar da tsohon gwamnan ya samu na nuni da cewa APC ta fara ɗaukar matakan tunkarar babban zaɓen 2027 a jihar Bauchi, yayin da ake sa ran za a fafata sosai tsakanin manyan jam’iyyun siyasa a jihar.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Masana Lafiya – Preeclampsia Cuta Ce Mai Hadari Amma Ana Iya Magance Ta
Next Post: Bola Ahmed Tinubu Ya Lashe Zaben Fidda Gwani Na Shugaban Kasa A Gombe

Karin Labarai Masu Alaka

Najeriya Ta Bawa Dan Takarar Guinea-Bissau Mafaka Afrika
Ministan Yaɗa Labarai Ya Yi Kira Ga Haɗin Kai Domin Bunƙasa Maɗaba’u Afrika
Isra’ila Zata Rusa Gidajen Da Suke Iyakarta Da Lebanon Labarai
Sojoji Sunkai Farmaki Gidan Dan Adawa A Kasar Uganda Bobi Wine Afrika
Kasar Congo Ta Dau Alwashin Bin Tsari Wajen Rarraba Ma’adanai Afrika
Amurka Tace Zata Gama Yakin Iran Cikin Makonni Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Trump Yace Amurka Ta Kai Hare-Hare Masu Yawa Akan ‘Yan Ta’adda A Najeriya Amurka
  • Dangantaka Tayi Tsamari Tsakanin Salah Da Slot. Wasanni
  • Muhimmin Sako Ga Alhazai Dake Kasar Saudiya Afrika
  • Ukraine Takai Hari Wajen Kera Makami Mai Linzami A Rasha Labarai
  • Shugaban Amurka Ya Ya Bukaci Iran Ta Mika Wuya Afrika
  • Ana Zargin Tsohon Shugaban Kasar Philippines Da Ta’addaci A Lokacin Mulkinsa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Sojojin Amurka Sun Isa Najeriya Don Yaki Da Ta’addanci Amurka
  • Kasashen Yankin Gulf Sun Bada Sanarwa Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.