Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Bola Ahmed Tinubu Ya Lashe Zaben Fidda Gwani Na Shugaban Kasa A Gombe
Published: May 23, 2026 at 3:53 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaban Kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya lashe zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress da aka gudanar a Jihar Gombe State.

Da yake sanar da sakamakon zaben, jami’in tattara kuri’u na zaben fidda gwani na shugaban kasa na APC a jihar, Gwamna Inuwa Yahaya, ya ce Shugaba Tinubu ya samu kuri’u 450,517, yayin da abokin takararsa Sterling Osifor bai samu ko kuri’a daya ba.

Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana cewa an gudanar da zaben cikin lumana a dukkan rumfunan zabe da kananan hukumomi goma sha daya na jihar.

Ya ce an bai wa dukkan mambobin jam’iyyar damar kada kuri’unsu ba tare da wata matsala ba, tare da jaddada cewa an gudanar da sauran zabukan fidda gwani na mukaman siyasa cikin nasara.

A nasa martanin, Shugaban APC na jihar Gombe, Mohammed Dantata Ndus, ya yabawa Gwamna Inuwa Yahaya bisa jagoranci da yadda ya tafiyar da harkokin jam’iyyar a jihar.

Ndus ya kuma bayyana kwarin gwiwarsa cewa ‘yan takarar APC a jihar za su samu nasara a zabukan gama gari masu zuwa.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: APC Ta Ayana Tsohon Gwamnan Bauchi M.A Abubakar A Matsayin Dan Takarar Gwamna
Next Post: An Kamallah Jigilar Alhazain Najeriya Domin Hajjin 2026

Karin Labarai Masu Alaka

Kungiyar Kwallon Mata Sun Tsallaka Iyakar Turkiyya Zuwa Iran Afrika
Tinubu Zai Gabatar Da Jawabi ga Shugabannin Duniya A Taron UNGA Afrika
Sabunta Manhajar Ilimi A Duk Matakai Nasara Ce! Najeriya
An Kashe Sojojin Ukraine Dubu 55 A Kasar Rasha Afrika
Shugaba Tinubu Yace Bazai Bawa ‘Yan Najeriya Kunya Ba Afrika
Dottin Shara Ya Damu Jama’ar Havana Kasar Cuba Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gwamna Abba Kabir Ya Hana Yunkurin Kafa Sabuwar Hisba A Kano Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Najeriya Ta Tura Mutane 386 Gidan Yari Afrika
  • Wasu Mayakan ‘Yan Tawaye Sunkai Hari Filin Jirgin Saman Kasar Kwango Labarai
  • Shugaban Amurka Ya Sauke Antoni Janar Amurka
  • Shugaban Kasar Tunisiya Ya Tsawaita Dokar Da Baci A Kasar Labarai
  • EU Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Amurka Da Iran Afrika
  • EFCC Ta Cafke Fitacciyar Jarumar Kannywood Samha Inuwa Labarai
  • Wani Ya Yiwa ‘Yar Sa Mai Shekaru 8 Fyade A Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.