Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

An Kamallah Jigilar Alhazain Najeriya Domin Hajjin 2026
Published: May 23, 2026 at 5:09 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

An samu wani babban gagarumin nasara a harkokin aikin Hajjin shekarar 2026 yayin da Hukumar Alhazain Najeriya (NAHCON) ta kammala jigilar alhazan Najeriya zuwa Ƙasar Saudiyya cikin nasara, inda aka yi jigilar alhazai sama da 40,000 cikin kwanaki 18 kacal.

Wannan nasara ta sake tabbatar da irin kulawa da muhimmancin da Gwamnatin Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ke bai wa harkokin addini da jin daɗin al’ummar Najeriya, musamman Musulmai masu gudanar da ibadar Hajji.

A cewar Hukumar NAHCON, an gudanar da jimillar jirage 98 daga ranar 3 ga watan Mayu zuwa ranar 21 ga watan Mayu, inda aka yi jigilar alhazai 40,250 da suka samu bizar Hajji ta hannun hukumar. Wannan ya nuna irin ingantaccen shiri da tsare-tsaren da aka yi tun kafin fara aikin.

Shugaban Hukumar NAHCON, Ambassador Ismail Abba Yusuf, ya bayyana cewa nasarar da aka samu ba za ta rasa nasaba da cikakken goyon baya da jagorancin Shugaba Tinubu da kuma sa ido na kusa da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, waɗanda suka tabbatar da samar da yanayin da ya ba da damar gudanar da aikin cikin sauƙi duk da ƙalubalen da ake fuskanta a duniya.

Haka kuma, kwamitin haɗin gwiwa na Majalisar Dokoki ta Ƙasa da ya ƙunshi sanatoci da mambobin Majalisar Wakilai ya yaba da yadda aka gudanar da aikin Hajjin bana, inda ya bayyana cewa an samu gagarumin ci gaba a fannin daidaitawa, haɗin kai tsakanin masu ruwa da tsaki da kuma ingancin ayyukan da aka samar wa alhazai idan aka kwatanta da shekarun baya.

Yayin wata ziyarar sa ido da suka kai birnin Madina domin duba masaukan alhazai da tantance ayyukan da ake gudanarwa, shugaban tawagar, Sanata Ali Ndume, ya ce aikin Hajjin 2026 ya nuna kyakkyawan tsari, ingantaccen shugabanci da kuma ƙwarewar gudanarwa daga NAHCON da sauran hukumomin da ke da alhakin aikin.

Ya ƙara da cewa nasarar kammala jigilar alhazai kafin rufe sararin samaniyar Saudiyya wata shaida ce ta ingantaccen shiri da kuma kyakkyawar jagoranci wajen tabbatar da nasarar manyan ayyukan ƙasa.

Har ila yau, gwamnatin ta tabbatar da cewa an kammala shirye-shiryen gudanar da ayyukan Masha’ir a Mina, Arafat da Muzdalifah domin tabbatar da jin daɗi, tsaro da walwalar alhazan Najeriya yayin gudanar da manyan rukunnan Hajji.

Wannan ci gaba ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin Tinubu ke ƙara mayar da hankali wajen inganta ayyukan sufuri, gudanarwa da hidimomin jama’a, lamarin da ke haifar da sakamako mai kyau a fannoni daban-daban na rayuwar al’umma.

Bugu da ƙari, NAHCON ta sanar da cewa shirye-shiryen dawo da alhazai gida bayan kammala aikin Hajji sun riga sun fara, inda ake sa ran fara jigilar dawowa Najeriya daga ranar 3 ga watan Yuni.

Yayin da miliyoyin Musulmai daga sassa daban-daban na duniya ke gudanar da wannan babban rukuni na Musulunci, Najeriya ta sake nuna cewa tana da ƙwarewa da tsari wajen kula da alhazanta, abin da ke ƙara ɗaga martabar ƙasar a idon duniya.

Ana sa ran wannan nasara za ta zama tubalin da za a gina sabbin nasarori a kai, musamman yayin da NAHCON ta sanar da cewa shirye-shiryen Hajjin shekarar 2027 za su fara nan take bayan kammala aikin Hajjin bana.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Nishadi, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Bola Ahmed Tinubu Ya Lashe Zaben Fidda Gwani Na Shugaban Kasa A Gombe
Next Post: Za’a Fassara Hudubar Arfa Da Harshen Hausa

Karin Labarai Masu Alaka

Shugabannin Kasashen Afirka Ta Tsakiya Sun Kamallah Taron Koli Afrika
Ministan Harkokin Wajen Iran Yagana Da Shugaban Sa’ido Akan Nukiliya Afrika
Wata Tankar Mai Ta Kife A Apapa Legas Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Koriya Ta Arewa Ya Goyi Bayan Iran Wajen Zaben Sabon Jagora Mojtaba Khameni Afrika
Prime Ministan Pakistan Yace Zai Karbi Bakoncin Tattaunawar Amurka Da Iran Afrika
Sojin Najeriya Da Amurka Sun Hallaka Jagoran ISIS Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Tinubu Ya Lashe Zaɓen Fidda Gwanin APC Da Kuri’u Miliyan 11 Afrika
  • Tabbas Atiku Abubakar Ya Karbi Katin Jam’iyyar ADC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Wikki Tourist FC: Ta Sallami ‘Yan Wasa Hudu Wasanni
  • Gwamnatin Somaliya Da MDD Sun Bayyana Cewa Kimanin Mutane Miliyan Shida Da Rabi Suna Fuskantar Barazanar Yunwa Labarai
  • Masarautar Borgu a Jihar Neja na neman daukin Gwamnatin Najeriya akan matsalar rashin tsaro Najeriya
  • Afirka Ta Kudu Ta Kama ‘Yan ƙasar Kenya Su Bakwai Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Shugabar Hamayya A Venezuela Ta Gana Da Paparoma Leo Amurka
  • Kamfanin Magani Na Aspen Yayi Gagarumar Asara A Cinikayya Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.