Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Shugaba Tinubu Ya Tafi Kasar Faransa
Published: May 2, 2026 at 4:36 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai tashi daga Abuja a ranar Asabar, 2 ga Mayu, 2026, domin gudanar da ziyarar diflomasiyya zuwa ƙasashe uku wato France, Kenya da Rwanda, a wani yunƙuri na ƙarfafa hulɗar Najeriya da ƙasashen duniya da kuma bunƙasa gyaran tattalin arziki.

A cewar wata sanarwa da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Juma’a, jadawalin tafiyar shugaban zai fara ne da ziyara zuwa France kafin daga bisani ya wuce Nairobi a ƙasar Kenya, inda zai halarci taron Africa-France Summit da zai fara a mako mai zuwa.

Ana sa ran taron, wanda Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Shugaban Kenya William Ruto za su jagoranta tare, zai mayar da hankali kan muhimman batutuwa na duniya da nahiyar Afirka, ciki har da sauyin makamashi, bunƙasa masana’antu masu kare muhalli, sauyin fasahar zamani, matakan yaƙi da sauyin yanayi, da sake fasalin tsarin kuɗaɗen duniya.

Bayo Onanuga ya ce halartar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a taron da za a yi daga 11 zuwa 12 ga Mayu, zai nuna cikakken ƙudirin Najeriya na ƙarfafa alaƙar dabaru da ƙasashen Afirka da kuma Jamhuriyar Faransa.

Taken taron shi ne, “Africa Forward: Africa-France Partnerships for Innovation and Growth,” kuma zai zama babban dandali da shugabannin Afirka da na Faransa za su tattauna kan muhimman batutuwa kamar sauya tattalin arziki, jurewa matsalolin sauyin yanayi, bunƙasa ababen more rayuwa, ƙarfafa matasa, ci gaban fasaha, da kuma gina zaman lafiya.

Sanarwar ta ce, “A wajen taron, Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai gabatar da jawabi da zai bayyana gyare-gyaren da gwamnatin sa ke yi domin mayar da Najeriya wuri mafi dacewa ga zuba jari da ci gaba.”

Afrika, Labarai, Najeriya

Post navigation

Previous Post: Gwamna Bala Kauran Bauchi Ya Koma Jam’iyar APM
Next Post: An Gudanar Da Tiyatar Ido Kyauta A Gombe

Karin Labarai Masu Alaka

Kano: Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Amince da Garo A Matsayin Mataimakinsa Na 2027 Afrika
Farashin Kasuwar Yawon Bude Ido A Kasuwar Hannayen Jari Ya Fadi Afrika
Zelensky Na Buƙatar Ganawa Da Trump Domin Cimma Matsaya Kan Batutuwa Masu Sarƙaƙiya Labarai
Rashin Hanya da Asibiti Ya Jawo Asarar Rayuka A Jihar Gombe – Sarkin Gargajiya Afrika
Mutane 13 Sun Mutu Inda Wasu 57 Suka Jikkata A Barundi Afrika
Wasu Yara 50 Sun Kubuta Daga Hannun ‘Yan-Ta’adda Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Jirgin Sama Mai Saukar Ungulu Ya Kashe Mutane Biyar A Tanzaniya Afrika
  • ‘Yan-Ta’adda Sun Yi Ma Wasu Mutane Yankan Rago A Jihar Neja Labarai
  • Ghana Tayi Watsi Da Yarjejeniya Akan Hakar Ma’adanai Afrika
  • An Zargi Shugaba Trump Da Kalaman Da Basu Dace Ba Afrika
  • Jirgin Sama Ya Fadi A Kano Labarai
  • Najeriya Ta Kai Wasan Kusa Da Na Karshe A Wasan Dambe Na Matasan Afirka Wasanni
  • Shirin Safe 0500 UTC Yau Alhamis 11.20.2025 Rediyo
  • Amurka Ta Janye Sojojinta Daga Gabas Ta Tsakiya Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.