Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Sabuwar Shekarar Musulunci 1448: Kiristoci Sun Yi Murna, Sunyi Kiran Samar Da Hutu Ga Shekarar Musulunci
Published: June 16, 2026 at 1:56 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugabannin Kungiyar Kiristoci a Arewacin Najeriya sun miƙa saƙonnin taya murna ga Musulmi a Najeriya da ma duniya baki ɗaya, bisa shigowar Sabuwar Shekarar Musulunci (Hijira 1448), inda suka jaddada muhimmancin zaman lafiya, jituwa da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai.

Sun kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta yi la’akari da ayyana ranar Sabuwar Shekarar Musulunci a matsayin ranar hutu ta ƙasa, domin bai wa Musulmi damar gudanar da bukukuwan su cikin natsuwa da tunani.

Shugaban Majami’ar Christ Evangelical and Life Intervention Ministry da ke Kaduna, Pastor Yohanna Buru, ya taya Musulmi murna, tare da kiran a ƙara yin addu’o’in zaman lafiya da haɗin kai a Najeriya da yankin Yammacin Afirka baki ɗaya.

A yayin ziyararsa ga wasu malaman Musulunci, Pasto Buru ya ce wannan na daga cikin ƙoƙarinsa na ƙarfafa dangantakar addinai da inganta zaman lafiya tsakanin Kirista da Musulmi a jihar Kaduna da ƙasar baki ɗaya.

Ya ce ya saba amfani da kafafen sada zumunta wajen aika saƙonnin zaman lafiya a duk Sabuwar Shekarar Musulunci, domin taya abokansa Musulmi murna tare da yi musu fatan alheri.

Ya kuma buƙaci al’ummar Jihar Kaduna da su ci gaba da zama cikin zaman lafiya, tare da goyon bayan matakan gwamnati na ƙarfafa haɗin kai da daidaito a ƙasa.

“Nigeriyawa su riƙa nuna haƙuri da yafiya, su kuma mara wa gwamnati baya wajen ƙoƙarin tabbatar da haɗin kai na ƙasa da magance matsalolin da suka shafi ƙabilanci, siyasa da addini,” in ji shi.

A nasa jawabin, Pasto John Immanuel ya yi kira ga mazauna Kudancin Kaduna da su ƙara rungumar zaman lafiya da fahimtar juna.

Ya kuma taya Musulmi murna, tare da yin addu’ar Allah ya kawo ƙarshen matsalolin tsaro da ke ci gaba da addabar sassan Arewacin Najeriya.

A wani ɓangare kuma, wasu malaman Musulunci, Mallam Idris Musa da Liman Ilyasu Husaine, sun nuna godiya ga shugabannin Kiristoci bisa saƙonnin goyon baya da fatan alheri da suka aiko.

Sun ce bikin Sabuwar Shekarar Musulunci ba na Musulmi kaɗai ba ne, illa na dukkan bil’adama, domin yana ɗauke da saƙon zaman lafiya da juna.

A ranar Talata 16 ga Yuni, 2026, daidai 1 ga Muharram 1447, ne ake fara sabuwar shekarar Musulunci, bisa ganin jinjirin wata.

Sabuwar Shekarar Musulunci na tunawa da Hijirar Manzon Allah (SAW) daga Makka zuwa Madina, wadda ke da matuƙar muhimmanci a tarihin Musulunci.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Nishadi, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Sabuwar Shekarar Musulunci: Shugaban Gwamnonin Arewa Ya Yi Kira Da A Yawaita Addu’o’i Da Haɗin Kai
Next Post: Shugaba Tinubu Ya Yabawa Dakarun Tsaro Bisa Ceto Matar Marigayi Janar Rabe

Karin Labarai Masu Alaka

Tinubu Ya Kawo Ƙarshen Aikin Kwamitin Sayar Da Kaddarorin Gwamnati Afrika
Farmakin Da Aka Kai Makarantar Mata A Iran Yayi Ajalin Yara Da Dama Afrika
Idan Allah Yasa Muka Kafa Gwamnati Zamu Kyautata Wa Ma’aikata Yakubu Adamu Dan Takarar Kujeran Gwamnan Bauchi Labarai
Wasan Hamayya (Istanbul Derby) Fenerbahçe Da Galatasaray 1-1 Labarai
Bangladesh Tasamu Rangwamen Harajin Da Amurka Ta Kakaba Mata Labarai
Ga Fili Ga Doki Najeriya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Zamu Hada Kai Mu Yaki Cutar Shan’inna (Polio) Labarai
  • Allah Ya Yi Wa Sheikh Dahiru Bauchi Rasuwa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Tawayen Houthi Sunkai Hari Isra’ila Afrika
  • Hamas Ta Kwance Damara Afrika
  • Kananan Hukumomi Na Kokarin Karbar Kudadensu Daga Jihohi Najeriya
  • Sunayen Jakadu: Kungiyar CISLAC Ta Nemi A Janye Sunan Mr. Ayodele Oke Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • An Fara Dawo Da Alhazain Najeriya Gida Afrika
  • Shugabannin Sojojin Najeriya sun Kai Ziyarar Aiki Maiduguri  Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.