Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Ce Albashin ₦70,000 Ya Gaza Biyan Bukatun Ma’aikata Afrika
  • NUJ Gombe Ta Ƙarfafa Bin Ɗa’a A Aikin Jarida, Ta Kaddamar Da Kwamitin Ladabtarwa Afrika
  • Hukumar UBRBDA Ta Fara Raba Kayan Noma A Gombe, Yobe Da Borno Amurka
  • Masu Ruwa Da Tsaki Sun Buƙaci Ƙarin Tallafi Ga Iyaye Mata Masu Shayarwa A Gombe Afrika
  • Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Yi Gargaɗi Ga Masu Karya Dokokin Hanya Afrika

Farmakin Da Aka Kai Makarantar Mata A Iran Yayi Ajalin Yara Da Dama
Published: March 12, 2026 at 4:22 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Wani Harin da aka kai a makarantar ‘yan mata ta Iran wanda ya yi sanadin mutuwar yara da dama na iya kasancewa sakamakon amfani da bayanan da Amurka ta yi amfani da su a baya, kamar yadda wasu majiyoyi biyu da ke da masaniya kan lamarin suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a ranar Laraba, inda suka ba da sabbin bayanai game da abin da zai kasance cikin mafi muni da fararen hula suka rasa rayukansu cikin shekaru da dama da aka shafe ana gwabzawa da Amurka.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton farko a yau alhamis cewa wani bincike na cikin gida na sojojin Amurka da ke ci gaba da gudana ya nuna cewa akwai yiwuwar sojojin Amurka ne suka kai harin da aka kai makarantar ‘yan matan da ke Minab.

Kamar yadda wani Bidiyo da ya fito wanda masana suka ce da alama ya nuna makami mai linzami na Amurka Tomahawk ya afkawa yankin. Sai dai ba a san ainihin yadda lamarin ya faru ba, kuma ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta ki cewa komai, tana mai cewa ana ci gaba da gudanar da bincike.

Harin wanda aka kai a rana ta farko ta harin da Amurka da Isra’ila suka kai kan Iran, ya kashe dalibai 150, a cewar jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya a Geneva, Ali Bahreini.

Afrika, Amurka, Labarai, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Rikicin Gabas Ta Tsakiya Yanuna Alakar Kasashen Da Najeriya
Next Post: Jama’a A Yankin Gulf Sun Bukaci Dakatar Da Hare Hare Daga Washington

Karin Labarai Masu Alaka

Tinubu: Zamu Kara Kyautata Samar Da Kayan Aiki Ga Jami’an Tsaro Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Gabannin Harin Amurka Da Isra’ila Iran Farisa Ta Shirya Nata Afrika
Hukumar Hasashen Kasuwanci Na Zargin Saida Bayanan Sirri Amurka
Sabon Magajin Garin New York Zai Soke Wasu Dokoki Amurka
Gwamnonin Arewa Maso Yammacin Najeriya Sun Halarci Taron Inganta Makashi A Birnin Landan Afrika
Isra’ila Zata Kai Hari Cibiyar Makamashin Iran Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Ce Albashin ₦70,000 Ya Gaza Biyan Bukatun Ma’aikata
  • NUJ Gombe Ta Ƙarfafa Bin Ɗa’a A Aikin Jarida, Ta Kaddamar Da Kwamitin Ladabtarwa
  • Hukumar UBRBDA Ta Fara Raba Kayan Noma A Gombe, Yobe Da Borno
  • Masu Ruwa Da Tsaki Sun Buƙaci Ƙarin Tallafi Ga Iyaye Mata Masu Shayarwa A Gombe
  • Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Yi Gargaɗi Ga Masu Karya Dokokin Hanya

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • An Gurfaranar Da Wadanda Ake Zargi Takai Hari Gaban Kotu Najeriya
  • Rasha Ta Nuna Kudurin Cimma Zaman Lafiya Da Ukraine Amurka
  • Shirin Safe 0500 UTC Yau Asabar 11.15.2025 Rediyo
  • Dakarun Gwamnatin Kasar Sham Tayi Mamaya Zuwa Gabashin Kasar Labarai
  • Anyi Girgizar Kasa Mai Karfi A Kasar Mexico Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ankara Gano Wani Abu Mai Kama Da Abun Fashewa A Jabo Jihar Sokoto Tsaro
  • Wasan Dambe Ya Dau Sabon Salo A Jihar Inugu Wasanni
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.