Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Rwanda Zata Janye Dakaru Daga Mozambique
Published: March 14, 2026 at 7:46 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Kasar Rwanda ta ce zata janye dakarun ta daga yankin Cabo Delgado na kasar Mozambique, inda suke taimakawa wajen dakile hare-haren ‘yan ta’adda, idan kokarin nata baya samun goyon baya na tallafin kudade daga kasashen waje.

Dakarun da aka aike su tun shekarar 2021 bayan da Mozambique ta bukaci hakan, sun taimaka wajen kawo kwanciyar hankali a yankunan da da ke fama da ‘yan ta’adda, a cewar mai magana da yawun gwamnatin Rwanda a Yolande Makolo, a shafin sa na sada zumunta na X.

A wani rahoto na mujallar kasuwanci da kasafin kudi ta Bloomberg, tallafin da Tarayyar Turai ke bawa dakarun zai kare a watan Mayu, kuma babu wani shiri na sabunta shi.

Jami’an Tarayyar Turai a Brussels basu ce komai game da tambayoyin da aka yi musu kan sha’anin ba.

Da yake nuni kan rahoton na Bloomberg, Yolande Makolo yace, dorewar dakarun ya ta’allaka ne ga samun isassun kudade, wanda ake gani. Ya kara da cewa, idan ba’a ganin amfanin aikin dakarun na Rwanda da ake kira RDF a Cabo Delgado, suna da dama su bukaci gwamnati ta kawo karshen yarjejeniyar yaki da ta’addanci, su fice daga wajen.

Afrika, Labarai, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Ruwan Sama Yayi Ajalin Mutane 70 A Nairobi
Next Post: An Gudanar da Taron Kwana Biyu kan Tsarin Sa Ido da Tantance Ayyukan AGILE a Jihar Gombe 

Karin Labarai Masu Alaka

Kakakin Majalisar Kasar Amurka Yana Tsaka Mai Wuya Game Da Kasafin Kudi Amurka
Shugaba Tinubu Ya Nada Shugaban NAHCON Labarai
Majalisar Wakilai Ta Rikon Kwaryar Nijar Ta Gudanar Da Zama Karo Na Biyu Afrika
Gwamnatin Gombe Ta Kulla Yarjejeniyar Da New Zealand Kimiya
Gwamnonin Arewa Sunyi Allah Wadai Da Matsalar Tsaro A Shiyar Labarai
Netanyahu: Zamu Kashe Dala Billiyan $110 Cikin Shekaru Hudu Don Kera Makamai Sauran Duniya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • SERVICOM, ATBUTH Ta Cafke Wani Da Ake Zargin Dan Damfara Ne Labarai
  • An Bude Gasar Kwallon Kafa Ta Mata A Najeriya NWFL 2025 Wasanni
  • Chelle: Rashin Jituwa Tsakanin Osimhen Da Lookman Matsala Ce Ta Cikin Gida Wasanni
  • Asusun IMF Zasu Ziyarci Kasar Gabon Afrika
  • Gidauniyar Jalo Wali Ta Ƙaddamar Da Bada Audugar Mata A Gombe Afrika
  • Hatsarin Mota Yayi Ajalin Mutum 7 A Gombe Najeriya
  • Sanarwar MDD Ya Nuna Aniyar Mayakan RSF Na Kisan Kare Dangi Afrika
  • Amurka Tasakawa Sojin Rwanda Takunkumi Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.