Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gwamna Inuwa Yahaya Ya Amince Da Gyaran Fadar Sarkin Gombe Afrika
  • Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Ce Albashin ₦70,000 Ya Gaza Biyan Bukatun Ma’aikata Afrika
  • NUJ Gombe Ta Ƙarfafa Bin Ɗa’a A Aikin Jarida, Ta Kaddamar Da Kwamitin Ladabtarwa Afrika
  • Hukumar UBRBDA Ta Fara Raba Kayan Noma A Gombe, Yobe Da Borno Amurka
  • Masu Ruwa Da Tsaki Sun Buƙaci Ƙarin Tallafi Ga Iyaye Mata Masu Shayarwa A Gombe Afrika

An Gudanar da Taron Kwana Biyu kan Tsarin Sa Ido da Tantance Ayyukan AGILE a Jihar Gombe 
Published: March 15, 2026 at 4:21 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

A wani yunƙuri na kafa tubali mai ƙarfi wajen sa-ido da tantance ayyukan shirin AGILE, Shirin AGILE na jihar Gombe tare da haɗin gwiwar kamfanin Taruscom International sun gudanar da horon kwana biyu kan ƙirƙirar tsarin Dashboard na sa-ido da tantance ayyuka, tare da horaswa a aikace kan amfani da manhajar Kobo Toolbox.

Da take buɗe taron horon a Otel ɗin Custodian da ke Gombe, Mai Kula da Shirin a matakin jihar, Dakta Amina Haruna Abdul, ta yaba wa masu ba da shawara kan shirya wannan shiri, tana mai cewa horon zai taimaka matuƙa wajen sabunta ilimin mahalarta.

Dakta Amina Abdul ta ƙara da cewa, horon kamar yadda ke ƙunshe a cikin sharuddan aikin kamfanin masu ba da shawara an tsara shi ne domin horas da ma’aikatan Sashen Aiwatar da Shirin a jiha (SPIU) da kuma jami’an Tsarin Bayanai na Ilimi (EMIS) daga Ma’aikatar Ilimi, Hukumar Ilimin Bai-ɗaya ta Jiha (SUBEB) da kuma ƙananan hukumomi a faɗin jihar.

Don haka ta buƙaci mahalarta da su yi amfani da wannan dama domin amfana da ƙwarewar masu horaswar.

Tun da fari a jawabin buɗe taron, Shugaban sashen sa-ido da tantance ayyuka na AGILE a jihar, Malam Abubakar Sadiq Mohammed, ya bayyana cewa horon zai taimaka wa mahalarta su ƙara samun ilimi kan hanyoyin tattara rahotanni da sauran manhajojin da ake amfani da su wajen sa-ido da ayyukan AGILE.

Daga Gombe Wakilin GTA Hausa Amurka Ke Magana Aliyu Bala Gerengi Yana dauke da cikekken rahoto

https://gtahausa.com/wp-content/uploads/2026/03/AGAILE-HAUSA.mp3
Afrika, Labarai, Najeriya, Rediyo

Post navigation

Previous Post: Rwanda Zata Janye Dakaru Daga Mozambique
Next Post: Jami’ai Daga Amurka Sunce Yakin Amurka Da Iran Zaizo Karshe

Karin Labarai Masu Alaka

An Gargadi Kasar Canada Game Da Tura Sojoji Lebanon Afrika
Shugaba Tinubu Ya Tafi Kasar Faransa Afrika
‘Yan Majalisar Wakilai 17 Sun Fice Daga ADC Afrika
Iran Ta Tsagaita Kai Hare Hare Makwabta Afrika
PDP Ta Koka Kan Rushe-rushe, Korar Gombawa Motors da Zaɓen Kananan Hukumomi A Gombe Afrika
Kungiyar HPV A Jihar Gombe Ta Jagoranci Yaki Da Karuwar Cutar Daji Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Gwamna Inuwa Yahaya Ya Amince Da Gyaran Fadar Sarkin Gombe
  • Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Ce Albashin ₦70,000 Ya Gaza Biyan Bukatun Ma’aikata
  • NUJ Gombe Ta Ƙarfafa Bin Ɗa’a A Aikin Jarida, Ta Kaddamar Da Kwamitin Ladabtarwa
  • Hukumar UBRBDA Ta Fara Raba Kayan Noma A Gombe, Yobe Da Borno
  • Masu Ruwa Da Tsaki Sun Buƙaci Ƙarin Tallafi Ga Iyaye Mata Masu Shayarwa A Gombe

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Tsohon Alkalin Alkalai A Najeriya Ya Rasu Yana Da Shekaru 71 Labarai
  • Ministan Tsaro Ya Umarci Janye Sojoji Daga Shingayen Bincike A Tituna Najeriya
  • Shugaban Afrika Ta Kudu Yanuna Goyon Bayan Kawo Karshen Yaki Tsakanin Rasha Da Ukraine Afrika
  • ‘Yan Tawaye A Burkina Faso Sun Kashe ‘Yan Kasar Ghana Afrika
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Dan Gaddafi A Gidansa Dake Kasar Libya Afrika
  • Ko Meye Gaskiyar Rade-Radin Zanga-Zanga A Jos Dake Jihar Filato Labarai
  • Gwamnatin Tarayya: Bikin Al’adun Argungu Ya Karbu A Idon Duniya Labarai
  • ‘Yan Bindiga Sun Jikkata Mutane A Arewacin Kasar Benin Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.