Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya Afrika
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel Afrika
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki Afrika
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe Afrika
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba Afrika

Za’ayi Auren Zawarawa Dubu Uku A Kano
Published: April 29, 2026 at 2:21 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnatin Kano ta sanar da shirye-shiryen auren gata ga mutane dubu 3,000.

Gwamnatin Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Abba Kabir Yusuf, ta sanar da wani babban shiri na jin ƙai ga al’umma, inda za ta aurar da mutane dubu 3,000 a lokaci guda, wanda ya ƙunshi maza 1,500 da mata 1,500.

Sanarwar hakan ne ƙunshe cikin wani rubutu da kwamandan Hisbah na jihar Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya wallafa a Shafinsa na Facebook.

Sheikh Daurawa ya bayyana cewa auren zai fi mayar da hankali ne ga marayu da kuma mutane masu ƙaramin ƙarfi, da nufin taimaka musu wajen gina rayuwar aure mai ɗorewa.

Kwamandan ya ƙara da cewa a cikin Shirin, kowanne ma’aurata za su samu cikakken tallafi, wanda ya haɗa da:

• Kayan ɗaki: gado, madubi, katifa, matasai da zanin gado

• Kayan abinci: shinkafa, taliya (spaghetti) da man girki

• Tufafi: zannuwan Ankara da hijabi ga mata; shadda da hula ga maza

• Sadaki: Naira 100,000 ga kowace amarya

• Tallafin sana’a: Naira 100,000 ga kowace mace domin fara ƙaramar sana’a

•Domin tabbatar da lafiyar masu niyyar shiga da kuma cancantarsu, za a gudanar da gwaje-gwajen lafiya, sannan masu nema za su cika fom guda uku na tantancewa.

Wannan shiri na nuna ƙudurin gwamnati wajen tallafa wa al’umma, rage talauci, da bunƙasa ci gaban jama’a.

Afrika, Najeriya, Nishadi

Post navigation

Previous Post: Kotu Tayi Watsi Da Tarukan ADC Bangaren David Mark
Next Post: Shugaba Tinubu Ya Bukaci Samar Da Zaman Lafiya A Filato

Karin Labarai Masu Alaka

Kungiyar Cigaban Al’ummar Tangale Tace Bata Goyon Bayan Kai Ziyara Wa Gwamnan Gombe Labarai
Gidauniyar Sultan Ta Jaddada Muhimmancin Kula Da Lafiyar Yara A Gombe Afrika
Tantance Gaskiyar Bayanai Shi Ne Ginshiƙin Aikin Jarida Mai Nagarta – Abdulaziz Afrika
Kano: Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Amince da Garo A Matsayin Mataimakinsa Na 2027 Afrika
Tinubu Ya Kafa Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Afrika
Malami: “Da Gwamnatin Tarayya Na Daukar Shawara Da Ba’a Kai Inda Ake Ba” Najeriya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • ECOWAS Zata Kafa Rundunar Yaki Da Rashin Tsaro Afrika
  • Rundunar Sojin Iran Tace Harin Amurka Ya Kashe Musu Sama Da Mutane Dari Afrika
  • Shirin Safe 0500 UTC Yau Talata 11.18.2025 Rediyo
  • Ana Cigaba Da Shirye-Shiryen Fara Gasar Kwallon Sarakuna A Gombe Afrika
  • Fubara Yana Yiwa Dimokraɗiyya Zagon Kasa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Babban Hafsan Tsaron Najeriya Ya Gargadi Jama’ar Arewa Maso Gabas Afrika
  • Jirgin Ruwan ‘Yan Gudun Hijira Ya Nitse Kogi A Tunisiya Labarai
  • Gwamna Fubara Ya Koma Jam’iyar APC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.