Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • NAWOJ Ta Yi Kira Ga Gwamnati Da Iyaye Kan Illolin Auren Wuri Afrika
  • Talauci Ya Hana Iyalan Ɗaliban Borno Da Aka Sace Zuwa Abuja Domin Zanga-Zanga Afrika
  • Shugaban Al’ummar Igbo Ya Buƙaci Karfafa Noma domin Tabbatar Da Wadataccen Abinci Afrika
  • An Bawa Fasto Yohanna Buru Sarautar “Jagoran Zaman Lafiyar Arewacin Najeriya” Afrika
  • Inuwa Yahaya Ya Yi Alkawarin Barin Gombe Ba Tare Da Bashin Fansho Ba Afrika

Jiragen Saman Yakin Najeriya Suka Gurgunta Yunkurin Juyin Mulki A Benin
Published: December 9, 2025 at 3:25 AM | By: Ibrahim Alfah Ahmad

Hukumomin Jamhuriyar Benin, sun fada jiya litinin cewa hare-haren da jiragen saman yaki na Najeriya suka kai sune suka gurgunta yunkurin juyin mulki a kasar, inda sojoji masu bore suka yi kokarin kama shugaba Patrice Talon.

Sojoji masu yunkurin juyin mulkin sun samu isa dab da Shugaba Talon, wanda ya gane ma idanunsa ba-ta-kashi tsakaninsu da masu gadinsa, kuma har sun iya suka kama wasu manyan hafsoshin soja guda biyu wadanda ba a sako su ba sai jiya litinin da safe.

Wadannan bayanan suna kumshe a cikin wata sanarwar da gwamnatin Jamhiriyar Benin ta wallafa game da yunkurin juyin mulkin, a bayan wani zaman majalisar ministocinta.

Sanarwar ta ce jiragen saman yakin Najeriya sun kai hare-hare suka lalata motocin yaki masu sulke na sojoji masu juyin mulkin, ba tare da sun kashe wani ba. Daga bisani, wasu zaratan sojoji daga kasar Cote D’Ivoire sun isa Cotonou, inda aka girka su domin daukar mataki ko da boren sojojin zai ci gaba.

Sojojin da suka yi yunkurin juyin mulkin sun fito daga sansanin soja na Togbin, inda tun kafin ketowar alfijir na ranar lahadi suka fara yada zango a gidan babban hafsan sojojin kasar, Janar Bertin Bada. An kashe matar janar din a gwabzawar da aka yi a wurin, amma hafsan ya samu ya tsere musu.

Sojojin sun samu suka kama babban hafsan sojojin kasa, Janar Abou Issa da Kanar Faizou Gomina, wadanda gwamnatin Benin ta ce an sako su daga bisani jiya litinin da safe a garin Tchaourou na arewacin kasar.

Masu yunkurin juyin mulkin, sun je suka kwace gidan telebijin na wani dan lokaci kafin a kore su, inda suka koma barikin Togbin, inda sojoji masu biyayya ga gwamnati da kuma jiragen saman yakin Najeriya suka yi ta far musu.

Har yanzu babu labarin inda Kanar Tigri Pascal yake, watau mutumin da aka ce shine jagoran masu yunkurin juyin mulkin.

Afrika

Post navigation

Previous Post: An Samar Da Dala Kusan Biliyan Biyu Don Yakar Polio
Next Post: Yarjejeniyar Britaniya Da Mauritius Kan Tsibiran Chagos Cin Zarafi Ne

Karin Labarai Masu Alaka

JEI Da Abokan Hulɗar Sun Gudanar Da Aikin Shuka Itatuwa Domin Bikin Ranar Muhalli Ta Duniya Afrika
Sanyin Hunturu Yayi Ajalin ‘Yan Cirani A Morocco Afrika
Amurka Da Kasashen Yamma Suna Cigaba Da Kai Ruwa Rana Akan Nukiliyar Iran Afrika
Wata Kotu A Abuja Ta Wanke Abba Kyari Afrika
Jamhuriyar Dimokraɗiyya Kwango Zata Karbi ‘Yan Gudun Hijirar Da Amurka Ta kora Afrika
Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • NAWOJ Ta Yi Kira Ga Gwamnati Da Iyaye Kan Illolin Auren Wuri
  • Talauci Ya Hana Iyalan Ɗaliban Borno Da Aka Sace Zuwa Abuja Domin Zanga-Zanga
  • Hukumomin Agajin Gaggawa Sun Bada Tallafin Abinci Ga ’Yan Gudun Hijira A Kebbi
  • Shugaban Al’ummar Igbo Ya Buƙaci Karfafa Noma domin Tabbatar Da Wadataccen Abinci
  • An Bawa Fasto Yohanna Buru Sarautar “Jagoran Zaman Lafiyar Arewacin Najeriya”

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kasar Saudiya Ta Sanar Da Ganin Watan Azumi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Bayan Sake Zaben Fidda Gwani PDP Ta Dakatar Da Mailantarki Da Garry Afrika
  • ‘Yan Tada Kayar Baya Sun Tayar Da Bom A Maiduguri Labarai
  • IBB: Ba Shakka Abiola Ya Lashe Zaben Yuni 12 Rediyo
  • Makokin Ashura: An Gudanar Da Taron Tunawa Da Aliyul Asghar A Gombe Afrika
  • Ana Zargin Tsohon Shugaban Kasar Philippines Da Ta’addaci A Lokacin Mulkinsa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • An Kashe Mutum 2 Da Suka Ba ‘Yan-Matan (GGCSS Maga) Kariya! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mbappé Ya Yi Hat-Trick Yayin Da Real Madrid Ta Lallasa Real Sociedad 4 Da 1 Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.