Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Ana Cigaba Da Shirye-Shiryen Fara Gasar Kwallon Sarakuna A Gombe
Published: May 13, 2026 at 12:58 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

An gudanar da bikin fitar da jadawalin wasannin Kofin Sarakunan jihar Gombe na shekarar 2026 cikin nasara a Cibiyar NITDA ICT da ke Jami’ar jihar Gombe, inda ya samu halartar sarakunan gargajiya, masu ruwa da tsaki a harkar kwallon kafa, ‘yan jarida da sauran baki daga sassa daban-daban na jihar Gombe

An shirya tare da daukar nauyin gasar ne daga GWG Sports. A yayin taron, an gabatar da sakonnin taya murna da fatan alheri daga masu ruwa da tsaki, sannan aka bayyana jadawalin wasannin kungiyoyin masarautu da na gargajiya da za su fafata a gasar.

Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Kwamitin Shirye-shiryen gasar Ahmad Shuaibu Gara Gombe, ya yaba wa sarakunan gargajiya da kafafen yada labarai bisa ci gaba da bayar da gudunmawa wajen bunkasa gasar. Ya ce masarautun jihar Gombe na da matukar rawar da suke takawa wajen samar da hazikan ‘yan wasan kwallon kafa da ke taimakawa ci gaban wasanni a jihar da ma kasa baki daya.

Ya kara da cewa an kirkiri wannan gasa ne domin karfafa hadin kai, inganta shigar matasa cikin harkar wasanni, da kuma gano sabbin basira a fadin jihar. Ya bayyana cewa an takaita shiga gasar ga kungiyoyin da aka yi rajista na masarautu da chiefdoms.

An gudanar da fitar da jadawalin karkashin jagorancin Shugaban Kwamitin Fasaha, Alhaji Abdulkadir Kawu, tare da Daraktan gasar, Haruna Isa Kalshingi, inda kungiyoyi suka zabi cibiyoyin wasannin su da suka hada da Kananan Hukumomin Funakaye, Deba da Billiri.

Haka kuma, taron ya samu halartar wakilan masarautu, jami’an kula da harkar kwallon kafa, da sauran masu ruwa da tsaki, wadanda suka yaba da cigaban gasar a matsayin wata hanya ta inganta zaman lafiya, hadin kai da bunkasa matasa ta hanyar wasanni.

An kammala taron ne da bayyana jadawalin wasanni a hukumance, addu’ar rufewa, da kuma daukar hoton tunawa tare da mahalarta daga masarautu da chiefdoms goma sha biyu na jihar Gombe

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Shirye-Shirye

Post navigation

Previous Post: Gwamnatin Najeriya Zata Samar Da Sabbin Dakunan Karatun Dalibai
Next Post: Hukumomin Bada Agaji Sun Fadakar Da Al’ummar Jihar Gombe

Karin Labarai Masu Alaka

Gwamnatin Najeriya Ta Jaddada Aniyarta Ta Daƙile Yaɗuwar Makamai Ba Bisa Ƙa’ida Ba Afrika
‘Yan Sanda A Gombe Sun Jaddada Shirin Yaƙi Da Munanan Dabi’u Afrika
Sabuwar Dama Ga Masu Zaɓe: INEC Ta Tsawaita CVR Zuwa Ƙarshen Yuli Afrika
ADC Ta Kaucewa INEC Ta Gudanar Da Babban Taro Labarai
Ana Cigaba Da Yaki Tsakanin Amurka Da Isra’ila Da Kasar Iran Afrika
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha: Tura Sojojin Birtaniya Ukraine Zai Kara Ta’azzara Yaki Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kasar Gambiya Ta Gayawa Kotun MDD Shirin Myanmar Akan Musulmai Afrika
  • Ukraine Ta Tura Tawagar Kwarerru Zuwa Kasashen Larabawan Domin Basu Kariya Labarai
  • GTA Hausa Logo
    Shirin Dare 2030 UTC Yau Juma’a 11.21.2025 Rediyo
  • An Sako Dan Siyasar Kasar Venezuela Daga Gidan Yari Labarai
  • Shugaban Amurka Yayi Watsi Da Tattaunawar Kawo Karshen Yaki Da Iran Afrika
  • Ankara Kai Wani Harin Bom Birnin Maiduguri Afrika
  • An Gudanar Da Addu’o’i Na Musamman Don Neman Zaman Lafiya Labarai
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.