Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Gwamnatin Najeriya Zata Samar Da Sabbin Dakunan Karatun Dalibai
Published: May 12, 2026 at 8:14 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirin kashe kudi kusan naira biliyan 250 a cikin shekarar 2026 domin gina sabbin dakunan kwanan dalibai a manyan makarantun gaba da sakandare na kasar.

Wannan mataki na kunshe ne a cikin wani babban shiri na kyautata jin dadin dalibai da kuma fadada damar samun ilimi mai inganci, wanda ake ganin shi ne jari mafi tsoka da aka taba zubawa a fannin gidajen dalibai a tarihin Najeriya.

Ministan Ilimi, Maruf Olatunji Alausa, ya bayyana cewa wannan shiri zai magance matsalolin karancin masauki da dalibai ke fuskanta.

Za a kashe naira biliyan 100 wajen gina dakunan kwanan dalibai masu dauke da gado 500 a kowace jami’a daga jami’o’i guda 50 a fadin kasar nan. Kowanne aiki daya an kiyasta shi a kan naira biliyan 2.

Za a gudanar da wasu ayyukan guda 24 na hadin gwiwa da masu zuba jari masu zaman kansu, inda gwamnati za ta bayar da biliyan daya, su kuma masu zuba jari su bayar da biliyan 3 a kowanne aiki. Wannan zai samar da masauki ga dalibai tsakanin 1,200 zuwa 1,500 a kowace makaranta.

Hukumar tallafawa manyan makarantu ta TETFund ce za ta dauki nauyin samar da wadannan kudade, inda za a yi amfani da su wajen gina sabbi da kuma gyara tsofaffin dakunan kwanan dalibai da suka lalace.

Babban burin wannan shiri shi ne samar da yanayi mai kyau na koyo da koyarwa, tare da rage cinkoson dalibai a daki daya da ake samu a manyan makarantun kasar nan a halin yanzu.

“Wannan shiri ne da zai tabbatar da cewa dalibanmu sun samu wurin kwana mai tsafta da walwala, wanda hakan zai taimaka musu wajen mayar da hankali kan karatunsu.” — Maruf Olatunji Alausa

Masana ilimi sun yi amanna cewa idan har aka kammala wadannan ayyuka, za a samu sauki kwarai wajen rage kuncin da daliban jami’o’i da kwalejoji ke fuskanta, musamman ‘ya’yan talakawa da ke dogara da masaukin makaranta.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya

Post navigation

Previous Post: Gwamnatin Tarayya Ta Cire Sharadin Rubuta UTME Ga Masu Neman Shiga Kwalejojin Ilimi
Next Post: Ana Cigaba Da Shirye-Shiryen Fara Gasar Kwallon Sarakuna A Gombe

Karin Labarai Masu Alaka

Karamar Sallah: Hukumar Kashe Gobara A Gombe Ta Kuduri Aniyar Kare Al’umma Afrika
NSCIA Ta Gargadi Gwamnati Kan Zargin Tauye Haƙƙin Musulmi Afrika
Gwamnatin Najeriya Ta Fara Aikin Babbar Hanyar Da Za Ta Haɗa Jihohin Arewa Afrika
An Samu Nasarar Karbo Karin Yara 130 Daga Hannun ‘Yan-Ta’adda Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Majalisar Tarayya Ta Amince Da Mutane Uku A Matsayin Jakadun Kasashen Waje Labarai
Gwamnan Jihar Gombe Ya Ƙarfafa Wa Sabbin Masu Ashaka Cement Gwiwar Samar Da Ayyukan Yi Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Sojojin Amurka Sun Kashe Wasu Fararen Hula Ba Dalili Amurka
  • SERVICOM, ATBUTH Ta Cafke Wani Da Ake Zargin Dan Damfara Ne Labarai
  • Najeriya Da Amurka Sun Amince Su Haɗa Kai Don Inganta ’Yancin Addini Da ƙarfafa Tsaro A Nijeriya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Yagana Da Shugaban Sa’ido Akan Nukiliya Afrika
  • Kamfanin Bitcoin A Korea Ta Kudu Yayi Kuskuren Turawa Masu Mu’amala Da Kamfanin Kudade Afrika
  • Majalisar Dattawar Najeriya Ta Amince Da Tura Sakamakon Zabe Ta Intanet Labarai
  • Bayan Rikicin Manoma Da Makiyaya, Kwamitin White Paper Ya Ziyarci Bojude Da Kwami Afrika
  • Ghana Tayi Watsi Da Yarjejeniya Akan Hakar Ma’adanai Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.