Wani matashin ɗan siyasa a jihar Gombe dake arewa maso Gabashin Najeriya Abdulhamid Ibrahim, ya yi kira ga gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya da hukumomin da abin ya shafa da su bi umarnin kotu domin tabbatar da adalci da daidaito ga dukkan jam’iyyun siyasa.
Abdulhamid Ibrahim, wanda ya fito daga garin Bambam da ke ƙaramar hukumar Balanga, ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da Manema labarai a Gombe kan halin da siyasar Gombe ta Kudu ke ciki, musamman a mazaɓun Billiri da Balanga.

Matashin ɗan siyasar ya yabawa gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya da ta Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa nasarorin da suka samu, amma ya jaddada muhimmancin bin doka da oda, tare da mutunta umarnin kotuna.
Ya ce kotun babban mataki ta bayar da umarnin gudanar da sabon zaɓen fitar da gwani cikin kwanaki talatin, yana mai cewa a cewarsa, kwanaki goma sha ɗaya ne kawai suka rage wa wa’adin, amma har yanzu ba a ga wani yunƙuri na aiwatar da umarnin ba.
Abdulhamid Ibrahim ya kuma bayyana Alfred Attahiri a matsayin ɗaya daga cikin matasa ’yan siyasa masu nagarta a Gombe ta Kudu da ya kamata a ba su dama domin su gwada sa’arsu a siyasa.
Ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar da an aiwatar da umarnin kotun, domin guje wa duk wani abu da ka iya kawo cikas ga wakilcin al’ummar mazaɓar a zaɓen gama-gari na shekarar 2027.
Ya ƙara da cewa mutunta umarnin kotu zai taimaka wajen tabbatar da adalci, ƙarfafa dimokuraɗiyya da kuma kare muradun al’ummar Gombe ta Kudu.


