Sanata Tambuwal na nan daram da cikakken goyon bayansa ga jam’iyyar ADC. Hankalinsa ya karkata ne wajen ƙarfafa jam’iyyar, gina haɗin gwiwa mai faɗi da kuma wayar da kan ’yan Najeriya gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Sanarwar Prince Daniel Mai Bai wa Sanata Aminu Waziri Tambuwal Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Dabarun Sadarwa ya sanar da cewa, a daidai lokacin da ’yan Najeriya ke neman amsoshi kan manyan ƙalubalen tattalin arziki, tsaro da shugabanci, ya kamata tattaunawar jama’a ta mayar da hankali kan muhimman batutuwa da gaskiya.
Hasashe marar tushe bai kamata ya ɗauke hankali daga muhimmin aikin samar wa ’yan Najeriya ingantaccen shugabanci da kyakkyawar makoma ba.
Muna kira ga magoya baya da sauran jama’a da su mayar da hankali kan ayyukan da ke gabansu. Ƙudurin Sanata Tambuwal na tabbatar da shugabanci mai ɗaukar alhaki, kiyaye ƙa’idojin dimokuraɗiyya da kuma inganta rayuwar ’yan Najeriya bai sauya ba.
Muna kira ga kafafen yaɗa labarai da masu sharhi a kafafen sada zumunta da su tabbatar da sahihancin irin waɗannan bayanai ta hanyar tuntuɓar Ofishin Yaɗa Labarai na AWT kafin wallafa su. Bai kamata a gabatar da hasashe a matsayin tabbatacciyar gaskiya ba.


