Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Ilimi: Gidauniyar Danbayo Ta Tallafa Wa Ɗalibai Dubu Uku A Gombe Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Ebola A Abuja Afrika
  • UNICEF Ta Miƙa Kwalayen Abincin Jinya Ga Yara Masu Tamowa A Gombe Afrika
  • Billiri/Balanga: Kotu Ta Bayar Da Umarnin Sabon Zabe, Amma Gwamnati Ta Yi Shiru – AB Ibrahim Afrika
  • Hukumomin Kashe Gobara A Gombe Sun Ƙarfafa Haɗin Kai Don Hana Gobara A Lokacin Bazara Labarai

Nafiu Baba-Ahmed: Tinubu Ya Yi Jimamin Rasuwar Babban Jigon Shari’a
Published: October 6, 2026 at 1:04 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaban Ƙasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhininsa bisa rasuwar Sakatare-Janar na Majalisar Koli ta Shari’ar Musulunci a Najeriya (SCSN), Malam Nafiu Baba-Ahmed, wanda ya rasu da sanyin safiyar Talata bayan tsawon shekaru yana hidimtawa addinin Musulunci da ƙasa.

Shugaba Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin jagora mai tasiri, wanda ya jagoranci harkokin Majalisar Koli ta Shari’a cikin hikima, hangen nesa da kishin haɗin kan al’umma, adalci da zaman lafiya.

Shugaban ya tuna da doguwar alaƙar da ke tsakaninsa da marigayin, musamman tun daga shirye-shiryen zaɓen shekarar 2011, da kuma shekarun baya, inda Malam Baba-Ahmed ya kasance cikin waɗanda suka ba shi shawarwari tare da mara masa baya a lokacin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

A cewar Shugaba Tinubu, marigayin ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da cewa Majalisar ta ci gaba da bayar da gudummawarta kan muhimman batutuwan ƙasa, tare da ƙarfafa fahimtar juna da kuma yaɗa kyawawan ɗabi’u, adalci da gyaran zamantakewar al’umma.

Shugaban Ƙasar ya miƙa ta’aziyyarsa ga Shugaban Majalisar Koli ta Shari’ar Musulunci a Najeriya, shugabanni da mambobinta, iyalan Baba-Ahmed, gwamnatin da al’ummar Jihar Kaduna, da kuma daukacin al’ummar Musulmi a Najeriya bisa wannan babban rashi.

Ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, Ya jikansa, Ya sanya shi cikin Aljannatul Firdausi, sannan Ya bai wa iyalansa da daukacin al’ummar Musulmi haƙurin jure wannan babban rashi.

Afrika, Labarai

Post navigation

Previous Post: NNGF Ta Yi Ta’aziyya Ga Musulmi Kan Rasuwar Nafiu Baba-Ahmed
Next Post: CP Chuso Ya Buƙaci Al’ummar Gwani Su Haɗa Kai Da ’Yan Sanda Wajen Yaƙi Da Laifuka

Karin Labarai Masu Alaka

Uwargidan Shugaban Ƙasar Najeriya Ta Ƙaddamar Muhimman Ayyuka A Jihar Jigawa Afrika
Diphtheria: Mutane 23 Sun Mutu A Jihar Filato Afrika
Shugaba Tinubu Ya Gana Da Masu Zuba Jari A Birnin Paris Afrika
Gwamnatin Tinubu Ta Karyata Kafa Kamfanin Gwal A Legas Labarai
Amurka Da Jamhuriyar Dimokraɗiyya Kwango Sun Fara Wata Tattaunawa Afrika
Hukumar Kula Da Makamashin Nukiliya Ta Duniya Zata Binciki Kasar Iran Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Agadez: An Gudanar Da Jana’izar Mutane Da Suka Mutu A Wani Harin Ta’addanci
  • Ilimi: Gidauniyar Danbayo Ta Tallafa Wa Ɗalibai Dubu Uku A Gombe
  • Gwamnatin Najeriya Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Ebola A Abuja
  • Tambuwal Ya Karyata Rahotannin Shirin Komawarsa APC
  • UNICEF Ta Miƙa Kwalayen Abincin Jinya Ga Yara Masu Tamowa A Gombe

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugaba Tinubu Ya Umurci Janyewa Manyan Mutane ‘Yan Sanda Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ministan Kudin Botswana Yace Akwai Hasashen Cewa Tattalin Arzikin Kasar Zai Ragu Amurka
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi Afrika
  • An Kama Wani Da Abubuwan Fashewa A Zamfara Najeriya
  • Anyi Bikin Cikar Tsohon Shugaban Kasa Abdulsalami Shekaru 84 Afrika
  • Wikki Tourists FC: Ta Yi Sabbin ‘Yan Wasa Uku Wasanni
  • Kasar Saudiya Ta Sanar Da Ganin Watan Azumi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Tinubu: Munsayi Jiragen Yaki Daga Wajen Amurka Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.