Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Ilimi: Gidauniyar Danbayo Ta Tallafa Wa Ɗalibai Dubu Uku A Gombe Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Ebola A Abuja Afrika
  • UNICEF Ta Miƙa Kwalayen Abincin Jinya Ga Yara Masu Tamowa A Gombe Afrika
  • Billiri/Balanga: Kotu Ta Bayar Da Umarnin Sabon Zabe, Amma Gwamnati Ta Yi Shiru – AB Ibrahim Afrika
  • Hukumomin Kashe Gobara A Gombe Sun Ƙarfafa Haɗin Kai Don Hana Gobara A Lokacin Bazara Labarai

NNGF Ta Yi Ta’aziyya Ga Musulmi Kan Rasuwar Nafiu Baba-Ahmed
Published: October 6, 2026 at 12:38 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Ƙungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya (NNGF) ta bayyana matuƙar alhini da jimami bisa rasuwar Babban Sakataren Majalisar Ƙoli ta Shari’ar Musulunci a Najeriya (SCSN), Malam Nafiu Baba-Ahmed, wanda ya rasu a yau.

A cikin wata sanarwa Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya, kuma Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai hikima, adalci da kishin ɗabi’a, wanda gudunmawarsa wajen tattaunawar al’amuran ƙasa ta sanya ya samu girmamawa a Arewacin Najeriya da ma ƙasar baki ɗaya.

Gwamna Inuwa Yahaya ya ce rasuwar Nafiu Baba-Ahmed babban rashi ne ga Arewacin Najeriya, al’ummar Musulmi da kuma ƙasar baki ɗaya.

Ya bayyana cewa Najeriya ta yi rashin wata murya mai ƙarfi da tsayawa kan gaskiya, wadda shawarwari da tsoma bakinta a cikin muhimman al’amuran ƙasa suka taimaka wajen inganta tattaunawar jama’a da kuma ƙarfafa manufofin adalci da ɗaukar nauyin al’umma.

Gwamna Inuwa Yahaya ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, shugabanci da mambobin Majalisar Ƙoli ta Shari’ar Musulunci a Najeriya, Gwamnati da al’ummar Jihar Kaduna, da kuma daukacin al’ummar Musulmi.

Ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki da Ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, Ya yawaita masa ladan kyawawan ayyukansa, Ya kuma sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Post navigation

Previous Post: Gwamna Zulum Ya Jinjinawa Inuwa Yahaya Kan Sauya Fasalin Gombe
Next Post: Nafiu Baba-Ahmed: Tinubu Ya Yi Jimamin Rasuwar Babban Jigon Shari’a

Karin Labarai Masu Alaka

Mohammed Abdullahi Abubakar Ya Sayi fom Don Tsayawa Takarar kujeran Gwamnan Bauchi A APC 2027 Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Kungiyar Maharba Da ‘Yan Sintiri Sun Samu Kyautar Motoci Labarai
Billiri/Balanga: Kotu Ta Bayar Da Umarnin Sabon Zabe, Amma Gwamnati Ta Yi Shiru – AB Ibrahim Afrika
Birtaniya Ta Bukaci Israela Ta Janye Shawarar Fadada Iko Da Kogin Jordan Labarai
An Saka Dokar Hana Fita A Jos Ta Arewa Afrika
Hukumar DSS Ta Sake Kama Abubakar Malami Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Agadez: An Gudanar Da Jana’izar Mutane Da Suka Mutu A Wani Harin Ta’addanci
  • Ilimi: Gidauniyar Danbayo Ta Tallafa Wa Ɗalibai Dubu Uku A Gombe
  • Gwamnatin Najeriya Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Ebola A Abuja
  • Tambuwal Ya Karyata Rahotannin Shirin Komawarsa APC
  • UNICEF Ta Miƙa Kwalayen Abincin Jinya Ga Yara Masu Tamowa A Gombe

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • ‘Yan-Ta’adda Sun Yi Ma Wasu Mutane Yankan Rago A Jihar Neja Labarai
  • ‘Yan Kungiyar Boko Haram Sun Yi Awon Gaba Da Mata 13 A Borno Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Sace Ni Bai Hana Ni Bin Hanyar Jere Ba-Ali Gantsa Labarai
  • Wani Abu Ya Fashe A Ofishin Jakadancin Amurka Dake Kasar Norway Afrika
  • Dangote Ya Rage Farashin Mai A Najeriya Labarai
  • An Yi Fashin Kaguwa Da Dodon-Kodi Na Miliyoyin Dalar Amurka Amurka
  • Zabebben Shugaban Hungary Yace Zaidawo Da Tsarin Dimokraɗiyya Afrika
  • Bayan Rikicin Manoma Da Makiyaya, Kwamitin White Paper Ya Ziyarci Bojude Da Kwami Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.