Sace Ni Kan Hanyar Abuja Bai Sa Na Daina Bin Hanyar Ba-Alh. Ali Gantsa
Shahararren dan siyasa Alhaji Ali Tukur Gantsa ya ce duk d fadawa tarkon barayin mutane kan hanyarsa zuwa Abuja ta ratsen Jere har Allah ya yi wa abokin tafiyarsa Alha.Abba Anas rasuwa, bai hana shi cigaba da bin hanyar ba “na kan bi hanyar don komai za ka yi ka dogara ga Allah”
Alhaji Ali Gantsa dai ya ba da labarin yadda barayi su ka sace shi tare da tsohon dan majalisar wakilai Abba Anas Adamu a tsakanin yankin Jere da Bwari a wani dare da su ke tahowa Abuja “mu biyu ne a motar ni da Alhaji Abba kuma ni ke tuka motar inda mu na cikin tafiya sai mu ka iso shingen barayi har zan juya sai na ga sun haska tocila ko ta ina”

Ali Gantsa ya ce barayin kimanin 7, sun dauke su, su ka yi ta tafiya da su a cikin daji kuma kamar sun nufi wajajen dajin Rijana ne inda bayan kwana biyu a ka shiga cinikin yadda za a dau fansar su “ni da su ka dauka direba ne su ka aza min biyan Naira miliyan 15 shi kuma Alhaji Abba da ya ke da alamun manyan mutane a gwamnati su ka ce zai biya Naira miliyan 35 wato duk kudin Naira miliyan 50”
Alhaji Gantsa ya cigaba da cewa daga bisani bayan magana ta waya da ‘yan uwa, nan ne su ka kara kudi har a ka tsaya kan Naira miliyan 75 kuma su ka cigaba da yi mu su barazana da kisa ta hanyar shuna mu su bindiga.
Kazalika Ali Gantsa ya ce ya ji barayin na magana da Fulfulde don dama harshensa ne cewa in an kawo kudi za su rike daya daga masu kawowa, wannan ya sa ta hanyar magana ta waya ya ankarar da masu kawo kudi inda lokacin da su ka kawo kashi mafi tsoka na farko kusan Naira miliyan 60 sai su ka arce don kar su fada tarko.
Gantsa ya ce a lokacin da barayi su ka shagala da rabon kudi bayan sun kwance mu su daurin da su ka yi mu su, sai ya tashi Alhaji Abba inda bayan dan taku kadan sai Alhaji Abba ya yi kukan ciwon zuciya kuma a nan dai ba a jima ba Allah ya yi ma sa rasuwa “mun kwana 7 a daure kuma ba ma tashi ga shi ba magani ba abinci wanda hakan ya ta’azzara hawan jini na Alhaji Abba”

Wanda Allah ya kubutar din ya ce daga nan ya bar wajen ya shiga kungurmin daji har ya fada wani kogi inda ya ji barayin na harba bindiga su na nemansa. Da gari ya yi duku-duku wajajen asuba sai ya fice daga kogin ya shiga wata gona har ya isa wani kauye inda su ka ba shi kunu da kuma taimaka ma sa ya dawo Jere.
Alhaji Ali Gantsa ya ce da taimakon sojoji su ka koma daji inda su ka samo gawar marigayi Alhaji Abba Anas don yi ma sa jana’iza.
Da faruwar wannan jarrabawa, Alhaji Ali Gantsa ya ba da shawarar komawa tsarin tsaro irin na kaka-da-kakanni ta hanyar masu sarauta kama daga Dagaci, Hakimi zuwa Sarki don hakika su ne su ka san shiga da fitar kowa “idan waje ya nuna za a yi sulhu a yi idan ba bukata sai a dau matakin murkushewa”
Alhaji Gantsa ya ce babbar hanyar magance ta’addanci da barayin daji shi ne adalci na shugabanni da magance cin hanci da rashawa.
Wani darasi da Alhaji Gantsa ya lura da shi, shi ne yadda barayin ke samun bayanai don har shaida mu su, sun yi cewa motarsu na ajiye a ofishin ‘yan sanda a Jere. Hakanan ya ce sun ba su labarin duk abubuwan da su ka wuce a hanya kamar wata mota da kofarta ke bude har inda su ka iso shingen nasu.

