Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Wani Ya Yiwa ‘Yar Sa Mai Shekaru 8 Fyade A Bauchi
Published: January 8, 2026 at 5:10 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Rundunar ‘Yan Sandan jihar Bauchi a Najeriya ta kama wani mutum mai suna Baffaji Abba mai shekaru 28, bisa zargin yi wa ‘yarsa ta cikinsa mai shekaru takwas fyaɗe a ƙaramar hukumar Alkaleri.

A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Nafiu Habib ya fitar, ya bayyana cewa wani ɗan’uwan wanda ake zargin, Baffaji Muhammed, wanda ke zaune a adireshi ɗaya da shi, ne ya kai rahoto zuwa ofishin ‘yan sanda na Alkaleri a ranar 31 ga Disamba, 2025.

Rahoton ya ce lamarin ya faru ne a ranar 30 ga Disamba, 2025, inda wanda ake zargin ya yaudari yarinyar zuwa bandaki sannan ya tilasta mata mu’amala ta jima’i ta hanyar farji da dubura har sau da dama a rana ɗaya, ba tare da amincewarta ba.

Da rundunar ta samu rahoton, tawagar jami’an bincike ƙarƙashin jagorancin CSP Kadiri Danjuma, DPO na Alkaleri, suka je wajen da abin ya faru, suka kai yarinyar asibitin gwamnati na Alkaleri domin samun kulawar gaggawa, sannan suka kama wanda ake zargin.

Yayin bincike, wanda ake zargin ya amsa laifin da aka tuhume shi nan take.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Sani-Omolori Aliyu, ya umurci Mataimakin Kwamishinan ‘yan sanda mai kula da sashen binciken manyan laifuka (SCID) da ya gudanar da cikakken bincike mai zurfi bisa shaidu da hujjoji.

Ya jaddada kudurin rundunar na ganin an tabbatar da adalci kuma za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Post navigation

Previous Post: Sarkin Kagarko Ya Rasu Yana Da Shekaru 110
Next Post: Barau Jibril: Mu Ba ‘Yan Amshin Shata Bane A Majalisa

Karin Labarai Masu Alaka

Shugaba Trump Ya Jinjinawa Tinubu Kan Yaƙi Da Ta’addanci A Najeriya Afrika
Najeriya: Ta Aiwatar Da Tsarin Ba Aiki Ba Albashi Ga Ma’aikata Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Fadar Shugaban Ƙasan Najeriya Ta Musanta Wani Labarin ƙarya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Najeriya Da Amurka Sun Karfafa Alakar Tsaro Afrika
Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Ce Albashin ₦70,000 Ya Gaza Biyan Bukatun Ma’aikata Afrika
Farashin Mai Ya Fadi Fiye Da Dala Daya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Masar Ta Jibge Jiragen Yaki Marasa Matuka Afrika
  • Duniyar Dambe A Makon Jiya Nishadi
  • Babban Sakataren MDD Yayi Allah Wadai Da Matakin Soja A Gabas Ta Tsakiya Afrika
  • Yau Lahadi Ake Gudanar Da Zabe A Kasar Myanmar Labarai
  • ‘Yan Jaridar Gidan Gwamnatin Bauchi Sun Kammala Taron Horo Kan Fasahar Sadarwar Zamani Afrika
  • Babban Hafsan Tsaron Najeriya Ya Gargadi Masu Tayar Da Hankali Najeriya
  • Barayin Waya Sun Yanke Yatsun Hannu Guda Biyu Da Gefen Kunne A Bauchi Labarai
  • Harin Da Israela Ta Kai Gaza Yayi Ajalin Mutane 27 Da Yara Uku Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.