Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama Afrika
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara Afrika
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe Afrika
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro Afrika
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa Afrika

CHAN Ta Duba Lafiyar Idanun ‘Yan Jarida A Filato
Published: July 19, 2026 at 5:07 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Masana harkokin lafiya sun shawarci al’umma da su rika kula da lafiyar idanunsu tare da yin gwajin ido a kai a kai domin kaucewa kamuwa da cututtukan da kan haddasa makanta.

Sun bayyana cewa cututtukan ido ba wai kawai suna shafar lafiyar mutum ba ne, har ma suna jefa iyalai cikin matsin tattalin arziki, saboda mai fama da makanta kan rasa damar gudanar da wasu ayyukansa na yau da kullum tare da dogaro da ‘yan’uwa wajen kulawa da shi da kuma sayen magunguna.

Bayanai sun nuna cewa kimanin mutane miliyan 48 ne ke fama da nau’o’in cututtukan ido a duniya, yayin da masana ke hasashen adadin zai karu zuwa miliyan 61 nan da shekarar 2050 idan ba a dauki matakan kariya ba.

A wani yunkuri na inganta lafiyar ido, Kungiyar Christian Health Association of Nigeria (CHAN) ta shirya duba lafiyar idanun ‘yan jarida a Jihar Filato, domin tabbatar da cewa aikin da suke yi da na’urorin zamani bai jefa lafiyar idanunsu cikin hadari ba.

Daraktan kungiyar CHAN, Dakta Suleiman Mshelia, ya ce sakaci wajen kula da ido na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa matsalolin gani, musamman yayin da mutum ke kara shekaru.

Shi ma Farfesa Ezekiel Major Adeyi na Jami’ar Jos ya bayyana cewa ya shafe shekaru 30 yana fama da matsalar ido, amma saboda bin shawarwarin likitoci da kula da idanunsa, har yanzu yana iya karatu da rubutu duk da kusantar sa shekara 70 da haihuwa.

A nata bangaren, ‘yar jarida Hadiza Ahmad Hassan ta ce shirin ya kara mata ilimi kan yadda za ta kula da idanunta da kuma wayar da kan al’umma game da muhimmancin kula da lafiyar ido.

Masanan sun jaddada cewa yin gwajin ido a asibiti lokaci-lokaci na iya rage yawan masu makanta da kusan kashi uku cikin hudu, tare da yin kira ga gwamnati da ta hada kula da lafiyar ido cikin ayyukan kiwon lafiya domin saukaka wa al’umma samun wannan muhimmin ayyuka

Wakiliyar GTA Hausa Zainab Babaji tana dauke da cikekken rahoton Daga Jos

https://gtahausa.com/wp-content/uploads/2026/07/AUD-20260719-WA0026.mp3
Afrika, Kiwon Lafiya, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Tinubu Zai Gabatar Da Jawabi ga Shugabannin Duniya A Taron UNGA
Next Post: Shari’ar Ta’addanci: Manyan Jagororin Ansaru Biyu Sun Amsa Laifi A Abuja

Karin Labarai Masu Alaka

Channels TV: Ta Yi Rashin Hazikin Dan Jarida Mr Khani Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Mutane Kusan 30 Ne Suka Mutu a Nguru Dake Jihar Yobe Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Fadar Shugaban Kasa Ta Karyata Jita-Jitar Yunkurin Sanya Wa Tinubu Guba A Abinci Afrika
Ganduje: Mun Janye Shirin Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano Najeriya
Shugabannin Kiristoci Sun Taya Musulmi Murnar Sallah Domin Ƙarfafa Zaman Lafiya Afrika
Harkar Zirga Zirgar Jiragen Sama Ya Bunkasa A Kenya Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • An Yiwa Dokokin Kare Hakkin Yara Rikon Sakainar Kashi Labarai
  • Majalisar Dinkin Duniya Ta Amince Da Kudurin Kasar Ghana Afrika
  • Anyi Rashin Mutane Da Yawa Yayinda Bom Ya Fashe Ana Sallar Magariba Maiduguri Labarai
  • NAHCON Ta Fitar Da Jadawalin Hajjin Bana 2027 Afrika
  • Kudaden Shigan Kasar Namibia Ya Bunkasa Saboda Tashin Farashin Gwal Labarai
  • Karo Na Biyu Cikin Kwanaki 29 An Samu Gobara A Kasuwar Katako Labarai
  • ‘Yan Sandan Birnin New York Sun Karyata Zargin Jefa Bom Ga Masu Zanga Zanga Amurka
  • Zaben Fidda Gwani Ya Gudana Lafiya A Jihar Gombe Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.