Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Malaman Addinin Musulunci Da Kirista Sunyi Bikin Cika Shekara 15 Na Iftar A Najeriya
Published: February 27, 2026 at 5:03 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Tsohon Ministan Matasa da Wasanni a Najeriya Solomon Dalung, ya jagoranci tawagar fitattun Malaman Kirista daga Arewacin Najeriya zuwa taron buda bakin azumin Ramadan da aka gudanar a Kaduna, inda aka sake jaddada al’adar shekaru 15 na ƙarfafa zaman lafiya, haɗin kai da fahimtar juna tsakanin Musulmi da Kirista.

Ana gudanar da wannan taro na shekara-shekara a gidan marigayi Dahiru Usman Bauchi, wanda tsawon fiye da shekaru goma yana tara shugabannin addinan Musulunci da Kiristanci daga jihohin Arewa 19 domin tattauna muhimman batutuwa da kuma inganta zaman tare cikin lumana tsakanin mabiya addinai daban-daban.

Da yake jawabi a wajen taron, Dalung ya bayyana cewa iftar na wannan shekarar ya kasance mai cike da jimami sakamakon rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda har zuwa rasuwarsa bayan gajeriyar jinya, ya rika karbar bakuncin wannan iftar na haɗin gwiwar addinai da nufin inganta zaman lafiya da haɗin kan ‘yan Najeriya a gida da ƙasashen waje.

Yace, tsawon shekaru 15 ana haduwa a wannan wuri a lokacin Ramadan domin buda baki tare, tattauna matsalolin da ke addabar al’umma da kuma nemo hanyoyin da za a ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.

Dalung ya jaddada cewa marigayin malamin addinin Musulunci ya sadaukar da rayuwarsa wajen wa’azin zaman lafiya, haƙuri da juriya da kuma haɗin kai, yana mai cewa gadonsa zai ci gaba da zama haske wajen inganta fahimtar juna tsakanin addinai a Najeriya.

Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta gaggauta daukar matakai kan matsalolin tsaro da rashin kwanciyar hankali a ƙasa, yana mai cewa dorewar zaman lafiya shi ne ginshikin ci gaba a dukkan fannoni.

A nasa bangaren, Babban Limamin Majami’ar Christ Evangelical and Life Intervention Ministry da ke Gwagyi Villa a Kaduna, Yohanna Buru, ya bayyana muhimmancin wannan lokaci na ibada, yana mai cewa azumin Ramadan da na Lent sun zo a lokaci guda a wannan shekarar.

Ya ce sun zo ne domin taya ‘yan’uwansu Musulmi murnar fara azumin Ramadan da kuma kara dankon zumunci da aka dade ana ginawa bisa tattaunawa da mutunta juna.

Pastor Buru ya bayyana marigayi Sheikh Dahiru Bauchi a matsayin uba ga limaman Kirista da dama, tare da addu’ar Allah ya jikansa da rahama, ya kuma saka masa da Aljanna sakamakon gudunmawar da ya bayar wajen inganta zaman lafiya da hadin kai.

Shi ma Fasto Titus Ishaya ya yaba wa iyalan marigayin bisa ci gaba da karbar bakuncin malaman Kirista da manyan malaman Musulmi daga sassa daban-daban na Najeriya a wannan iftar na Ramadan.

Ya yi addu’ar Allah Ya saka musu da alheri bisa kokarinsu, tare da kira ga Gwamnatin Tarayya da ta karrama marigayin da iyalansa da lambar yabo ta kasa saboda rawar da suka taka wajen inganta fahimtar juna da zaman lafiya tsakanin Musulmi da Kirista.

A nasa jawabin na mayar da martani a madadin iyali, Sheikh Ibrahim Usman Dahiru Bauchi ya gode wa tawagar Kiristocin bisa amsa gayyata da kuma ci gaba da raya manufar haɗin kai da mahaifinsa ya assasa.

Ya tabbatar da cewa iyalan za su ci gaba da inganta zaman lafiya da kyakkyawar alaka tsakanin mabiya addinai, tare da kira ga ‘yan Najeriya da su kasance masu yawan addu’a da jajircewa wajen zaman tare cikin lumana duk da kalubalen da ake fuskanta.

Afrika, Labarai, Najeriya, Nishadi

Post navigation

Previous Post: Ana Cigaba Da Ceto Masunta Daga Ruwa A Ghana
Next Post: Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha: Tura Sojojin Birtaniya Ukraine Zai Kara Ta’azzara Yaki

Karin Labarai Masu Alaka

An Gano Wani Kurkukun Sirri Da Ake Azaftar Da Mutane A Kasar Libya Afrika
Kungiyar Kwadago Ta Shirya Zanga-Zanga A Najeriya Najeriya
‘Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji A Jihar Kebbi Afrika
NAHCON Ta Fara Shirye-shiryen Dawowar Alhazai Afrika
Zaman Lafiya Yafara Dawowa A Sudan Afrika
Gwamnatin Najeriya Na Shirin Yin Zamiya Don Biyan Bashi Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Yaki Ta Sararin Samaniya Ya Cigaba Tsakanin Amurka, Isra’ila Da Iran Afrika
  • Shirin Manuniya Kashi Na Daya, Yau Juma’a 11.21.25 Shirye-Shirye
  • Lewandowski: Zan Kokarta Zura Kwallo Ta 90 Don Kafa Tarihi A Poland Wasanni
  • Iran Tace Dole A Tsagaita Wuta A Lebanon Kafun Fara Shawarwari Amurka
  • Jam’iyar SDP Tana Gudanar Da Babban Taro A Bauchi Afrika
  • Rundunar Sojin Iran Tace Harin Amurka Ya Kashe Musu Sama Da Mutane Dari Afrika
  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama Afrika
  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.