Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Yaki Ta Sararin Samaniya Ya Cigaba Tsakanin Amurka, Isra’ila Da Iran
Published: March 3, 2026 at 4:58 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Yaki ta sararin samaniya da Amurka da Isra’ila suke yi kan Iran sun fadada shi ranar Litinin ba tare da sanin yau she zai so karshe ba, inda Isra’ila ta kai hari a Lebanon, a zaman martani ga harin da Hezbollah ta kai mata, sannan Iran tana ci gaba da kai hare hare da makamai masu linzami, da jiragen drones kan kasashe da suke yankin Gulf inda Amurka take da sansanonin.

Shugaban Amurka Donald Trump yace sai ta yiwu za’a ci gaba da yakin na tsawon makonni, tare da cewa ba’a san wanene mai fada a ji a Tehran ba, bayanda kisan shugaban addinin kasar Ayatollahi Ali Khameni, a farkon Farmakin na hadin guiwa da Amurka da Isra’ila suka kaddamar kan kasar.

Harin da Amurkan da Isra’ila suka kai kan Iran ya jefa yankin Gulf cikin yaki, yayi sanadin mutuwar mutane a Iran, da Isra’ila da lebanon, lamarin ya jefa zirga zirga da balaguro ta sama cikin yamutsi, da kuma rufe mashigin ruwa na Hormuz, inda kashi daya cikin biyar na mai da ake amfani a duniya yake bi kusada gabar ruwan Iran, wadda yasa farashin mai ya tashi.

Sakamakon yakin cibiyar gudanar yake yaki ta Amurka da ake kira Central Command da turanci, tace bisa kuskure Kuwait ta harbo jiragen yakin Amurka uku, amma duka ma’aikatan jirgin su shida sun tsallake rijiya da baya.

Afrika, Amurka, Labarai, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Hanyar Gombe Dukku Darazo Ta Zamo Abun Damuwa Ga Al’ummar Arewa Maso Gabashin Najeriya
Next Post: China Ta Yi Kira Da Kasashen Gabas Ta Tsakiya Su Hada Kai

Karin Labarai Masu Alaka

Gwamnatin Tarayya Ta Cire Sharadin Rubuta UTME Ga Masu Neman Shiga Kwalejojin Ilimi Afrika
Shugaban Hukumar NAHCON Ya Ajeye Mukaminsa Labarai
Akwai Bukatar APC Tayi Gyare-Gyare Kafun Zabe Afrika
Harin ‘Yan Daba Ya Hallaka Mutane 70 A Kasar Haiti Labarai
Jami’an Tsaro A Jihar Borno Sun Kama ‘Yan Bindiga Labarai
‘Yan Bindiga Sun Hallaka Sojoji 15 Da Wasu Fararen Hula A Benin Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Al’ummomin da Ambaliyar Ruwan Mokwa a Jihar Nejan Najeriya ta sharewa gidaje sun Koka. Najeriya
  • Rundunar Sojin Amurka Sunfara Ficewa Daga Kasar Sham Amurka
  • Jami’ai A Mexico Sun Tabbatar Da Kashe Shugaban Masu Shan Ƙwaya Nemesio Oseguera Labarai
  • Sarkin Musulmi Ya Ziyarci Shugaba Bola Tinubu Afrika
  • ’Yar Kasuwa Ta Tsallake Rijiya Da Baya Bayan Hari Da Saurayinta Ya Kai Mata Afrika
  • Gwamnatin Gombe Ta Kaddamar Da Sabon Ofishin GOGIS Don Inganta Tsarin Filaye Afrika
  • Ana Cigaba Da Shirye-Shiryen Fara Gasar Kwallon Sarakuna A Gombe Afrika
  • Hukumar Tsaro Ta DSS Ta Aika Sammaci Dr. Yusuf Baba-Ahmed Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.