Dubban malaman Alƙur’ani da malamai masu koyar da Tsangayoyi daga ƙananan hukumomi goma sha daya na jihar Gombe sun bayyana cikakken goyon bayansu ga gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, tare da amincewa da Dakta Jamilu Ishaku Gwamna a matsayin ɗan takarar gwamnan jam’iyyar APC.
Malaman sun bayyana hakan ne a wani babban taro da Ƙungiyar Malaman Tsangaya ta Jihar Gombe ta shirya, inda suka bayyana gamsuwarsu da ayyukan gwamnatin Gwamna Inuwa Yahaya, musamman a fannin ilimi, kiwon lafiya da walwalar Almajirai.
Sun ce matakan da gwamnatin ta ɗauka wajen inganta ilimin Tsangaya, ciki har da gina makarantun Tsangaya na zamani da samar da cibiyoyin karatu sama da 120 da aka tanada da kayan aiki, sun sauya yanayin karatun Almajirai a jihar.
Malaman sun ce wasu daga cikin ɗaliban Almajirai sun samu damar ci gaba da karatu a ƙasashen waje, yayin da wasu suka amfana da ingantattun wuraren kwana, koyon sana’o’i da kayan karatu.

Sun kuma yaba da shigar da Almajirai 1,000 cikin tsarin inshorar lafiya na Jihar Gombe, suna mai cewa shirin ya taimaka wajen inganta lafiyarsu da jin daɗin rayuwarsu.
Haka kuma, sun bayyana kafa Hukumar Almajiri ta jihar Gombe a matsayin wani muhimmin mataki da zai samar da ingantaccen tsari na tallafawa ilimin Alƙur’ani da makomar Almajirai.
Da yake wakiltar Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya a wajen taron, Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin jihar Gombe, Alhaji Abubakar Inuwa Kari, ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da bai wa ilimin addini da na zamani muhimmancin da ya dace.
Alhaji Inuwa Kari ya ce Gwamna Inuwa Yahaya ya kasance yana bai wa dukkan ’yan asalin Jihar Gombe damar jin cewa su ma suna da muhimmiyar rawa a tafiyar da harkokin jihar.
Ya kuma tabbatar wa malaman cewa gwamnatin za ta cika sauran alkawuran da ta ɗauka na tallafawa ilimin Alƙur’ani kafin ƙarshen wa’adinta.
Shugaban Ma’aikatan ya ce bayan shawarwari da tuntubar masu ruwa da tsaki, Gwamna Inuwa Yahaya ya goyi bayan Sardaunan Gombe, Dakta Jamilu Ishaku Gwamna, a matsayin wanda zai iya ci gaba da tafiyar da ayyukan ci gaba da gwamnatin ta fara.
Ya yi kira ga malaman da su ci gaba da addu’a da goyon bayan gwamnatin domin samun nasarar shirye-shiryenta na ci gaban jihar.
Shi ma Shugaban Ƙaramar Hukumar Gombe kuma Shugaban Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomi ta Najeriya (ALGON) a jihar, Farfesa Abdullahi Bappah Ahmed Garkuwa, ya gode wa malaman Alƙur’ani bisa goyon bayansu ga Gwamna Inuwa Yahaya da Dakta Jamilu Ishaku Gwamna.
Farfesa Garkuwa ya kuma yi kira da a ƙara bai wa Alarammomi da malaman Alƙur’ani dama wajen samun mukamai da shiga cikin harkokin gwamnati, domin hakan zai ƙara musu damar bayar da gudunmawa wajen ci gaban jihar.
A nasa bangaren, Kwamishinan Ƙananan Hukumomi, Barista Sani Ahmadu Haruna, ya buƙaci shugabannin ƙananan hukumomi da su yi koyi da Gwamna Inuwa Yahaya wajen tallafawa malaman Alƙur’ani da ayyukansu.
Ya ce hakan na cikin manufar gwamnatin na tafiyar da mulki cikin adalci da haɗa kan dukkan ɓangarorin al’umma.
Shi ma Sakataren Hukumar Jin Daɗin Alhazai a jihar, Alhaji Sa’adu Hassan Adamu ya yaba da ƙoƙarin gwamnatin wajen zamanantar da ilimin Almajirai da samar musu da kyakkyawar makoma.
Ya ce irin waɗannan ayyuka sun ƙarawa malaman Alƙur’ani kwarin gwiwar goyon bayan wanda Gwamna Inuwa Yahaya ya amince ya gaje shi, wato Dakta Jamilu Ishaku Gwamna.
Tun da farko, Babbar Mai Ba Gwamnan jihar Gombe Shawara kan Ilimin Almajirai da Tsangaya, Sayyada Amina Dahiru Bauchi, ta bayyana cewa gwamnatin Gwamna Inuwa Yahaya ta bai wa ilimin Tsangaya muhimmiyar kulawa.
Ta ce an gina manyan makarantun Tsangaya guda 11 a ƙananan hukumomi 11 na jihar, tare da samar da wasu cibiyoyin koyar da sana’o’i.
A cewarta, shirye-shiryen sun taimaka wajen bai wa Almajirai damar samun ilimin addini da na zamani, tare da koyon sana’o’in dogaro da kai.
Ta ce wasu daga cikin shirye-shiryen an fara su ne karkashin shirin Better Education Service Delivery for All (BESDA), wanda ya taimaka wajen inganta tsarin koyar da ilimin Alƙur’ani da ƙwarewar zamani.
Da yake jawabi a madadin ɗan takarar gwamnan APC, Alhaji Tanko Ishiyaku Gwamna, ya tabbatar da cewa Dakta Jamilu Ishaku Gwamna zai ci gaba da ayyukan da Gwamna Inuwa Yahaya ya fara, tare da ƙara inganta su.
Ya kuma yi kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa Gwamna Inuwa Yahaya, Dakta Jamilu Ishaku Gwamna da sauran ’yan takarar APC goyon baya.
An gudanar da taron ne tare da karatun Alƙur’ani da addu’o’in neman zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba a jihar Gombe da Najeriya baki ɗaya.


