Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar Na Kokarin Inganta Harkokin Noman Kasar
Published: December 24, 2025 at 2:27 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Jamhuriyar Nijar ta kudiri aniyar rage yawan shinkafa da masara da alkamar da ke shiga kasar daga ketare da kashi 50% kafin nan da shekarar 2027.

Gwamnatin ta Nijar tace wannan wani mataki ne da ke hangen samar wa kasar cikeken ‘yancin kai a fannin cimaka a daidai lokacin da ta ke kokarin katse abin da ta kira ‘’ragowar igiyoyin mulkin mallaka’’ da a ke hasashen su na dabaibaye harakoki da dama.

Wakilin GTA Hausa Amurka ke Magana Souley Moumouni Barma ya aiko mana Cewar, Hekta 21200 ne gwamnatin ta Nijar ta ce ta dauri aniyar bajewa domin fadada aiyukan noman zamani ba’idin hekta 10000 da tuni aka riga aka ga tasirin da suka yi wajen samar da wadatar cimaka a kasar a cewar ministan noma da kiwo kanal Mahaman Alhaji Ousman a yayin da ya ke jawabi a zauren majalissar wakilai ta rikon kwarya CCR.

Ta hanyar wannan tsari da ake saran shimfidawa a jimilce kan hekta 39700 ana hasashen girbe amfani sau biyu a kowace shekara inji ministan wanda kuma ya kara da cewa abu ne da zai bada damar samun a kalla Ton 481000 na shinkafa daga nan zuwa shekarar 2027, lamarin da ka iya rage adadin shinkafar da ke shiga kasar daga waje har ma da marasa da alkama.

Bayanan ministan sun gamsar da ‘yan majalissar kamar su Issa Adam domin a ta su fahimta zartar da kudirin gwamnatin zai samar da sassaucin rayuwa a wajen al’umma.

Galibin jama’ar Nijar sun dogara kan noma da kiwo a matsayin hanyoyin samar wa kansu cimaka sai dai matsaloli masu nasaba da canjin yanayi na haifar da babban gibin amfani, a kowace shekara idan aka kwatanta da abinda ake samu a baya abinda ke zama silar tsadar farashi a kasuwanni.

Hakan yasa shugaban kungiyar kare hakkin masaya ta ADDC Maman Nouri ke yaba wa da shirin da hukumomin suka bullo da shi.

Dam dam da manyan madatsun ruwa ne ake shirin ginawa kari akan wadanda ake da su a baya domin tabbatar da wadatar ruwan da za a yi amfani da shi a aiyukan da aka sa gaba a illahirin jihohi, kamar yadda aka yi tanadin kwararrun ma’aikata da kayan aikin noman zamani a wani bangare na aiyukan da shugaban Nijar Janar Abdourahamane Tiani ya yi alkawali a kundin manufofinsa, aikin da zai lakume makuddan miliyoyin cfa.

Afrika

Post navigation

Previous Post: Kotu A Birnin Tarayya Abuja Ta Bada Belin Tsohon Minista Abubakar Malami
Next Post: Jihar Kano Tayi Rashin ‘Yan Majalisu Biyu

Karin Labarai Masu Alaka

Mayakan Boko Haram Da ISWAP Sun Kai Hari Cikin Dare Afrika
Sojoji Sunkai Farmaki Gidan Dan Adawa A Kasar Uganda Bobi Wine Afrika
Gombe Da UNFPA Sun Ƙarfafa Haɗin Gwiwa Don Yaƙi Da Cutar Fistula Da Tamowa Afrika
PDP Ta Koka Kan Rushe-rushe, Korar Gombawa Motors da Zaɓen Kananan Hukumomi A Gombe Afrika
‘Yan Ta’adda Sun Hallaka Sojoji Da Fararen Hula A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
Ministan Sadarwan Kasar Uganda Yayi Allah Wadai Da Kaiwa Bobi Wine Hari Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kasar Chadi Ta Rufe Iyakar Ta Da Kasar Sudan Afrika
  • Masu Ruwa Da Tsaki Sun Buƙaci Ƙarin Tallafi Ga Iyaye Mata Masu Shayarwa A Gombe Afrika
  • Hawan Sallah Daga Masarautar Kaltungo Nishadi
  • Putin, Sakon Sabuwar Shekara Ya Jinjinawa Dakarun Rasha Da Suke Yaki A Ukraine Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Patrick Vieira Ya Cimma Yarjejeniyar Zama Sabon Kocin Senegal Wasanni
  • Isra’ila Zata Karbi Mutanenta A Yankin Gaza Labarai
  • Ga Fili Ga Doki Dambarwar APC Da ADC Najeriya
  • Gwamnatin Tarayya Ta Ce Babu Musguna Wa ’Yan Jarida A Mulkin Tinubu Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.