Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

TIC Dutse Ta Nemi Ƙarin Tallafin Gwamnatin Jigawa Don Faɗaɗa Ayyukanta
Published: July 8, 2026 at 8:47 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnatin jihar Jigawa ta sake tabbatar da aniyarta na ci gaba da tallafa wa Cibiyar Bunƙasa Fasaha (Technology Incubation Centre – TIC) da ke Dutse domin bunƙasa kasuwancin fasaha, haɓaka harkokin kasuwanci da samar da ayyukan yi a faɗin jihar.

Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar, Alhaji Muhammad K. Dagaceri, ne ya bayyana hakan yayin da ya karɓi Manajan Cibiyar, Injiniya Shukuranu Uzairu, tare da tawagarsa a ziyarar girmamawa da suka kai masa a ofishinsa.

Dagaceri ya bayyana TIC Dutse a matsayin cibiyar da ta yi fice a jihar, inda ya yaba da irin gudunmawar da take bayarwa wajen bunƙasa ƙirƙire-ƙirƙire da tallafa wa masu sana’o’i da ‘yan kasuwa.

Ya ce gwamnatin jihar tana sane da irin ayyukan alheri da cibiyar ke yi wajen haɓaka sabbin dabarun kasuwanci, tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da haɗa kai da ita domin ƙara faɗaɗa tasirinta wajen bunƙasa tattalin arziki.

Tun da farko, Manajan Cibiyar, Injiniya Shukuranu Uzairu, ya ce ziyarar na daga cikin shirin ƙarfafa alaƙa da masu ruwa da tsaki da kuma gano sabbin hanyoyin haɗin gwiwa tun bayan da ya karɓi ragamar jagorancin cibiyar.

Ya bayyana cewa shirin Cibiyoyin Bunƙasa Fasaha ya taka muhimmiyar rawa wajen haɓaka ƙirƙire-ƙirƙire da kasuwanci, yana mai cewa tallafin gwamnati ga irin waɗannan cibiyoyi a faɗin ƙasar ya taimaka wajen kafa dubban ƙanana da matsakaitan masana’antu (SMEs), tare da samar da ayyukan yi kai tsaye da kuma a kaikaice.

Uzairu ya roƙi gwamnatin jihar da ta ƙara tallafa wa cibiyar ta hanyar bunƙasa kayayyakin more rayuwa, samar da wuraren masana’antu ga waɗanda suka kammala shirin koyon sana’a da matasa masu tasowa a harkokin kasuwanci, da kuma ƙarfafa sauran shirye-shiryen haɗin gwiwa domin faɗaɗa ayyukan cibiyar.

Ziyarar ta nuna ƙudirin Gwamnatin jihar Jigawa na amfani da fasaha, ƙirƙire-ƙirƙire da bunƙasa harkokin kasuwanci a matsayin hanyoyin inganta tattalin arziki da samar da ayyukan yi ga matasa.

Afrika, Kimiya, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sana'o'i, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Gobara Ta Lalata Babban Zauren Majami’ar ECWA Gospel A Gombe
Next Post: Sabuwar Sakatariyar Ƙungiyar Gwamnonin Arewa Za Ta Ƙarfafa Ayyukan Ci Gaban Yankin

Karin Labarai Masu Alaka

‘Yan Bindiga Sun Jikkata Mutane A Arewacin Kasar Benin Afrika
Sojoji Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 1,597, Sun Ceto Mutane 1,516 – DHQ Afrika
Tinubu Ya Kawo Ƙarshen Aikin Kwamitin Sayar Da Kaddarorin Gwamnati Afrika
Gombe Ta Ƙarfafa Matasa da Ƙwarewar da Za Ta Kai Su Masana’antar Mai Da Iskar Gas Afrika
An Kai Hari Babbar Tashar Iskar Gas A Iran Afrika
Farashin Danyen Mai Ya Tashi A Kasuwannin Duniya Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Sanarwar MDD Ya Nuna Aniyar Mayakan RSF Na Kisan Kare Dangi Afrika
  • Emmanuel Macron: Yakamata Wani Sashi Ya Rika Takawa Wani Sashi Birki A Tsarin Demokradiya Amurka Amurka
  • ‘Yan Ta’adda Sun Hallaka Malaman Makaranta A Tilabery Afrika
  • Amurka Zata Bawa Ukraine Tsaro Na Musamman Amurka
  • Amurka Ta Yi Juyin Mulki A Kasar Venezuela Amurka
  • Za’a Dauko Messi Aro Zuwa Barcelona Deco Wasanni
  • Tinubu Yace Zayyi Hadaka Da Kasashen Duniya Domin Kawo Karshen Rashin Tsaro. Najeriya
  • Kenya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kasar Rasha Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.