Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Gobara Ta Lalata Babban Zauren Majami’ar ECWA Gospel A Gombe
Published: July 8, 2026 at 6:41 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Mambobin Majami’ar ECWA Gospel da ke kan titin Ashaka a jihar Gombe na ci gaba da tantance irin asarar da suka yi bayan wata gobara ta tashi ta lalata babban zauren cocin.

Gobarar, wadda ta faru a daren Talata, 7 ga Yuli, ta ƙone mimbari, dandalin mawaƙan coci, kayan kiɗa, kayan gudanar da ibada, rufin cikin gini (ceiling), rufin sama da sauran kadarorin cocin.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa bayan an kammala nazarin Littafi Mai Tsarki da misalin ƙarfe 6:00 na yamma, an rufe Majami’ar kamar yadda aka saba.

Sai dai da misalin ƙarfe 8:00 na dare, jami’in tsaron cocin ya hango hayaƙi na tashi daga saman ginin yayin da yake bakin aikinsa. Bayan ya je ya duba, ya tarar da cewa babban zauren cocin ya cika da hayaƙi, lamarin da ya sa ya gaggauta sanar da Faston da ke kula da cocin da kuma sauran mambobin coci.

Nan take mambobin cocin suka hallara domin dakile gobarar kafin ta bazu zuwa sauran sassan ginin.

Mazauna yankin tare da mambobin cocin sun haɗa kai wajen kashe gobarar, yayin da jami’an Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Gombe suka isa wurin da manyan motocin kashe gobara guda huɗu, inda daga bisani suka yi nasarar shawo kan gobarar.

Faston da ke kula da Majami’ar, Rabaran Dakta Gideon Danbauchi, ya gode wa Allah da cewa babu wanda ya rasa ransa sakamakon gobarar.

Ya bayyana lamarin a matsayin babban ƙalubale, amma ya ce cocin na da cikakken ƙwarin gwiwa da imani cewa za a sake gina sashen da gobarar ta lalata.

Rabaran Danbauchi ya kuma yaba wa Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Gombe da mazauna yankin saboda gaggawar da suka yi wajen taimakawa domin hana gobarar yaɗuwa.

Ya yi kira ga mambobin cocin, masu fatan alheri da al’ummar Kirista da su ba da gudummawa domin taimakawa wajen gyaran cocin.

Daraktan Fasaha na cocin, Mista Olatunji Daniel, ya ce ya samu labarin gobarar ne bayan ya ga hayaƙi mai yawa yana tashi sama tare da samun kiran gaggawa daga mutanen da ke kusa da cocin.

Ya ce lokacin da ya isa wurin, an riga an kulle cocin, lamarin da ya tilasta wa masu agaji fasa tagogi domin shiga su kashe gobarar, amma ƙarfin wutar ya fi ƙarfinsu.

Ko da yake har yanzu ba a tabbatar da musabbabin gobarar ba, shaidun gani da ido na zargin cewa matsalar wutar lantarki ce ta haddasa tashin gobarar.

Har yanzu ana ci gaba da tantance cikakken girman asarar, amma kiyasin farko ya nuna cewa darajar kayan da gobarar ta lalata na iya haura Naira miliyan 100.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Gombe: ‘Yan Sanda Sun Tarwatsa Ƙungiyar Masu Fashi Da Damfara Ta Yanar Gizo
Next Post: TIC Dutse Ta Nemi Ƙarin Tallafin Gwamnatin Jigawa Don Faɗaɗa Ayyukanta

Karin Labarai Masu Alaka

Kotu A Kasar Tunisiya Ta Daure Wani Babban Dan Kasuwa Da Wasu ‘Yan Majalisa Afrika
Gwamnatin Gombe Ta Dauki Sabbin Matakan Tsaro Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
‘Yan Sandan Gombe Sun Fara Kama Motocin Da Ba Su Da Lambar Rajista ko Masu Boye Lambobinsu Afrika
Ana Kokarin Kawo Karshen Matsalar Kashe Matafiya A Filato Afrika
Anyi Jana’izar Mahaifiyar Nasiru El Rufai A Abuja Afrika
Fadar Shugaban Ƙasan Najeriya Ta Musanta Wani Labarin ƙarya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shirin Safe 0500 UTC Yau Litinin 11.17.2025 Rediyo
  • Trump Yayi Barazanar Goyon Bayan Hari Akan Kasar Iran Labarai
  • Sakataren Harkokin Wajen Amurka Yace Rahoton Kasashe Biyar Akan Rasha Yana Dauke Da Damuwa Amurka
  • Dakarun Pakistan Da Afghanistan Sunyi Arrangama Labarai
  • Jamhuriyar Dimokraɗiyya Kwango Ta Bukaci Rwanda Ta Daina Marawa ‘Yan Tawayen M23 Baya Afrika
  • Kungiyoyi Sunyi Hasashen Jinkiri A Bunkasar Tattalin Arzikin Kashen Afirka Afrika
  • Najeriya Ta Kai Wasan Kusa Da Na Karshe A Wasan Dambe Na Matasan Afirka Wasanni
  • IBB: Ba Shakka Abiola Ya Lashe Zaben Yuni 12 Rediyo
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.