Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

‘Yan Sandan Gombe Sun Fara Kama Motocin Da Ba Su Da Lambar Rajista ko Masu Boye Lambobinsu
Published: June 11, 2026 at 10:23 AM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: June 11, 2026

Rundunar ’Yan Sandan jihar Gombe ta fara aiwatar da wani samame na musamman kan motocin da ke zirga-zirga ba tare da lambar rijista ba ko kuma masu amfani da hanyoyin boye bayanan lambobin motocinsu.

Rundunar ta bayyana cewa matakin ya biyo bayan umarnin Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Olatunji Rilwan Disu, wanda ya bayyana cewa yawaitar motocin da ke aiki ba tare da cikakken rajista ba ko masu boye lambobin mota ya saba wa doka kuma yana barazana ga tsaro da lafiyar jama’a.

A cewarsa, rajistar mota na taka muhimmiyar rawa wajen dakile aikata laifuka, tattara bayanan sirri na tsaro da kuma saukaka ayyukan jami’an tsaro. Ya kara da cewa masu aikata laifuka kan yi amfani da motocin da ba a iya gane su wajen aikata miyagun laifuka tare da kauce wa gano su.

A cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar ’Yan Sandan jihar Gombe, DSP Buhari Abdullahi, ya fitar, rundunar ta ce ta fara gudanar da sintiri da bincike a sassan jihar domin gano motocin da ba su da sahalallun lambobin rijista ko kuma wadanda aka boye lambobinsu.

Sanarwar ta yi gargadin cewa duk motar da aka samu da irin wannan laifi za a tsayar da ita, a kwace ta tare da daukar matakan shari’a da suka dace kamar yadda doka ta tanada.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Gombe, Umar Ahmed Chuso, ya bukaci masu ababen hawa su tabbatar da cewa motocinsu suna da cikakkiyar rajista tare da nuna sahalallun lambobin mota a fili a kowane lokaci.

Ya kuma gargadi masu motoci da su guji amfani da murfin lamba ko wasu gyare-gyare da ke hana ganin lambobin mota a sarari, yana mai jaddada cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukuncin da doka ta tanada.

Kwamishinan ya yi kira ga duk masu amfani da hanyoyi da su bi dokokin hanya domin taimakawa kokarin gwamnati da hukumomin tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Rundunar ’Yan Sandan jihar Gombe ta sake tabbatar da kudurinta na ci gaba da aiwatar da dukkan matakan da suka dace wajen hana aikata laifuka da kuma tabbatar da tsaron jama’a a fadin jihar.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: ’Yar Kasuwa Ta Tsallake Rijiya Da Baya Bayan Hari Da Saurayinta Ya Kai Mata
Next Post: Shugaba Tinubu Ya Kafa Kwamitin Gaggawa Akan Cutar Ebola

Karin Labarai Masu Alaka

Sojojin Amurka Sunfara Isowa Gabas Ta Tsakiya Amurka
‘Yan Ta’adda Sun Hallaka Sojoji Da Fararen Hula A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
Gwamnatin Kano: Zamu Kara Daukar Malamai Domin Inganta Ilimi Najeriya
Rundunar ‘Yan Sandan Kebbi Ta Dakile Yunkurin Garkuwa Da Mutune, Ta Kama Masu Laifi Afrika
Amurka Ta Kai Hari Kan ‘Yan ISISI A Jihar Sakkwato Bisa Rokon Gwamnatin Najeriya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Ministan Harkokin Wajen Najeriya Yayi Murabus Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Cutar Zazzabin Lassa Tayi Ajalin Mutum 1 Yayinda Mutane 11 Suka Kamu A Jihar Gombe Najeriya
  • Musulmai A Kasashen Duniya Da Dama Sunfara Azumin Ramadan Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Rahoton Leken Asiri Yanuna Cewa Harin Amurka Bazai Samar Da Shugabanci A Iran Ba Afrika
  • Hatsarin Mota Yayi Ajalin Mutum 7 A Gombe Najeriya
  • Indiya Da Brazil Sun Kulla Yarjejeniyar Cinikayya Afrika
  • Afirka Ta Kudu Ta Bayyana Yadda Aka Yaudari ‘Yan Kasar Ake Tilasta Musu Ayyukan Bauta Afrika
  • Anyi Rashin Mutane Da Yawa Yayinda Bom Ya Fashe Ana Sallar Magariba Maiduguri Labarai
  • Fubara Yana Yiwa Dimokraɗiyya Zagon Kasa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.