Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

’Yar Kasuwa Ta Tsallake Rijiya Da Baya Bayan Hari Da Saurayinta Ya Kai Mata
Published: June 11, 2026 at 9:46 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Wata ’yar kasuwa a jihar Gombe ta tsallake rijiya da baya bayan wani hari da ake zargin saurayinta ya kai mata da guduma a cikin gidanta da ke unguwar Pantami a birnin Gombe.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:00 na dare, lokacin da wanda ake zargin, Musa Adamu mai shekaru 35, mazaunin unguwar Riyal, ya tsallaka katangar gidan matar tare da shiga ɗakinta ba tare da izini ba.

Ana zargin ya kai mata hari da gudumar ƙarfe, sannan ya yi ƙoƙarin shaƙe ta da igiyar USB. Duk da munanan raunukan da ta samu, matar ta samu damar yin ihu domin neman taimako, lamarin da ya jawo hankalin maƙwabta tare da tilasta wa maharin tserewa daga wurin.

Rundunar ’Yan Sandan jihar Gombe ta tabbatar da kama wanda ake zargin bisa laifukan yunƙurin kisa, fashi da makami da kuma jikkata mutum.

Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa bayan harin, jami’an ’yan sanda sun garzaya da matar zuwa asibiti domin samun kulawar likitoci, inda daga bisani aka sallame ta bayan samun sauƙi.

Binciken farko da ’yan sanda suka gudanar ya nuna cewa wanda ake zargin ya taɓa neman matar ta ba shi kuɗi, amma ta ƙi amincewa da buƙatarsa, abin da ake zargin ya haddasa sabanin da ya kai ga harin.

Rundunar ta ce ta ƙwato gudumar da ake zargin an yi amfani da ita wajen kai harin da kuma igiyar USB da ake zargin an yi ƙoƙarin amfani da ita wajen shaƙe matar.

Kwamishinan ’Yan Sandan jihar Gombe, Umar Ahmed Chosu, ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da ɗaukar tsauraran matakai domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma tare da tabbatar da cewa an hukunta masu aikata laifuka bisa doka.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sana'o'i, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Sabon Babin Tsaro A Najeriya: Gombe Ta Fito Da Tsarin Smart Security Na Farko
Next Post: ‘Yan Sandan Gombe Sun Fara Kama Motocin Da Ba Su Da Lambar Rajista ko Masu Boye Lambobinsu

Karin Labarai Masu Alaka

Majalisar Tattalin Arzikin Najeriya Ta Bawa Gwamnan Kebbi Mukamin Kyautata Harkar Kiwo Najeriya
Najeriya Da Amurka Sun Amince Su Haɗa Kai Don Inganta ’Yancin Addini Da ƙarfafa Tsaro A Nijeriya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Kamfanin NNPC Yana Tattaunawa Da Wani Kamfanin Kasar China Labarai
Bincike Yanuna Kasashen Afirka Suna Cikin Mafiya Cin Bashi A Duniya Afrika
Ana Cigaba Da Ceto Masunta Daga Ruwa A Ghana Labarai
Sojojin Najeriya Sun Kashe Fitaccen ’Yan Bindiga Kallamu A Jihar Sakkwato Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kungiyoyi Sunyi Hasashen Jinkiri A Bunkasar Tattalin Arzikin Kashen Afirka Afrika
  • Sanata Barau Ya Raba Motoci Da Babura Ga Al’ummar Kano Ta Arewa Afrika
  • Wikki Tourists FC: Ta Yi Sabbin ‘Yan Wasa Uku Wasanni
  • Gwamnan Jihar Filato Na Shirin Komawa APC Siyasa
  • NAHCON Ta Fitar Da Jadawalin Hajjin Bana 2027 Afrika
  • Lawanti Ya Ƙara Wa Gombe Daraja A Fannin Aikin Jarida – NUJ Afrika
  • Na Yi Murabus Ne Don Amurka Ta Keta Haddin Iraniyawa Amurka
  • Hukumar Upper Benue Zata Inganta Noma A Dadinkowa Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.