Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Za’ayi Jana’izar Marigayi Ali Khamenei a Tehran, Qom da Mashhad
Published: June 3, 2026 at 5:02 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Mahukuntan Iran sun sanar da shirye-shiryen gudanar da jana’izar tsohon Jagoran Addini na kasar, Ayatollah Ali Khamenei, wanda ya rasu yana da shekaru 86 a duniya.

A cewar jami’an kasar, za a gudanar da jana’izar ne a manyan biranen Tehran, Qom da Mashhad cikin wani shiri na kwanaki uku da aka tanada domin bai wa miliyoyin ‘yan Iran da masu biyayya daga sassa daban-daban na duniya damar yi masa bankwana na karshe.

Rahotanni sun bayyana cewa za a fara gudanar da manyan tarukan addu’o’i da zaman makoki a Tehran, babban birnin kasar, inda ake sa ran miliyoyin mutane za su hallara domin girmama marigayin wanda ya jagoranci Iran na tsawon shekaru fiye da talatin. Jami’ai sun ce faretin jana’izar a Tehran kadai zai dauki akalla sa’o’i 24 saboda yawan mahalarta da ake tsammani.

Bayan kammala bukukuwan da za a yi a Tehran, za a ci gaba da jana’izar a birnin Qom, wanda ake kallonsa a matsayin cibiyar ilimin addinin Shi’a a Iran. Daga nan ne za a kai gawar zuwa Mashhad, garin haihuwarsa da ke arewa maso gabashin kasar, inda za a binne shi a Hubbaren Imam Reza bisa wasiyyarsa.

Mahukuntan Tehran sun ce mutane daga kasashe da dama, ciki har da Pakistan, Afghanistan, Indiya, Bangladesh da yankin Kashmir, na sa ran halartar jana’izar domin nuna girmamawa ga marigayin. Haka kuma, larduna daban-daban na Iran sun nemi damar karbar bakuncin tarukan makoki, lamarin da ke nuna irin tasirin da ya yi a fagen siyasa da addini.

Ana kallon wannan jana’iza a matsayin daya daga cikin mafi girman bukukuwan makoki da Iran za ta taba yi tun bayan jana’izar Ayatollah Ruhollah Khomeini a shekarar 1989, wadda ta jawo taron miliyoyin mutane daga sassa daban-daban na duniya.

Ali Khamenei ya kasance Jagoran Addinin Jamhuriyar Musulunci ta Iran tun daga shekarar 1989 har zuwa rasuwarsa, kuma mutuwarsa ta kawo karshen wani zamani mai muhimmanci a tarihin siyasar kasar.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Lewandowski: Zan Kokarta Zura Kwallo Ta 90 Don Kafa Tarihi A Poland
Next Post: Mourinho Ya ƙara Ta’azzara Takaddamarsa Da Hukumomin ƙwallon ƙafar Turkiyya

Karin Labarai Masu Alaka

Babban Sakataren MDD Yayi Allah Wadai Da Matakin Soja A Gabas Ta Tsakiya Afrika
PDP Ta Nemi Bincike Kan Rushewar Ginin Majalisar Dokokin Gombe, Tayi Zargi Game Da Sakaci Labarai
Kotu A Abuja Tabawa Goodluck Jonathan Daman Tsayawa Takara Afrika
Akalla Mutane 8 Sun Mutu Biyo Bayan Bindiga Da Wata Tanka Tayi Afrika
An Kashe Mutane 25 Yayin Kai Wasu Hare Hare Jihar Adamawa Labarai
Tawagar Masu Yi Wa Maniyyata Hidima Za Ta Tashi Zuwa Saudiyya Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Ministan Yaɗa Labarai: Ceto Daliban Neja An Samu Natsuwa A Kasa Labarai
  • ‘Yan Jarida Sunyi Mummunan Hatsari A Bauchi Labarai
  • Sojoji Sun Dakile Harin ’Yan Ta’adda a Kukareta Afrika
  • Gwamna Bala Kauran Bauchi Ya Koma Jam’iyar APM Afrika
  • ‘Yan Ta’adda Sun Tarwatsa Wani Kauye A Jihar Sakkwato Tsaro
  • Gwamnatin Somaliya Da MDD Sun Bayyana Cewa Kimanin Mutane Miliyan Shida Da Rabi Suna Fuskantar Barazanar Yunwa Labarai
  • Isra’ila Ta Cire Sunayen Wasu Mutane Biyu Cikin Wadanda Take Fako Afrika
  • Kungiyoyi Sunyi Hasashen Jinkiri A Bunkasar Tattalin Arzikin Kashen Afirka Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.